Rashin amfani da cokali mai yatsu ya sa wata ’yar Kuwait ta nemi mijinta ya saketa
Wata mata a kasar Kuwait ta kai kara, inda ta bukaci a raba aurenta da mijinta, bayan aurensu da mako guda,. Bayan da ta gano mijinta ba ya son tsirar koren wake da cokali mai yatsu, ya fi son ya saka shi a cikin burodi.Matar ta zargi mijinta da rashin bin ka’idar zama a teburin […]
Wata mata a kasar Kuwait ta kai kara, inda ta bukaci a raba aurenta da mijinta, bayan aurensu da mako guda,. Bayan da ta gano mijinta ba ya son tsirar koren wake da cokali mai yatsu, ya fi son ya saka shi a cikin burodi.
Matar ta zargi mijinta da rashin bin ka’idar zama a teburin cin abinci, ya kuma ki bin tsarin cin abinci yadda ya dace, inda ta ce ta hadu da takaici, tare da “kaduwa,” ta yadda ba za ta iya ci gaba da zama da mijinta a tsawon rayuwarta ba. Don haka ta bukaci a raba aurensu, kamar yadda Jaridar Al kabas mai fitowa kullum ta kasar ta ruwaito.
Irin wadannan al’amura ba baki ba ne a kasar Kuwaiti, sabanin yadda mata ke neman saki idan ana muzguna musu a rayuwa, ko rashin biyayya ko rashin tattaunawa da juna, su sukan nemi saki ne akan dalilan da ba a saba ji ba, a cewar rahoton wannan jaridar.
A wani rikicin auren, makamancin irin wannan, wata mata ta sanar da lauyanta cewa tana son a raba aurenta da mijinta don yana matso man goge baki daga tsakiya, maimakon daga karshensa. “Mun sha yin tankiya,” kamar yadda jaridar ta ruwaito daga bakinta. “Na sha nanata masa cewa ya rika matso man goge baki daga karshensa, amma ya ci gaba da matso shi daga tsakiya.
A wata karar da ta shafi miji, maigida ya saki matarsa saboda ta ki kawo masa ruwa a kofi, inda suka yi takaddama kan cewa akwai ’yar aiki da za ta iya kawo masa. Jaridar ta ruwaito cewa, da ya bukaci ta kawo masa a karo na biyu ta ki, sasi ya sanar da ita cewa babu aure a tsakaninsu, kuma ya saketa.
A cewar masanan shari’a a kasar Kuwaiti, rashin juriya da hakuri da dabi’un juna, su ne manyan matsalolin da ke haifar da sakin aure a kasar.
“Kamata ya yi ma’aurata su fara fahimtar junansu, tun lokacin da ake neman aure, ta yadda za su yanke wa kansu hukuncin cancantar zamansu abokan rayuwar juna a cikin aure,” a cewar wani masanin dokoki da hukunce-hukuncen shari’a.
“Lokacin bin al’ada, inda ake yin aure, sannan m’aurata su san junansu ya wuce, don haka akwai damar tantance abokin zaman rayuwa, ta yadda za a iya yanke matsaya kan cancanta,” inji shi.
A wasu lokutan bai kamata a mayar da harkar aure tsarin gina iyali kawai, har ma da la’akari da zamantakewar al’umma, kamar yadda masanan shari’a suka bayyana wa jaridar.
A irin yanayin da mutanen kasar suka samu kansu, akwai bukatar masu nufin zaman ma’aurata su samu horo daga masana dabi’ar da zamantakewar al’umma da harkokin shari’a, don su nusar da su hanyar da ta dace wajen yanke matsaya a rayuwarsu.