Rashin fasahar zamani ne ya sa manoman Afirika zama a talauce – James Nyoro
Shin za ka iya bayyana mana ayyukan da asusun nan yake gudanarwa?Shi wannan asusu wata kafa ce mai zaman kanta wacce aka kafa ta don tallafa wa masu rauni da marasa galihu su gudanar da rayuwa mai inganci. Muna da shirye-shirye da ayyuka da muke gabatarwa da suka hada da bangaren lafiya, muna da shiri […]
Shin za ka iya bayyana mana ayyukan da asusun nan yake gudanarwa?
Shi wannan asusu wata kafa ce mai zaman kanta wacce aka kafa ta don tallafa wa masu rauni da marasa galihu su gudanar da rayuwa mai inganci. Muna da shirye-shirye da ayyuka da muke gabatarwa da suka hada da bangaren lafiya, muna da shiri na kawar da cutar foliyo da kawar da cutar kanjamau da kuma samar da rigakafin cutar maleriya da sauransu. Muna da sashe na bunkasa kasashe. Abin da muke yi a nan shi ne mu samar da hanyoyin samun kudi ga talakawa ta hanyar wayar salula da tallafi ta hanyar kungiyoyi. A bangaren noma kuwa muna tallafa wa kananan manoma ta hanyoyi masu yawa.
Wane kalubale kananan manoma suke fuskanta a nahiyar Afirka?
kalubalen da suke fuskanta shi ne na rashin samar da isasshen abinci kuma wannan dalilin ne ya sanya mafi yawansu suke cikin talauci. Wannan dalili ne ya sa asusunmu ya shigo cikin al’amarin inda muka hada gwiwa da kasashe guda uku da ke Nahiyar Afirika. Kamar kasar Najeriya da Tanzaniya da kuma kasar Itofiya don mu ga yadda za mu bunkasa harkokin nomansu. Ba ma za mu tsaya a nan ba kawai za mu bunkasa kudin shigarsu da samar da ayyukan yi.
Ta yaya za ku cin ma wannan buri a wadannan kasashe uku?
Akwai matakai guda uku da muka tsara. Dalilin da ya sa manomanmu na Afirika ba su iya noma isasshen kayan abinci shi ne rashin kimiyya da fasaha dangane da abin da ya shafi takin zamani da iri da kayan noma da makamantansu.
To ta yaya za ku tabbatar da cewa an samar da wadannan kayayyakin noma na zamani?
Muna da wani tsari na noma da muke kira tsarin samar da irin shuka daba-daban. Saboda haka muna aiki kafada da kafada da gwamnati don mu tabbatar cewa manoma sun ci gajiyar wannan shiri. Ka sani sarai a wannan kasa akwai wani shiri da gwamnati ta bullo da shi na rage tallafin noma inda ake ba manoma tallafin kayan noma cikin farashi mai rahusa. Muna aiki kafada da kafada da ma’aikatar noma da bunkasa karkara ta kasa don tabbatar da cewa ta bi abubuwanta daki-daki bisa tsari don cin ma burin da aka sanya a gaba na bunkasa noma da manoma a Najeriya.
To amma gwamnati tana ikirarin ba ta da isassun kudi, ta yaya za a cin ma wannan buri?
Haka ne amma kudi ai suna bangaren da ba na gwamnati ba, to amma tsarin da muke bi a yanzu ba zai iya zama mai gamsarwa ba idan aka yi la’akari da harkokin sanya hannun jari a yanzu. Muna aiki tare da gwamnati don ganin yadda za mu gyara wannan tsari ta yadda masu sanya hannun jari za su samu damar zuba jari. Misali, zai iya kasancewa kawai iri mai yawa amma yadda kamfanonin samar da iri za su bunkasa shi su sayar da shi ga manoma, wata babbar matsala ce. Saboda bunkasa kamfanoni masu zaman kansu wani babban kalubale ne.
Wace hanya kuke bi wajen ganin an yi maganin wannan kalubale?
Abin da muke yi shi ne mu ga an samu hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi da Gwamnatin Tarayya. Gwamnatin Tarayya tana yin dokoki kuma tana ba jihohi kudi su kuma gwamnoni su ne suke da ta cewa dangane da harkokin noman jihohinsu. Shi ya sa muke kokarin ganin an samu daidaito ta yadda za a rika yin abu bai daya don cin ma burin da aka sanya a gaba na bunkasa noma da samar da abinci a kasa baki daya.
Ka bayyana cewa noma mai dorewa shi ne hanyar da zai fitar da mutane daga talauci, me kake nufi da haka?
Kashi 70 cikin dari na al’ummar Najeriya manoma ne da ke rayuwa a yankunan karkara. Za ka ga cewa tattalin arziki kasar yana bunkasa ba tare da mafi yawan al’ummar kasar ba. Za ga ka cewa tattalin arziki yana karuwa ne da fannin sadarwa da sauransu ba tare da fannin noma ba. Ka ga ke nan kana da tattalin arziki mai bunkasa amma ba tare da mutane ba. To, wannan shi ya sa muka ce dole mu bunkasa mutanen karkara ta hanyar noma. Ta haka ne za mu fitar da su daga cikin talauci da kaka-ni-kayi. Shi ya sa a yanzu Najeriya take kashe kimanin Dalar Amurka miliyan 20 wajen sayen shinkafa da kaji da sauran abubuwan da kamata ya yi a ce ana samar da su a kasar. Ka ga hakan yana fitar da ayyukan yi da tashe kafofin samar da jari da rage zaman banza a tsakanin al’umma.
Me kake ganin shi ne babban kalubalen da Najeriya ke fuskanta a bangaren noma?
Gwamnati ba ta mayar da hankali a kan bangaren noma saboda tana samun kudi a wasu bangarori kamar man fetur. Amma a baya kasar tana tabuka abin a-zo-a-gani a bangaren gyada da koko da sauransu. Saboda haka rashin kulawa daga bangaren shugabanni wanda zai tsaya tsayin daka ya ce zai yi aiki saboda talakawa shi ne aka rasa. Na biyu shi ne rashin hadin kai na bai daya. Kun ce za ku yi noman rogo a Jihar Kaduna amma ba ku bin diddigin lamarin, ba ku bincikar mutane da kuka ba amana. Saboda haka wadannan su ne dalilaina da ke mayar da harkokin noma baya a Najeriya. Amma a yanzu muna ganin akwai alamun karfafa gwiwa. Wannan gwamnati da alamu tana da niyyar inganta harkokin noma a kasar nan.
Shin kana nufin kudin da aka ware wa bangaren noma ya yi kadan, saboda haka gwamnati ta kara kudi?
Makon da ya gabata mun tafi kasar Itofiya tare da tawagar Ministan Noma na Najeriya. Dalili shi ne kasar, Itofiya tana daga cikin kasashen da suke kokari a bangaren noma kuma sun yi amfani da noma wajen rage radadin talauci a tsakanin talakawansu. Abin da suka fada mana shi ne, Gwamnatin kasar Itofiya ta ware kimanin kashi hamsin da biyu na daukacin kasafin kudinta ga bangaren noma, ban san kashi nawa Najeriya ta ware ba amma dai na san bai zai wuce kashi biyar ba na kasafin kudinta. Idan kana so ka ga ci gaba dole ka kashe kudi mai dimbin yawa. A shekarun baya gwamnatoci ba su ware kudi masu yawa a bangaren noma, haka yake a jihohi. Dole sai mun sanya kudi masu yawa a bangaren noma sannan za mu cin ma burin da aka sanya a gaba.