‘Rashin audugar al’ada na jefa mata cikin tsaka mai wuya’

Ta ce dole dukkan masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen samar da audugar ga mata

‘Rashin audugar al’ada na jefa mata cikin tsaka mai wuya’

Zainab Nasir Ahmad

Zainab Nasir ita ce Shugabar kungiya mai zaman kanta ta YOSPIS a Jihar Kano, kuma ’yar gwagwarmaya a fafutukar inganta rayuwar mata. A wannan tattaunawar da Aminiya, Zainab ta yi bayani kan matsalar rashi ko karancin audugar al’ada a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin da mata da ’yan mata ke fama da su musamman a Arewacin Najeriya da ma hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar.

Mene ne muhimmancin ranar kula da Tsaftar al’ada ta duniya?

To da farko dai rana ce mai matukar muhimmanci wadda ake bikinta duk shekara. Wata kungiya ce mai suna Water, Sanitation and Hygiene (WASH), ma’ana ruwa da tsafta da kuma kula da kai, ta assasa ta a 2013.

Rana ce mai muhimmanci duba da matsayin jinin al’ada ga ’ya mace wanda duk macen da ta kai munzili ta ke yin sa, amma kuma ana yin shi cike da wasu matsaloli da kurakurai da kalubale wanda yawancin mata, musamman masu karancin shekaru suke fuskantar hakan saboda yanayi na a yi shuru, kada a yi tambaya, kada a tattauna da sauransu.

Wannan na daga cikin manyan dalilan da suka sa aka samar da wannan rana saboda a nuna wannan abu ne da ke faruwa da ‘ya mace wanda ba aibu ba ne, haka halitta ta zo da shi.

Kuma abu ne da ya kamata a bai wa muhimmanci saboda a dakile matsaloli da kalubalan da mata kan fuskanta a duk lokacin da suke cikin wannan hali.

Da kika ce matsaloli da kalubale, wadanne irin matsaloli da kalubale ne kike magana a kai?

Na ji dadin wannan tambayar. Babban kalubalen shi ne, babu cikakkun bayanai na kula da kai. ’Yan mata suna fama da rashin bayanai musamman a kasashe masu tasowa wanda Najeriya na daya daga cikinsu. Idan mace ta fara ganin al’ada daga gida ya kamata a soma yi mata bayani dalla-dalla kan yadda za ta kula da kanta, amma yawanci ba su iya yin hakan saboda kunya tsakanin iyaye da ’ya’ya.

Wasu lokutan, iyaye kan yi amfani da hikima wajen sanar da ’ya’ya mata batun al’ada ta hanyar alakanta shi da camfi ko ba da tsoro, misali kamar su ce idan yarinya ta bari namiji ya taba mata hannu a lokacin da take al’ada za ta samu juna-biyu, ko idan mace na ala’da ba a son ta yi kaza da kaza da sauransu wanda ita kuma yarinya za ta tashi da shi alhali wannan abu ne mai hadari ga rayuwarta.

Sannan akwai yanayi na kunya wanda kan hana a fadi bayanan da suka dace, ba ma a gidaje kadai ba har da makarantu. Za ka ga yawanci a makarantu malamai ba su iya yi wa yara cikakken bayani sai dai  a yi musu bayani a dukunle.

Yawanci a wajen kawayensu suke samun bayanai, kuma da yake tsara suke shekarunsu guda ba lallai ne su fi su sanin abin ba saboda su ma ba su samu wani cikakken bayani yadda ya kamata ba, ta haka za ka ga ana samun rashin iya kula da kai.

Sai kuma yanayi na tsadar audugar da ake amfani da ita, musamman ma a irin yankunanmu da ake fama da talauci. Wannan ne ma ya sa Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya yi hasashen cewa wasu yara mata da  ke tafiya makarantun sakandare kan rasa zuwa makaranta na kwana biyar a duk wata. Saboda suna ganin cewa da su fita su bata jikinsu da al’ada, walau saboda rashin halin sayen auduga, ko gudun kada ta yi amfani da tsumma ya goce da makamantansu, gara ta yi zamanta a gida, ka ga wannan ya shafi yanayin karatunta.

Sannan akwai matsalar ruwa. Saboda ko da yarinya ta ce za ta yi amfani da tsumma, shi tsumman kan shi ba kowanne aka yarda da amfaninsa ba, amma a haka za ta zo ta yi amfani da shi cikin rashin sani, watakila ta yi amfani da mai datti wanda ka iya haifar mata kamuwa da kwayoyin cututtuka ya taba lafiyarta.

Duk abin da zai taba lafiya da ilimi ba karamin al’amari ba ne, abu ne da bai kamata a kau da kai ga barinsa ba. Kamata ya yi a zauna a fahimci mece ce matsalar sannan a samar da hanyar magance ta.

Akwai wani gangami ko yekuwa da kika taba yi a shekarun baya na ganin an samar da audugar al’ada kyauta ga yan mata, yaya kika fuskanci girmar matsalar da har ya sa kika fito da wannan yekuwar?

Eh, kamar dai bayanan da na yi a baya, wadannan matsalolin nake ganin mata suna fama da su yau da kullum, amma kuma suna jin kunya da tsoro saboda yanayin al’ummar da muke ciki, inda wasu ke ganin cewa abin kunya ne mace ta fito ta tattauna batun al’ada, ni kuma na fahimci cewa muddin aka ci gaba da yin shuru lamarin ba zai haifar da da mai ido ba.

Kullum ana ta tafiya ana fuskantar  matsaloli ba tare da daukar mataki ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa na fito da wannan gangamin na nuna cewa wannan fa matsala ce da bai kamata a ce an kau da kai ba, bai kamata a ci gaba da jin kunya ba.

Kamata ya yi a kawar da al’adar nan ta jin kunya sannan a warware camfe-camfen da ake kakaba wa mata dangane da al’ada. Haka nan, a wayar musu da kai a kan yadda za su rika kulawa da kuma tsaftace kansu ko da kuwa ba su da halin sayen auduga sai tsumma za su yi amfani da shi, a nuna musu yadda za su kare kansu.

Ba wani abu ba ne idan kina al’ada, saboda yawanci idan mace na cikin wannan hali sai ka ga ta takura wa kanta ta daina fita, ta daina abubuwa da yawa wanda hakan ma ba ya cikin tsarin addini.

Mun san abin da addini ya tsara wanda ya kamata mace ta yi idan tana al’ada, don haka wadannan al’adu da suke cutarwa sai a ajiye su a gefe. Wadannan su ne dalilan da suka sa na fito da wannan gangami a Arewacin Najeriya wanda ya samu karbuwa sosai, har ta kai ga wasu kungiyoyi da dama suka shigo cikin lamarin don a yi da su.

Yanzu idan ka lura an samu cigaba sosai saboda wayewar kan na ta karuwa tun da ana shiga cikin al’umma ana wayar wa ’yan mata kai. Sannan muna ta kira ga gwamnati a kan ta shigo a samu ko da harajin da ke tattare da audugar a janye shi tun da mun sani akwai wasu kayayyakin da ake cire musu haraji, ya kamata a ce ita ma audugar mata ta samu shiga jerin irin wadannan kayayyaki don ta zama da saukin samu ga wadanda lamarin ya shafa.

Akwai wata kungiya da ta yi hasashen cewa alkaluman matan da ba su iya samun audugar al’ada a Najeriya sun kai kusan miliyan 37, shin yaya kike kallon alkaluman?

Gaskiya alkaluma ne masu ban tsoro. Saboda rashin samun audugar ya nuna wadannan matan suna cikin wadannan matsalolin ne. Wannan ne ma ya sa aka kirkiro wani kunzugun da ake iya wankewa a maimaita amfani da shi.

Ana ba da bayanan yadda mace za ta rika tsaftace kunzugun bayan ta yi amfani da shi wanda zai dauke ta tsawon wata shida tana amfani da shi. Muna ta karfafawa kan samar da irin wannan kunzugu a cikin gida maimakon dagaro da na ketare ta yadda ba zai yi tsada ba idan aka samar da shi.

Sai dai kalubalen da ke tattare da kunzugun shi ne, idan mace ta yi amfani da shi dole ta bukaci ruwa da sabulun da za ta wanke shi, ka ga wannan ma wani kalubale ne mai zaman kanasa.

Kuma ba kowace mace ce za ta juri wanke kunzugun ba saboda kyankyani ko kyama. Shi ya sa na mayar da hankalina wajen wayar da kan mata dangane da yin amfani da ainihin audugar al’ada, saboda in dai za a samu saukin audugar, haka ma za a samu saukin wadannan matsalolin da na yi bayani a baya.

Kamar a bangaren gwamnati da sauran al’umma, wace irin rawa kike ganin ta dace su taka a wannan fannin?        

Gaskiya wannan abu ne da ya kamata a ce kowa ya shigo ciki ba wai sai kungiyoyi masu zaman kansu kawai ba. Alal misali, a matsayinka na uba ya kamata ka rika lura da yanayin da ‘ya’yanka suke ciki. Saboda galibi ko a gidaje za ka tarar ba a mai da hankali, za ka ga an ajiye kayan abinci da sauran kayan bukatu amma ba a damu da tanadin audugar mata ba alhali ita ma audugar abar bukata ce.

Haka nan, shugabannin al’umma da masu hannu da shuni suna iya shigowa su taimaka, su rika saye ko makarantu suna kaiwa, musamman makarantun kwana. Saboda wani bincike da na gudanar a baya, wasu ‘yan makarantar kwana sun fada mini cewa har katifar kwanciyarsu suke yankawa suna amfani da ita a lokacin da suke al’ada saboda tsumman da suke amfani da shi kan yi musu karanci alhali ba su da halin mallakar auduga. Ka ga idan masu hali za su shigo cikin lamarin su taimaka wa irin wadannan ‘yan matan, za a samu sauki sosai. Saboda a ganina matsalar ta shafi kowa ba iya mata kadai ba.

Ko kina da wani karin bayani da kike ganin yana da muhimmanci al’umma su sani?

Karin bayanin da zan yi shi ne, gwamnati ta taba yin alkawari amma har yanzu ba ta cika ba. Saboda a 2020 gwamnati ta ce za a fara raba wa ’yan mata auduga kyauta musamman a makarantun sakandare, amma har yanzu shuru kake ji.

Don haka muke kira ga gwamnati da ta taimaka ta kalli wannan al’amari, ko da a ce a matsayinmu na al’umma muna ba da gudunmawarmu idan gwamnati ta sako hannunta ciki insha Allah za a samu warwarewar matsalolin.

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos