Rashin hadin kai ne babbar matsalarmu – Ado Mai Jos

Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Jarkoki ta Jihar Kuros Riba, Alhaji Ado Muhammed Mai Jos ya koka kan rashin hadin kai da kyashin juna da ke addabar al’ummar Arewa mazauna Kalaba inda ya ce  su ne manyan matsalolin da suke ci musu tuwo a kwarya. Ado Mai Jos ya fadi haka ne a yayin zantawarsa […]

Rashin hadin kai ne babbar matsalarmu – Ado Mai Jos
Rashin hadin kai ne babbar matsalarmu – Ado Mai Jos

Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Jarkoki ta Jihar Kuros Riba, Alhaji Ado Muhammed Mai Jos ya koka kan rashin hadin kai da kyashin juna da ke addabar al’ummar Arewa mazauna Kalaba inda ya ce  su ne manyan matsalolin da suke ci musu tuwo a kwarya.

Ado Mai Jos ya fadi haka ne a yayin zantawarsa da Aminiya a Kalaba, ya ce, “Babbar damuwar da muke da ita a kasuwarmu ta roba musamman ta nan Kalaba ba ta wuce hassada da kyashin juna da kuma rashin hadin kai ba, wacce muke rasa ’yancinmu da doka ta ba mu a matsayin al’ummar kasar nan,” inji shi.

Sai ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar su farka daga barcin da suke yi a tsawon lokaci, wanda a cewarsa ba haka sauran kabilu suka zaune kara-zube kamar Hausawa ba.

Ya ce “Mu sani cewa muna da hakki kamar kowa, ya kamata mu hada kai don cimma nasarar kasuwancin da muke rayuwa da shi. Domin ribar da ake samu a harkar nan ba ta wuce Naira 20 kowace jarka ba, amma rashin hada kai ya na haddasa mana nakasu cikin kasuwancin.”

Alhaji Ado Mai Jos ya kara da cewa ya yi iyakacin bakin kokarisa wajen ganin ’yan Arewa da ke karkashin shugabancinsa sun hada kai, amma a cewarsa ana bijire wa hakan.

Ya ce idan akwai hadin kai, to za a iya shawo kan kowace irin matsala da take addabarsu, amma yadda kowa ke cin gashin kansa, alamun rashin nasara ce gare su bakin daya.

Ya ce musamman ma matsalar kudin jangali da harajin da ake addabarsu da su, a duk lokacin da suka dauko kaya daga Arewa zuwa Kudu domin kasuwanci, abu ne da za a magance idan akwai hadin kai.