Rashin dacewar hana mata ’yan hidimar kasa (NYSC) sanya hijabi
Malam Abubakar Ishak (08064709454), ya rubuta tsokaci game da wani umarni da Darakta-Janar na Hukumar Masu yi wa kasa Hidima (NYSC) ya bayar a kwanakin baya. Malamin ya yi kokarin bayyana matsayin al’umma da ta addinin Musulunci dangane da sanya hijabi ga mata Musulmi. Babu shakka wannan tsokaci abin nazari ne: A makonni biyu da […]
Malam Abubakar Ishak (08064709454), ya rubuta tsokaci game da wani umarni da Darakta-Janar na Hukumar Masu yi wa kasa Hidima (NYSC) ya bayar a kwanakin baya. Malamin ya yi kokarin bayyana matsayin al’umma da ta addinin Musulunci dangane da sanya hijabi ga mata Musulmi. Babu shakka wannan tsokaci abin nazari ne:
A makonni biyu da suka gabata ne Darakta-Janar na Hukumar Masu yi wa kasa Hidima (NYSC), Mista Johnson Olawuni ya yi kashedin hana mata Musulmi masu yi wa kasa hidima sanya hijabi a sansanoninsu. Ya bayyana cewa, ya dauki matakin ne domin matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a kasar nan.
Al’ummar Musulmin Najeriya na Allah wadai da hana saka hijabi mai tsawo da Daraktan ya yi kuma muna kira ga duk wani mai fada a ji a kasar nan da ya shiga cikin wannan magana domin kiyaye addini da mutuncin ’ya’yanmu mata.
Saninmu ne cewa a shekarun baya, kokarinmu da duk wani kira da muke yi shi ne na yadda ’yan uwanmu mata za su yi karatu, domin cike mana gurbin da su ne ya kamata su cike mana. Bayan wannan kokari, zuwa yanzu alhamdu lillahi, mata sun farka daga barcin da suke yi. An samu mata da dama masu karatu wanda hakan yana faranta ran duk wani Musulmi mai kishin Musulunci. Sa’anan yanzu wani zai zo ya kawo mana yadda za mu saba wa addininmu, ta hanyar fakewa da wani dalili wanda bai da madogara wajenmu kuma mu zura ido muna ganinsa?
Kamar yadda kungiyar Kare Martabar Musulmi (MURIC) ta ce, wannan kira nasa shirme ne kuma bai da wani muhimmanci; sai dai fa idan zai yi amfani da wannan damar don nunawa a zahiri cewa shi makiyin addinin Musulunci ne.
Dalilin da ya bayar na rashin tsaro ba dalilin da za mu dauka ba ne, domin a lokuta da dama ana kama ’yan fashi a kasar nan sanye da kakin ’yan sanda ko na soja amma hakan ba isa a ce an hana su jami’an tsaron saka kakin ba. A daidai lokacin ma, abin ya faru a Jihar Ogun, inda aka yi wa bankuna shida fashi tare da kashe dan sanda da mace mai ciki kuma ’yan fashin sanye da kayan sarki, amma duk hakan bai kawo hana saka kakin ba. Amma saboda tsabar kiyayya ga addininmu shi ne ake neman karya gwiwar wasu daga cikin matan da muka samu suke karatun ta hana sanya hijabi.
Birgediya Johnson da ire-irensu suna so su yi amfani da rashin tsaro da kasar nan take fuskanta wajen bayyana boyayyiyar akidarsu ta kin Musulunci da Musulmi da kuma kunyatar da matanmu, wadanda suke saka hijabi a sansanonin horar da su.
Shin ko Johnson ya san da cewa mata ’yan sanda a Birtaniya suna saka hijabi a saman kakinsu? Ta yaya hijabi zai hana mace mai hidimar kasa gudanar da duk wani abu da ake aiwatarwa a wurin? Muna so ya san da cewa hijabi shi ne mutuncin matan Musulmi. Duk wacce ta san mutuncin kanta da addini, rashin sanya hijabi kan sa ta ji kamar a tsirara take. Bai san matsalar da matanmu suke fuskanta ba ne idan suna zaune haka kara-zube?
Ta yaya iyaye za su bayar da dukkan lokacinsu, karfinsu, kudinsu da sauran abubuwa wajen ba ’ya’yansu tarbiyya a cikin shekaru masu yawa; sa’annan a cikin abin da bai wuce awa 24 ba, wani ya zo ya bata dukkan wannan tarbiyyar da iyaye suka ba su? Wannan lallai rashin adalci ne ga Musulmi da ma iyayen yaran.
Mu idan aka yi mana rashin adalci, a kowane lokaci muka yi magana sai a ce muna neman tashin hankali ko ba mu gane abubuwan da suke gudana. Addininmu shi ne ya koya mana cikakken zaman lafiya da mutunta wanda ba harshenku ko addininku daya ba. Saboda haka Kiristoci da ke yankunanmu suke zaune cikin aminci da kwanciyar hankali, sabanin yadda mu ’yan uwanmu suke fama da rashin kwanciyyar hankali a Kudancin kasar nan.
Shin ya zama wajibi ne don kawai Birtaniya ta rene mu kuma ta ba mu ’yancin kai, mu dauki irin al’adunsu na tafiya cikin tsiraici da sauran munanan dabi’un da suka saba wa addininmu da al’adunmu? Shin sai an tilasta mana yin koyi da yammacin duniya ne kafin rayuwarmu ta gudana cikin kwanciyar hankali da lumana? Ya kamata mu tambaya, wa ya tsara ire-iren yunifom na makarantu da na soja da makamantansu? Shin ba Birtaniya ba ce? Shin duk ’yan Najeriya addininsu daya ne? To, me ya sa ba za a sakar wa Musulmi mara ba domin su gudanar da addininsu a cikin ’yanci da lumana? Me ya sa za a tilasta wa Musulmi ya yi shiga irin ta kafirci a kan dole? Me ya sa ake hana Musulmi more mulkin dimokuradiyya? Duk abin da ya saba wa addininmu, ba mu maraba da shi, muna Allah wadai da shi kuma ba za mu goyi bayan aiwatar da shi ba matukar zai iya kai mu ga saba wa Ubangijinmu.
Abin da zai nuna mana cewa hakan an yi ne da wata manufa shi ne: Me ya sa a yankunanmu irin su Kano, Zamfara da Sakkwato za a bar Musulmi mata su saka hijabi amma a hana su a Kudancin kasar nan? Shin da yankin Arewa da Kudu wanne ya fi fuskantar matsalolin tsaro?
Muna kira ga sarakunanmu, da gwamnoni da masu fada-a-ji a cikinmu su san cewa za a iya kai matasanmu bango har su iya daukar doka a hannunsu, wanda hakan ba zai haifar mana da da mai ido ba.
Ina kira ga dukkan masu yi wa kasa hidima su nazarci ka’idoji da dokokin yi wa kasa hidima, duk inda suka ga ya saba wa addininsu, su kai koke ga inda za a share musu hawayensu, domin kowa yana da ’yancin da zai yi addinin da ya so a kasar nan.
Ina kira ga Darakta-Janar na Hukuma Masu yi wa kasa Hidima ya guji duk wani abin da zai kawo hayaniya, tarzoma ko kuma fitina kan al’amarin hijibi da yake neman aiwatarwa a kan matan Musulmi. Ina kuma so al’umma su san cewa yawan Musulmin kasar nan ya wuce a yi mana wata barazana ko tsoratar da mu a kan wani abu kuma. Ba yadda za mu yi da ranmu, haka Allah Ya so ya gan mu da zama a kasar; don haka mutunta juna da zama lafiya tsakaninmu shi ne mafita a cikin rayuwarmu.