Rashin bin doka ke haddasa haddura a hanyoyi

Babban Daraktan Hukumar Kula da Ababen Hawa (b.I.O) na Jihar Katsina, Alhaji Salisu Musa Bello ya ce rashin bin dokokin tuki daga direbobi ke haddasa yawan haddura a hanyoyin kasar nan. Shugaban ya ce, in da direbobi na bin dokokin hanya ko ana hukunta duk wanda ya karya dokar tuki da tuni da an samu […]

Rashin bin doka ke haddasa haddura a hanyoyi
Rashin bin doka ke haddasa haddura a hanyoyi

Babban Daraktan Hukumar Kula da Ababen Hawa (b.I.O) na Jihar Katsina, Alhaji Salisu Musa Bello ya ce rashin bin dokokin tuki daga direbobi ke haddasa yawan haddura a hanyoyin kasar nan.
Shugaban ya ce, in da direbobi na bin dokokin hanya ko ana hukunta duk wanda ya karya dokar tuki da tuni da an samu saukin asarar rayuka da dukiyoyi da hadarin ke haddasawa.
Daraktan ya shaida wa Aminiya haka ne a ofishinsa da ke Katsina, inda ya kawo misali a kan irin kayan kida da ake sawa a babur mai kafa uku ko Keke NAPEP. “Ba wai baburan haya ba hatta da na gida bai kamata a ba yaron da bai san ka’idar tuki ba ko mai shaye-shaye. Amma sai ka ga masu tukin babura masu kafa uku suna sanya kade-kade su bude sautin yadda wanda ke nesa zai iya ji. Hakan na haddasa hadari saboda na cikin Keke-NAPEP din bai ma jin karar wani abin hawan da zai wuce shi.”
Ya ce, masu tuki suna yin waya ko amsa kira laifi ne babba da ya ce a doka duk wanda zai yi waya ko zai amsa waya ya samu wuri ya tsaya.
Alhaji Salisu ya ce, a halin yanzu hukumarsa na shirye-shiryen mika wa Majalisar Dokokin Jihar Katsina wasu dokoki kan tuki domin neman amincewarta. “bullo da dokoki za su taimaka wajen rage aukuwar haddura da samar da kudin shiga da kuma sama wa matasa aikin yi,” inji shi.
Daraktan ya bukaci gwamnati da majalisar da kungiyoyin sufuri da sauran masu amfani da ababen hawa su bai wa hukumarsa hadin kai domin aiwatar da ayyukanta don a rage aukuwar hadarurruka a jihar.