Rashin aikin yi ya karu a Najeriya — NBS
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce rashin aikin yi ya karu a Najeriya da kashi 27.1 cikin 100 a watanni shidan farkon shekarar 2020. A alkaluman da sashen kididdigar kwadago na hukumar ya fitar ranar Juma’a, NBS ta nuna cewa matsalar rashin aikin ta fi kamari tsakanin matasa da ke tsakanin 15 zuwa 34, […]
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce rashin aikin yi ya karu a Najeriya da kashi 27.1 cikin 100 a watanni shidan farkon shekarar 2020.
A alkaluman da sashen kididdigar kwadago na hukumar ya fitar ranar Juma’a, NBS ta nuna cewa matsalar rashin aikin ta fi kamari tsakanin matasa da ke tsakanin 15 zuwa 34, wanda ya karu daga kashi 20.7 zuwa kashi 34.9 cikin dari
Hukumar ta kuma ce matsalar ta fi kamari ne tsakanin matasa in an kwatanta su da manya masu tarin shekaru.
Aminiya ta gano cewa kimanin mutum miliyan 116 da dubu 870 daga cikin matasa masu shekara 15 zuwa 64 ne suke da cikakken aikin yi.
Rahoton hukumar ya kuma nuna cewa kimanin mutum miliyan 80 da dubu 290 da ke tsakanin shekarun yin aiki ne suke da aikin.
To sai dai rahoton ya gano cewa kason mutanen da suke da ayyukan yi a watanni shidan farkon shekarar ya tashi daga 22.8 zuwa 31.5 cikin dari, yayin da mazauna birane suka fi samun karuwar masu aikin yin idan aka kwatanta da takwarorinsu na yankunan karkara.
NBS ta ce daga cikin wannan kason, mutum miliyan 39 da dubu 590 ne suke da ayyukan yi na din-din-din, sai kuma miliyan 22 da dubu 940 da suke da ayyuka na wucin gadi.
Rahoton hukumar dai ya nuna an samu raguwar alkaluman masu aikin yi da kimanin kaso 15.8 cikin 100 a watanni shida farkon 2020 in aka kwatanta da watanni ukun da su ka gabata.