‘Rashin biyan karin albashi babbar matsala ce’

A ci gaba da zakulo matsalolin tattalin arziki da hanyoyin magance su  Aminiya ta sake jin ta bakin Malam Abudassalam Kani malami a Kwalejin  Ilimi na Sa’adatu Rimi da ke Kano domin bitar karin albashi da alfanunsa da matsalolin da ke tattare da kin biyan karin albashin kamar haka: Me ake nufi da mafi karancin […]

‘Rashin biyan karin albashi babbar matsala ce’

A ci gaba da zakulo matsalolin tattalin arziki da hanyoyin magance su  Aminiya ta sake jin ta bakin Malam Abudassalam Kani malami a Kwalejin  Ilimi na Sa’adatu Rimi da ke Kano domin bitar karin albashi da alfanunsa da matsalolin da ke tattare da kin biyan karin albashin kamar haka:

Me ake nufi da mafi karancin albashi?

Abin da ake nufi da mafi karancin albashi shi ne haduwa a kan matsaya guda wato albashi mafi kankanta da aka yarda da shi, ma’ana ko a yau aka dauki wani aiki to mafi karancin abin da za a biya shi, shi ne abin da doka ta ambata a lokacin tattaunawa  tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati, misali kamar abin da ake kai a halin yanzu tsakanin Kungiyar Kwadago da Gwamnati.

Me ya sa ma’aikata a Najeriya suke neman a yi musu karin albashi?

Doka ta yi tanadin duba yiwuwar karin albashi duk bayan shekara biyar ga ma’aikata, wato a duba halin da tattalin arziki yake ciki  musamman idan aka samu hauhawar farashin kayayyakin amfani yau da kullum, kamar halin da Najeriya ta shiga a shekarun baya. Ta haka ne za a rage radadin talauci a tsakanin ’yan kasa kuma kudade su rika gilmawa a tsakanin ’yan kasuwa da ’yan albashi.

Sannan idan aka yi karin albashi ga ma’aikata zai sanya musu karsashi wajen jajircewa a kan aikin da ya rataya a wuyansu.

Wadanne matsaloli karin albashi ke dauke da su?

Karin albashi ka iya sa farashin kayayyaki ya tashi, idan ba a dauki mataki ba. Sannan kuma gwamnoni idan suka kasa biyan mafi karanci za su rage ma’aikata, wanda hakan zai kawo tsaiko ga ci gaban tattalin arzikin kasa. Ko kuma gwamnatoci su fara cin bashi domin biyan albashi, wannan ma babbar matsala ce dole sai an yi wa kowace doka tanadi da dubi a tsanaki kafin a soma aiwatar da karin albashin. Dole sai gwamnati ta shigo wajen kula da farashin kayayyaki ta yi dokoki masu alaka da wannan matsala ta haka za a rika rage matsalar  tashin farashin kayayyaki. Idan gwamnati ba ta yi tanadi ba, to karin albashin zai zama kamar an bayar ne da hannun dama an karbe da hagu.

Sannan gwamnatoci su rage kudaden gudanar da gwamnati, ’yan siyasa su rage albashinsu da sauran kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati. Ta haka za a samu rarar kudaden da gwamnati za ta tallafa wa karin albashi musamman gwamnatocin jihohi da na tarraya.

Wace illa rashin biyan karin albashi zai jawo?

Zai jawo illoli  da yawa, da farko zai jawo ficewar kwararru zuwa kasashen waje  kamar abin da ke faruwa yanzu, duk wanda ya kware a wani fannin ilimi da zarar  an yi masa ta yi a kasashen waje za ka ga ya ketare saboda kudin da zai karba a can ya ninka wanda ake ba shi a kasarsa, kamar likitoci da injiniyoyi da sauran fannoni da dama.

Na biyu kuma zai haifar da rashin kwazon ma’aikata za ka tarar ma’aikata ba su da kwazo da karsashi hakan zai hafar da illoli masu yawa daga ciki akwai koma bayan tattalin arziki domin za ka tarar babu kwararru da za su rika kawo sauyi a fannin ci gaban kasa.

Na uku: zai jawo yawaitar yajin aiki shi kuma idan yajin aiki in ya yawaita na iya jawo masassarar  tattalin arziki, masassasarar kuma tana haifar da illoli masu yawa, kuma tana zubar da mutuncin kasa a idon duniya. Masu zuba jari za su yi karanci.

Wace hanya gwamnati za ta bi wajen rage wadannan matsaloli?

Da farko sai gwamnatoci sun rage kudaden tafiyar da gwamnati, wannan shi ne abin da ya jawo wadansu gwamnoni ba sa iya biyan albashi domin suna kashe kudade ta hanyar da ba su dace ba. Sannan Gwamnatin Tarraya ta canja yadda take rabon arzikin kasa ya zama gwmanatocin jihohi su rika samun kaso mafi tsoka domin sun fi kusa da al’umma da kuma kananan hukumomi. Sannan a tabbatar da an yi dokokin kula da tashin farashin kayayyaki, sai bangaren kayayyakin more rayuwa da kuma zirga-rizga wato hanyoyi kamar na layin dogo da sauran hanyoyi da kuma wutar lantarki domin tana taimakawa wajen yin tattalin kayan abinci wajen ajiye su a firiji ta haka za a samu saukin kashe kudade. Kuma zai rage hauhawar farashin kaya.

Sannan gwamnatoci  a dukkan matakai  su rika sanya ido wajen ma’aikatan bogi domin har yanzu ana samun ma’aikatan da babu su kuma wadansu masu hadama suna karbar wannan kudi suna taskancewa a aljihunsu. Idan aka sa ido sosai za a iya samun kudaden da suke zirarewa ta barauniyar hanya.