Rashin aikin yi ne ke sanya matasa sukar shugabanni – Kwamared Katuka

kungiyar dalibai ta kasa ta bayyana cewa rashin ayyukan yi tsakankanin matasa ne yake janyo suke bata lokaci a kafar sadarwar intanet suna sukar shugabannin.Kwamared Ahmed Katuka tsohon daraktan kungiyar dalibai ta kasa mai kula da sasanta rikici shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Minna a karshen makon da […]

Rashin aikin yi ne ke sanya matasa sukar shugabanni – Kwamared Katuka
Rashin aikin yi ne ke sanya matasa sukar shugabanni – Kwamared Katuka

kungiyar dalibai ta kasa ta bayyana cewa rashin ayyukan yi tsakankanin matasa ne yake janyo suke bata lokaci a kafar sadarwar intanet suna sukar shugabannin.
Kwamared Ahmed Katuka tsohon daraktan kungiyar dalibai ta kasa mai kula da sasanta rikici shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Minna a karshen makon da ya gabata.
Ya ce ba komai ne ya janyo kake ganin matasa sun mayar da hankalinsu kan fadar albarkacin bakinsu a kafar sadarwa ta intanet ba sai rashin aikin yi.
“Za ka ga matashi tun safe har zuwa dare yana sukar shugabanin ta kafar sadarwa iri-iri. Wasu lokutan ma har zagin shugabannin suke yi. Ka ga wannan ba komai yake janyo haka ba sai rashin aikin yi,” inji shi.
Katuka wanda, har ila yau, shi ne tsohon kwadinetan kungiyar ya bayyana cewa abin da zai yi maganin matsalar shi ne gwamnati ta samar da ayyukan yi ga matasa.
Ya bayyana cewa shirin da gwamnatin tarayya ta bullo da shi na daukar matasa dubu dari biyar aiki abu ne mai kyau da zai rage zaman kashe wandon da matasa suke yi a kasar nan.
Sai dai kuma ya shawarci gwamnati ta kara sanya ido wajen ganin an dauki wadanda suka cancanta tare da ba su horo don su samu kwarewa sosai.
Ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnati ta daura dammara wajen ganin ta cimma burinta na rage dogaro a kan man fetur.
Don inji shi ita ce mafita ga matsalolin tattalin arziki da kasar nan ta fada ciki, Katuka wanda yana daya daga cikin wadanda suka kafa gamayyar kungiyoyin dalibai na kasa ya yaba wa matakan da gwamnati take dauka na gyara tattalin arzikin kasa.
Da ya juya kan nasarorin da kungiyar ta samu, sai ya ce sun samu nasarar hada kan daliban kasar nan da ilimantar da su illoli masu yawa.
Ya bayyana cewa babban kalubalen da kungiyar ke fuskanta shi ne yadda wasu ’yan siyasa ke tsoma baki cikin harkokin dalibai don cimma burin kansu.
Ya ce wannan ba karamin tarnaki yake yi wa kungiyar ba wajen cimma burin da ta sanya a gaba.