Rashin aiki da doka ce babbar matsalar Najeriya –Sarkin Kazaure

A daidai lokacin da taron kasa ke gudana don nemo makoma ga kasar nan, wakilanmu sun tattauna da Mai martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Husaini Adamu, inda ya ce babbar matsalar kasar nan ita ce rashin aiki da doka da oda, kuma muddin ba a samu haka ba, babu abin da zai sauya: Mai martaba, akwai […]

Rashin aiki da doka ce babbar matsalar Najeriya –Sarkin Kazaure
Rashin aiki da doka ce babbar matsalar Najeriya –Sarkin Kazaure

A daidai lokacin da taron kasa ke gudana don nemo makoma ga kasar nan, wakilanmu sun tattauna da Mai martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Husaini Adamu, inda ya ce babbar matsalar kasar nan ita ce rashin aiki da doka da oda, kuma muddin ba a samu haka ba, babu abin da zai sauya:
 Mai martaba, akwai masu ganin cewa masarautu sun rasa tasirinsu a harkokin rayuwa da siyasar kasar nan. Ka amince, kuma me ya sa?
To, ya daganta kan yadda mutum ya kalli hakan. Kuma idan ka kalli tambayar cewa akwai bukatar a raba ta gida biyu. Rasa tasiri da kuma fasalin rayuwa da siyasa.
Idan kana nufin iko na mulki da ikon harkokin da suka shafi tafiyar da rayuwar al’umma ne, na amince cewa eh, masarautu ba su da  wani iko. Amma game da suna da tasiri a tsarin siyasa ko, a’a, wannan magana ce da ake ci gaba da muhawara a kai, kuma wannan ne ya sa, ya danganta da yadda mutane suka kalli hakan.
Idan aka dubi abin da ya shafi karfin iko ne, lallai mun rasa tasiri a tsarin siyasa ko mulki. Saboda ba mu da abin cewa, ba mu da ikon zartarwa ba mu da wani abin aiwatarwa, babu abin da muke yi a tsarin siyasar. Amma idan ka dubi bangaren tsarin rayuwar jama’ar kasa, ba zan ce masarautu ko sarakuna sun rasa tasirinsu ba, saboda muna nan, har yanzu mu ke tare da jama’a. Kuma muna gudanar da ayyukanmu na masu tsare al’adu da dabi’un jama’a, a matsayinmu na shugabanni na asali, shugabannin da suke tare da jama’a, suke zaune a tsakanin jama’arsu, suke cudanya da su a kusan kullum a kowane al’amari. Duk kuwa cibiyar ko hukumar da ke haka, ba za ta rasa tasirinta ba. Don haka ban yarda cewa sun rasa tasirinsu a abin da ya shafi yadda rayuwa ke gudana.
Bisa abin da ka ce, ka amince da kiran da jama’a ke yi na a ba sarakuna wani takamaiman aikin yi a tsarin mulki?
Gaba dayan batu game da aikin yi ga sarakuna a karkashin tsarin mulki, abu ne da ake ta tattaunawa a kai, yayin da wasu ke ganin kamar sarakuna suna rokon a ba su aikin yi ne, mu muna duban lamarin ne bisa tsarin siyasar kasar nan na yanzu. Idan ka kalli tsarin mulkin da muke aiki da shi a kasar nan a yanzu babu koda wuri daya da ya ambata ko ya san da zaman masarautu, sabanin tsarurrukan mulkin da suka gabata. Misali tsarin mulkin da aka tsara a baya, ya yi bayani tare da bayani kan masarautu, har ma ya ba su wata kafa ta wakilci a Majalisar kasa. Kuma tsarin mulkin ya amince da majalisun sarakuna na jihohi a duk fadin kasar nan. Amma tsarin mulkin 1999 ya yi waje kacokan da masarautun. Don haka abin da muke cewa, shi ne a matsayinmu na tubalan gina kasar nan, a matsayinmu na ginshikan da aka kafa kasar nan a kanta, akwai bukatar tsarin mulki ya san da zaman wadannan masarautu. Idan ka kalli aikinmu a yau na masu ba da shawara, a matsayinmu na masu jawo ra’ayin jama’a, a matsayinmu na gada a tsakanin wadanda ake mulka da gwamnati, wajibi ne mu amince cewa akwai bukatar a samar wa masarautun abin yi a tsarin mulki. Kasancewarsu masu ba da shawara ga talakawa da kuma gwamnati, wannan aiki na shawara akwai bukatar a samar masu da doka, wato a sanya a tsarin mulki. Wannan zai sanya a matakin da ya fi dacewa na bayar da shawarar, wannan shi ne abin da muke nema.
Ba muna neman yin gasa da hukumomi masu zartarwa ba ne, ba muna neman a ba mu wani kebantaccen aiki na zartarwa ba ne. Aikinmu na masu ba da shawara ga gwamnati, masu ba da shawara ga talakawa, muke so a sa a tsarin mulki, wannan ne muke nema. Amma wasu mutane saboda dalilan da su suka sani suke cewa muna neman a ba mu wani aiki ne na daban don gudanarwa, muna jin dadi da farin ciki kan abin da muke yi na kasancewa masu kare al’adu da dabi’un mutane, a wasu wurare da yanayi har da martabar addinansu.  A matsayin cibiyoyin da mutane ke girmamawa, masarautu suna daukar nauyi da dawainiyar zama gadojin da ke sadar da gwamnati da wadanda take yi wa mulki, don haka muke bukatar tsarin mulki ya lura da wannan, kuma wannan ne muke nema.
Mai martaba, a matsayinku na taskar al’adun jama’a, yaya kake kallon canje-canjen da suke gudana a fannin al’adu da dabi’un jama’a?
Gaskiyar lamari, muna karkacewa daga gwadaben da ya kamata, muna karkacewa ta yadda muke watsi da al’adunmu, kuma babu wata al’umma da take gini a kan harsashi ko ginshikin wani.
Yanzu ba mu kokarin yin gini kan harsashi ko ginshikinmu, al’adunmu su ne ginshikanmu. Eh, akwai bukatar mutane su tafi tare da zamani don tafiya da sauran duniya, to amma wannan ba ya nufin ka yi watsi da asalinka, ka tuttuge tushenka, ka koma rayuwa irin ta wani. Abin da nake nufi da haka, shi ne, yayin da muke bukatar tafiya tare da zamani, wajibi ne mu gina hakan a kan ginshikin al’adunmu. Mene ne al’adunmu, mene ne martabarmu? Su ne girmama na gaba, amma mun rasa wannan, gaskiya da rikon amana, mun rasa su. Muna ta batun ’yanci makauniyar ’yanci da zaman sasakai, ta hanyar watsi da kyawawan abubuwan da muka gada, wajibi ne kuma a yi gyara kan haka.
Wajibi ne mu koma kan kyawawan al’adunmu da muka watsar. Mun san abin da ya kamata mu yi, amma mun kasa yi. Mu dauki misali da masarautunmu, wasu mutane suna ganin ba su da sauran wani amfani, to daga su fa sai kuma wanne? Akwai mutanen da suke ganin ba za a iya samun ci gaban zamani ba, ta hanyar amfani da masarautu, to amma su dubi Birtaniya, har yanzu suna girmama al’adunsu, har yanzu suna gina al’amuransu ne kan al’adunsu. Amma mu abin da muke yi shi ne rusa al’adunmu. Ko Amurka duk abin da suke yi, suna yi ne bisa al’adunsu. Amma mu ba mu gina al’adunmu, sai dai mu yi gini a kan al’adun wasu. Ka san ina ka fito, ka san kana da ’yan uwa ko abokai, kana da manya, ya wajaba ka zama mai biyayya. To me ya kamata mu yi? Mu koma ga kyawawan al’adunmu, ko kun taba ganin an gina iyali ba tare da mahaifi da mahaifiya ba? Ko za ka iya gina iyali a kana bin da babu. Za ka iya mayar da mahaifi marar tasiri ko mahaifiya kuma ka sa ran gina iyali? Ko za ka iya kafa al’umma babu ginshiki, babu iyaye? Ana kiranmu iyayen kasa, amma kana son gina kasa ba tare da iyaye ba, ta yaya haka zai yiwu?
Lokacin da aka fara taron kasa, wasu mutane sun yi ta kiran a rushe tsarin kananan hukumomi, mene ne ra’ayinka kan wannan?
 Bai kamata a yi watsi da tsarin kananan hukumomi ba, ko ka so ko ka ki, wajibi ne a ci gaba da tsarin kananan hukumomi a matakan karkara. Saboda kana da matsala da karamar hukuma ba za ka ce a rushe su ba.
Abin da ya kamata ka tambaya shi ne mene ne matsalar? Shin matsala ce ta ma’aikata ko ta mece ce, kuma yaya za a yi a magance matsalar. Matsalar kasar nan ita ce mun cika nuna lalaci wajen magance matsaloli.  Idan aka samu matsala a wani wuri, sai mu ce a yi watsi da shi, a nemo wani abu daban. Kamar mutane ne su ce a rushe jihohi, saboda sun samu matsala da wani Gwamna. Misali wani ya nemi ya zama Gwamna amma bai samu ba, sai ya ce gwamnoni mahandama ne, gwamnoni suna cinye kudin kananan hukumomi da sauransu, wasu lokuta idan suka karbi kudin kananan hukumomin ba su yin komai, kuma babu abin da zai faru.
Duk wadannan abubuwa da muke magana a kai cewa ba su aiki, suna da alaka da abu daya ne. Gazawarmu ta mu tabbatar doka tana aiki. Abin da muke bukata shi ne mu tabbatar doka tana aiki. Idan wani ya karya doka a kai shi kotu a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada, ba yadda kai kaso ba. ’Yan makonnin da suka wuce muna tattaunawa da wasu, sai na ce zan so in ga lokacin da ga misali idan na tuka motata dan sanda ya tsare ne ya ce Mai martaba ina lasisin tukin motarka? Na ce, ya yi hakuri ba na da lasisi, sai ya ci tarata    Naira dubu 10, washegari su fito da labarin cewa Sarkin Kazaure ya tuka mota ba lasisi an ci tararsa Naira dubu 10. Ni a kashin kaina zan ji dadi da irin wannan hali. Dalili, saboda in haka ya faru, dan tasin da ke tuka karamar motar Golf ko makamaciyarta don daukar fasinja ba zai yi haka ba.
Domin haka, matsalar ba ta rusa tsarin kananan hukumomi b ace, a’a ta rashin yin aiki da doka ce. Ba mu aiki da doka a rayuwarmu, dokokinmu ba su jagorantar harkokinmu. Abin da ke bambanta mu da saura shi ne gaza sanya a yi aiki da doka, idan muka  yi aiki da doka, muka za mu masu bin doka da oda al’umma ba za ta hadu da nuna isa da gadara a sama ko a tsakiya ko a kasa ba. Domin akwai nuna isa da gadara a ko’ina. Idan ka ce shugabanni suna nuna isa da mulki da zalunci, za ka samu nuna isa da gadara da zalunci a kasa. Mutane suna wahala a can kasa a nan da can, akwai mutanen da suke daukar makamai su kashe mutane, su sace kayayyakinsu su kuma sha.
Mutane suna yin abin da suka ga dama, akwai mutanen da in suka ji ba su jin dadi, sai su bi wata hanya su tafka ta’asa, babu mai tsoron komai.
daya daga cikin manyan matsalolinmu a yau shi ne batun wannan lokacinmu ne a mulki, hatta a tsakanin jihohi, yaya kake ganin za a inganta batun fifita bukatun Najeriya, maimakon bukatun kabilanci?
Hakika matsalar da take damun dukanmu ita ce me muke bukata ga wannan kasar. Idan kana son gina al’umma wadda ta kubuta daga irin wannan, wajibi ne mu koma kan batun bin doka da oda. A samar da yanayin da mutane za su rika jin suna da ’yanci, su rika jin su ’yan Najeriya ne. Idan kana rike da wani mukami ko mulki amma kana batun kabilarka to za ka gaza, akwai bukatar ka rika yin abubuwa kamar yadda doka ta tanada ba bisa bukatun kabilarka ba. Muna da sabani da rabe-rabe a kusan komai, bambancin kabila da bambancin addin, amma akwai manufar da Allah Ya yi mu haka. Manufar ita ce mu zauna lafiya da juna cikin jin dadi, wannan ya sa ake samar da doka da oda a kowace al’umma domin nuna yadda dangantaka za ta gudana.
Idan muka samu mabambantan dangantaka, sai mu tsara tare da tallafawa don magance wannan bambanci mu samu matsayar da za mu ci gajiyar juna. Duk abin da ka yi, duk abin da ka ce, ko abin da ka yi alkawari, idan ba ka aikatawa, ba ka iyawa ko ba ka da niyyar ko azamar cewa eh wannan dokarmu ce, kuma dole ne dukkanmu mu yi aiki da ita ba za ka samu nasara ba. Ka tabbatar ba a kafa wata dokar kasa don biyan bukatun daidakun wata kabila ba, a’a ta biya bukatun kowace kabila da rukinin jama’a, in bah aka ba za ka gaza.
Ana kafa dokoki ne ta hanyar da daukacin kasa za ta ginu, dokar da za ta tabbatar da zaman lafiya, dokar da za ta tabbatar da tsaro. Daga duk inda ka fito, in ba ka ji dadi a garinku ko jiharku ba, in ka zo wurina za ka ji dadi, saboda ta yiwu ina aiki ba tare da nuna bambanci ba, na yanke shawarar sauke nauyin da ke kaina gwargwadon yadda ya kamata. Ina tabbatar da cewa duk wanda ke zaune a masarautata yana zaune cikin jin dadi, ba tare da tsoron musgunawa ba, ba tare da tsoro wani mugun abu zai faru da shi ba, ba tare da tsoron za a nuna masa bambanci ba. Idan a ko’ina muka samu daidaiton al’amura na tabbatar da tsaro, akwa zaman lafiya, me zai sa ka yi tunanin cewa yanzu lokacin mulkinku ne?
Idan ni sarkinka ne ko gwamnanka ko ciyaman kuma ina bin doka, ina tabbatar da adalci a tsakaninku, kuma idan ban yi adalci ba, doka za ta hukunta ni, me zai sa ka yi tunanin wannan lokacinku ne ko na wani mutuminku?
Me zai sa in damu da koma wane ne ke mulki, ko ke rike da madafun iko? Muna damuwa ne saboda babu abin da muke yi domin kai kasarmu ga tudun mun tsira. Muna ta dimuwa ne a tsakiyar daji, mun rasa alkibla, wannan ne ya sa mutanen Yamma su ce zangonsu ne, na Tsakiyar Najeriya su ce nasu ne, na Arewa ta Yamma ko ta Gabas su ce wannan, su ce wancan, ko a jihohinmu haka muke yi. Akwa ka’idoji na mayar da mutane kan ka’ida, amma idan ina yin abin da na ga dama, ta yaya zan ce maka ka bi ka’ida?