Rashin ciniki ne ya sa farashin shanu ya sauko – Shugaban mahauta

Shugaban kungiyar mahauta da ake kira International Butchers Association da ke kasuwar abbatuwa a jihar Legas, Alhaji Ado Garba,  ya ce rashin ciniki ne ya janyo farashin shanu ya yi kasa.Alhaji Ado Garba, wanda ake yi wa lakabi da ‘Kowa a ba shi,’ ya  shaida wa Aminiya a karshen makon da ya gabata cewa, rashin […]

Rashin ciniki ne ya sa farashin shanu ya sauko – Shugaban mahauta

Shugaban kungiyar mahauta da ake kira International Butchers Association da ke kasuwar abbatuwa a jihar Legas, Alhaji Ado Garba,  ya ce rashin ciniki ne ya janyo farashin shanu ya yi kasa.
Alhaji Ado Garba, wanda ake yi wa lakabi da ‘Kowa a ba shi,’ ya  shaida wa Aminiya a karshen makon da ya gabata cewa, rashin kudi a hannun jama’a shi ne ya janyo karancin cinikin shanu.
Ya ce, ‘Abokan huldarmu suna gaya mana cewa babu kudi a kasa. Kuma hidimar da suke yi a da, a yanzu ba za su iya yi ba saboda babu kudi a hannun jama’a. Wanda a da yake iya sayen naman Naira dubu goma a yanzu ba zai iya saya ba saboda karancin kudi. Saboda haka mahauta da dillalan shanu mun sha wahala a ’yan kwanakin nan.’
Ya ci gaba da cewa, ‘Tsadar kudin mota ta sanya farashin shanun ya hau, amma a yanzu saboda rashin ciniki farashin ya sauka kadan. Kafin kirsimeti muna sayar da sa Naira dubu 180 zuwa dubu 210, amma bayan kirsimeti farashin ya yi kasa. A da an samu karin Naira dubu goma a kan kowace saniya, amma a yanzu karin Naira dubu biyar ake samu.’
Ya bayyana cewa, dillalai da mahauta da dama sun tafka asara saboda suna yanka shanu amma babu masu saya. ‘Ka san bashi muke sayan nema, mun yanka babu masu saya, Dole ka ajiye cikin dakin sanyi. Kuma ga shi babu wuta sosai, ka ga dole nama ya lalace. Saboda haka idan mahauci ya yi asara dole dillali da falke mai kawo shanu su yi asara, sai dai Allah ya gyara.’ In ji shi