Rashin aikin yi kalubale ga matasa!
Hakika duk wanda ya san me ake nufi da matasa, to a ko’ina ne zai tabbatar da cewa, matasa su ne kashin bayan cigaban kowace al’umma. Domin kuwa mafi yawa daga cikin cigaban da al’umma ke samu yana samuwa ne ta hanyan matasan.Idan muka dauki irin cigaban da al’umma ke samu na yau da kullum […]
Hakika duk wanda ya san me ake nufi da matasa, to a ko’ina ne zai tabbatar da cewa, matasa su ne kashin bayan cigaban kowace al’umma. Domin kuwa mafi yawa daga cikin cigaban da al’umma ke samu yana samuwa ne ta hanyan matasan.
Idan muka dauki irin cigaban da al’umma ke samu na yau da kullum za mu ga cewar fiye da kashi 75 cikin 100 na zuwa ne ta hanyar matasa sauran kashi 25cikin 100 ne ke zuwa ta hanyar mata da tsofaffi, to amman abin mamaki, shi ne, yadda rayuwar matasan ke cike da kalubale iri-iri wadanda suka hada da matsalar rashin aikin yi da sauransu.
Rashin aikin yi babbar matsala ce da ta addabi matasan Najeriya da ma na Afirka baki daya, kuma shubaganni da dama da suka gabata sun yi bakin kokarinsu domin ganin sun kawar da wannan matsalar ta rashin aikin yi, amman abin ya faskara saboda a kullum adadin marasa aikin yi karuwa yake yi. Haka zalika duk shekara jami’o’in kasar da sauran makarantun gaba da sakandare na yaye dalibai da yawan gaske, illa kalilan ne daga cikinsu ke samun guraben aikin yi a gwamnati ko a kamfanoni masu zaman kansu. Wadansu kuwa na tsallakawa kasashen Turai domin neman aiki mai tsoka. A gefe guda kuwa, ga wadanda ba su je makaranta ba, su ma suna fama da wannan matsalar fiye da kima.
Ko a shekarun baya kungiyar kwadago ta duniya ta yi gargadi game da abin da ta kira tabon da matasa za su samu a tsawon rayuwarsu, sakamakon rashin aikin yi, ko kuma ‘yan kananan ayyukan da ba sa biyan bukata sosai.
A cikin rahoton da kungiyar ta fitar a kan rashin aikin da matasa ke fuskanta, kungiyar kwadagon ta ce, matsalar za ta yi mummunan tasiri a nan gaba a kan rayuwar matasan. Ta ce za a samu yawaitar zanga-zanga a tsakankanin matasan, kuma matasan za su dawo daga rakiyar tsare-tsaren siyasa.
Sabon binciken kungiyar ya nuna cewa, matasan da ba su da ayyukan yi a duniya sun kai miliyan 75, watau kashi 12 da digo 7 cikin 100 ke nan. Su kuwa matasan kasashen da ke tasowa, a cewar rahoton, su na fama ne da ayyukan da ba a bayar da albashi mai gwabi.
A gefe daya kuwa za mu ga ko da ’yan siyasa na alkawarta wa al’umma cewar idan suka hau mulki za su samar da guraben aikin yi da sauran hanyoyin sana’o’i ga matasa. Kuma tabbas hakan ya yi tasiri a cikin zukatan matasan domin kuwa ko a zaben da ya gabata a Najeriya masana sun tabbatar rashin aikin yi na daga cikin dalilan da yasa jam’iyya mai mulki ta fadi a wancen lokacin. Kuma alkawarin da jam’iyya mai mulki a yanzu ta yi wa al’umma na ba su guraben aikin yi da kyakykyawan tsarin ba da Naira dubu biyar ga marasa aikin yi domin rage radadin talauci.
Ko a nan kadai na tsaya mai karatu zai fahimci cewar matsalar rashin aikin yi babbar matsala ce da ke hana cigaban matasa da ma cigaban al’umma baki daya. Kuma wannan matsalar na bukatar taimakon gaugawa domin magance ta.
A daidai wannan gabar zan yi amfani da damar wurin yin kira ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da sauran daukacin Gwamnonin kasar mu musamman na Arewacin kasar da su tashi tsaye wajen magance wannan mummunar matsalar ta rashin aikin yi da ta addabin al’ummar Najeriya, kuma ya hana su ci gaba. Allah ya sa wannan kiran ya kai inda ya dace amin.
Amo, shi ne Sakataren kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina. 09097300909.