Rashin cika alkawarin ’yan siyasa ke haddasa rikice-rikice – ACF
Shugaban kungiyar Kare Muradun Arewa Arewa (ACF) reshen Jihar Neja, Malam Baba Abubakar ya ce rashin cika alkawari da ’yan siyasa ke yi wa jama’a yayin yakin neman zabe na daga cikin dalilan da suke haddasa rikice-rikice a sassan kasar nan.Alhaji Baba Abubukar ya bayyana haka ne lokacin da wakilan kungiyar suka yi taro a […]
Shugaban kungiyar Kare Muradun Arewa Arewa (ACF) reshen Jihar Neja, Malam Baba Abubakar ya ce rashin cika alkawari da ’yan siyasa ke yi wa jama’a yayin yakin neman zabe na daga cikin dalilan da suke haddasa rikice-rikice a sassan kasar nan.
Alhaji Baba Abubukar ya bayyana haka ne lokacin da wakilan kungiyar suka yi taro a Gidan Matasa da ke karamar Hukumar Bosso a Jihar Neja, inda ya ce yin haka, ya taimaka matuka wurin jefa wannan shiyya ta Arewa a cikin mawuyacin hali musamman a fannin tsaro da tattalin arziki.
Shugaban ya ce, ya kamata mutanen Arewa su dawo ga akidar da aka sansu tun asali na kwatanta gaskiya a duk inda suka samu kansu, don kuwa su suka sa mutanen sauran shiyyoyin suka yi ta ganin duk wanda ya fito daga Arewacin a matsayin kamilin mutum.
Da yake jawabi, wani jigo a kungiyar ta kasa Janar Muhammad Inuwa Wushishi, ya ce a matsayinsu na dattawa za su ci gaba da bayar da gudunmawar da ta kamata wurin farfado da martabar Arewa kuma ba za su gaji da wannan yunkurin da suka fara ba wanda yake cike da alheri musamman ga na baya.
Janar Inuwa Wushishi, ya ce a shirye kungiyar take ta karbi sababbin wakilan da ke sha’awar shiga cikinta muddin shekarunsu sun haura 30, saboda kowa yana da irin gudunmawar da zai bayar domin kungiyar ta ci gaba da bukasa a matakan jihohi da kananan hukumomin da ake sa ran kafawa nan gaba.
Injiniya Mamman Muhammad ya ce akwai bukatar gwamnatoci musamman na jihohi su tashe tsaye su ba fannin aikin noma kulawar da ta kamata, ba tare da sanya siyasa a cikin lamarin ba. Ya ce, rashin ba manoma isassun kayan aiki musamman takin zamani da maganin kwari yadda ya kamata na ci gaba da zama barazana ga fannin noma da ya kasance a sahun gaba wajen tattalin arziki kafin samun man fetur da ya dauke hankalin hukumomi baki daya a yanzu.
Ita kuwa Fati Eunice Ibrahim, ta nemi matasa a duk inda suke, su daina barin ’yan siyasa suna amfani da su ta hanyoyin da ba su dace ba.Ta ce, ya kamata duk wanda aka nemi ya yi bangar siyasa ya nemi wanda ya sa shi wannan aikin ya gabatar da ’ya’yansa su kasance a sahun gaba.