Rashin bin dokar hanya yasa tsohon shugaban kasa bada hannu a hanya

Sakamakon rashin bin dokar hanya yasa tsohon shugaban kasar Ghana, Jerry John Rawlings ya ajiye motarsa a gefen hanya ya shiga tsakiyan titin hanyar birnin Accra zuwa Aflao don daidai motocin da suke bin hanyar wanda hakan yasa dokar wurin ta yi muni. Wasu direbobin hanyar sun yi watsi da dokokin hanyar sakamakon hanya da […]

Rashin bin dokar hanya yasa tsohon shugaban kasa bada hannu a hanya

Tsohon shugaban qasar Ghana Jerry John Rawlings

Sakamakon rashin bin dokar hanya yasa tsohon shugaban kasar Ghana, Jerry John Rawlings ya ajiye motarsa a gefen hanya ya shiga tsakiyan titin hanyar birnin Accra zuwa Aflao don daidai motocin da suke bin hanyar wanda hakan yasa dokar wurin ta yi muni.

Wasu direbobin hanyar sun yi watsi da dokokin hanyar sakamakon hanya da mota daya zata wuce suka maida hanyar ta motoci hudu inda zasu kutsa hakan ya janyo cunkoson hanya, musamman shiyyar Prampram a birnin Greater Accra. Wannan rashin hakurin direbobin ya haddasa cunkushewar hanyar.

Bayan da tsohon shugaban kasar ya fahimci cewa, akwai rashin kiyaye dokar hanya da matafiya suke yi wanda ke janyo cakudewar  ababen hawa, daidaita motocin da tsohon shugaban kasar ya yi ya taimaka sosai aka saukin wucewa inda wasu share sa’a daya suna jira.

A cewar wani makusanci tsohon shugaba Rawlings, ganin yadda rashin kiyaye doka da ya yi kamari a mafi yawan hanyoyin yasa yanke shawarar shiga tsakiyan hanyar yana baiwa direbobi umarnin da kuma tabbatar da kiyaye doka.

Tun farko dai tsohon shugaban kasar ya nada sha’awar ya hada gwiwa da ‘yan sanda da sojoji a shiyyar da ba a kiyaye doka, don tabbatar da matafiya suna kiyaye dokar kasar.

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas