Rashin fahimtar juna ke kawo rudani a cikin al’umma – Gwamna Fashola
Gwamnan Jihar Legas, Mista Babatunde Raji Fashola ya ce rashin zaman lafiya da kasa ke fama da shi, ba kowa ne ya haddasa shi ba, illa ’yan kasa su kansu, domin misali, rikicin addini ba kowa ne ke kawo shi ba, illa mutanen kasar saboda an kasa samun hadin kai da fahintar addinin juna tare […]
Gwamnan Jihar Legas, Mista Babatunde Raji Fashola ya ce rashin zaman lafiya da kasa ke fama da shi, ba kowa ne ya haddasa shi ba, illa ’yan kasa su kansu, domin misali, rikicin addini ba kowa ne ke kawo shi ba, illa mutanen kasar saboda an kasa samun hadin kai da fahintar addinin juna tare da mutunta shi, lamarin da zai kawar da duk wani rudani a cikin al’umma.
Gwamnan yana magana ne sa’ilin da yake karbar bakuncin shugaban cocin Methodist na kasa a birnin Ikko, Dokta Chukwuemeka Uche, inda ya kara da cewa, “Muddin ba za mu dubi kanmu a matsayin ’yan Najeriya ba, wadanda Allah Ya yi mu iri daban-daban kuma a kasa daya ba, to ba shakka har kullum za mu ci gaba da samun matsalalar zamantakewa”.
Gwamna Fashola ya ce nauyin samar da kasa dunkulalliya ya rataya a wuyan shugabanni na kowane jinsin jama’a ko addini, saboda haka ya zama wajibi kowa ya yi bakin kokarinsa wajen ganin an mutanta matsayin kasar ba muzanta ta ba. “Matukar kowa ya sauke nauyin da ke kansa, Najeriya za ta bunkasa. Shugabannin addini na da babban kalubale a gabansu wajen samar da kasa daya dunkulalliya, domin kuwa batunsu tamkar wahayi yake ga mabiyansu, saboda haka akwai bukatar su fahimtar da mabiyan nasu muhimacin mutunta addinin juna da sanin kimar dan Adam.
Gwamnan ya ce da farko shi gidan mabiya addinin kirista ya tashi, har ya kai dan shekara 20 cocin Methodist yake zuwa tare da mahaifiyarsa mai bin addinin kirista, kodayake bayan nan ne ya koma bin addinin mahaifinsa na Musulunci, ga shi kuma matarsa mai bin addinin kirista ce. “Mu a nan Legas, an dan jima da fahintar juna a fannin addin, shi ya sa ba a rikicin addini”. Inji shi.
Shi ko Dokta Chukwuemeka cewa ya yi wanda ya karbi shugabancin cocin daga hannunsa ya yaba da irin rawar da gwamnan ke takawa wajen taimakon cocin, saboda haka ya yi fata shi ma zai samu irin wannan taimakon.
Ya ce kusan kowa na koyi da Gwamnan Fashola saboda irin ayyukansa da kuma tsarin tafiyar da mulkinsa, musamman wajen nada wadanda ma ba ’yan kabilar Yarabawa ba a matsayin kwamishina da mai ba shi shawara, irin shugabannin da Najeriya ke bukata ke nan.