Rashin hadin kai ne matsalar mawakan Hausa – Murja Baba

A kwanakin baya ne mawakiyar Hausa ta zamani, Murja Baba ta ziyarci garin Sakkwato. A ganawarta da wakilinmu, zabiyar ta yi bayani gamsasshe game da sana’arta ta waka, sannan ta bayyana abin da ke ci wa mawakan zamani tuwo a kwarya. Ga yadda tattaunawar tasu ta gudana: A matsayinki na mawakiyar fina-finan Hausa da ta […]

Rashin hadin kai ne matsalar mawakan Hausa – Murja Baba
Rashin hadin kai ne matsalar mawakan Hausa – Murja Baba

A kwanakin baya ne mawakiyar Hausa ta zamani, Murja Baba ta ziyarci garin Sakkwato. A ganawarta da wakilinmu, zabiyar ta yi bayani gamsasshe game da sana’arta ta waka, sannan ta bayyana abin da ke ci wa mawakan zamani tuwo a kwarya. Ga yadda tattaunawar tasu ta gudana:

A matsayinki na mawakiyar fina-finan Hausa da ta dade cikin harka a wannan zamani, wadanne abubuwa ne kike ganin suna yi maku tarnaki wajen ci gabanku?

Da farko dai sunana Murjanatu Yakubu Baba, waddda aka fi sani da Murja Baba ko ’Yar Baba. To gaskiya abu daya ne ke yi mana tarnaki da ke hana mu ci gaba, wanda har yanzu mun kasa magance shi. Hadin kai babu shi a cikin harkarmu. Duk abin da ba ya da shugabanci akwai matsala kuma ba za a taba hada kai ba. Wannan shi ke jawo mana duk matsalolin da ke addabar mu a cikin masana’antar wakokin Hausa na fim. Mu da takwarorinnmu na sauran kasashe muna da tsari iri daya amma duk sun fi mu ci gaba, don kawai ba mu da hadin kai; ga kuma hadama. Za ka ga mutum daya shi ke kida da waka da sarrafa wakar, wato babu wani mai ba shi umarni. Ba ina nufin wai na ce wannan ba kwarewa ba ce, sai dai abin nan ya hana mana karko, don mawakan kasashen waje za ka ga akwai mai shiryawa daban da mai rubutawa daban da mai gyara murya da mai kida duk daban, to amma mu ba mu yin haka; mutum daya zai hade wadannan duk shi kadai. Ka ko ga babu batun inganci a nan, da mun yi abu lokaci kadan sai ka ga ya bace, don babu jagoranci. Wasu na ganin wannan wayewa ce, wallahi wannan shirme ne. Abun da muke yi na kwakwalwa ne, yana bukatar taimako da tsari da hankali, ba komai a ce kai kadai za ka yi ba.

Bari mu dan koma baya, shin me ya ja hankalinki har kika shigo harkar wakokin fim na Hausa?
Haka ne gaskiya, ni tunda na taso ina sha’awar wakoki tun ban san mene ne burgewa ba, na tsinci kaina mai yawan son rera wakoki har a makaratar Islamiyyar da nake karatu ni ake ba kasidu ina rerawa a lokacin Mauludi. Haka a makarantar kwana da na yi, in za a ba da hutu mukan yi wakoki. A haka ne na tashi da waka har zuwa yanzu, na yi wakoki da ban san adadinsu ba; don duk wanda ya ce na jero su ya hada ni da aiki. Ko tun daga 2000 in na dauko zuwa yanzu, shekara 15 kuma ba a lokacin na fara waka ba. Na yi wakar ‘Fifita Mana Shayi’ da ‘Zarafin kauna’ da wakokin ‘Daham’ da Yakubu Muhammad da ‘Kwalli Ya Sa Ido Shanawa’ da ‘Jarumai Sun Karya Alkibla’ ga su nan da yawa, ba zan iya kirga su ba. A lokacin duk wakar da ka ji Yakubu Muhammad ya yi to tare da ni ce ya yi su, irinsu ‘Gara Aka Mini Gara Ake Shirin Aure’ da sauransu. Haka mawaki Adamu da Abubakar Sani duk mun yi wakoki kamar ‘Bakin ganga’ da ‘Sakalim Baye Ayyara Iyye Salim Baye’ da sauransu. Sani Danja ma wakokin ‘Babbar Riga’ da ‘Gurgu Mai Dala’ tare da ni ya yi su. In ka dawo wurin sababbin mawaka irin su Umar M. Sharif a wakarsa ta fim din Hallacci, mai taken ‘Ka Daure Ka Yi Min Hallacci’ da Adamu Nagudu, wakokin fim din Sirri na kwanan nan, tare muka yi. Hussaini Danko, wanda kusan yanzu na fi waka da shi, mun yi wakoki kamar ‘Tafiya Da gwaninka’ da ‘Basajarmu A So’ ‘Saura kiris’ da ‘Ga Dodon Maza’ duk dai ga su nan ba adadi; ga su ‘So Aljanar Duniya.’ In takaita maka, duk mawakan da da na yanzu, ba wanda ba na waka da shi. Ga shi yanzu ina Sakkwato, Kabiru Bisibul ne ya kirawo ni don yi masa waka.

Akalla kin fi shekara 15 kina wakoki, wadanne irin kalubale ne kike fuskanta a harkar sana’arki?
kalubale dole ne mutum ya rika fuskanta a kowace harka ta nema amma wadda ta fi damuna ita ce kallon da ake yi mana a gari a matsayin ’yan iska, lalatattu. Muna da iyayenmu da komai, sana’a muke yi kamar mata masu aikin jinya da ma’ikatan banki duk da maza da mata suke yinta, sai dai su ba a kiransu da ’yan iska sai mu. Hakan bai dace ba, domin ni a gaban mahaifana nake, uwata da ubana duka suna raye kuma idan ba ni da aiki ban fita ko’ina kuma da na kammala zan dawo. Gaskiya sunan ’yan iska da ake kiran mu ya dame ni.

A cikin wakokinki ko akwai wadda ta fi ba ki wahala ko take burge ki?
Ni Murja Baba, ba na yin wakokin batsa kuma hasalima ba wata waka da ke ba ni wahala, sai dai in mutum ya soma fara waka takan yi masa tarnaki kadan. Wakar ‘Zarafin kaun’a da muka yi da Adamu Nagudu ta ba ni wahala sosai. Na yi awa hudu a wurin yinta, na kasa gane inda matsalar take; rashin sabo ne ko wakar ce mai wahala? Tun da akwai wakoki masu wahala. Wakar da na fi so da take burge ni ita ce ‘Na rike Manzon Allah Na So Annabi Mai Kyauta, Zuciya Kullum Kwadayinta Annabi Ne Shar Shar.’ Wannan wakar ita ce ta sanya tsohon Shugaban Majalisar Kano ya biya min aikin Hajji, sai kuma wakar da na yi wa masoyana. Ina kaunar wakar da alfahari da ita, domin masoyana su ne mu, da za su sanya a yi alfahari da kai. Ga yadda wakar take: ‘Jinjina masoyana Murja Baba, ina murna gaisuwa cikin murna domin kuna muradina, addu’a kuke guna Allah sa mini albarka.’

Mawaka kuna baya idan an hada nasarorinku da na masu shirya fina-finan Hausa, me ya janyo haka?
Har yanzu zan mayar da kai baya, mu mun rasa jagoranci ne; ba mu da shugaba. Abin da ya cuce mu ke nan, dole tilas da’iman mu yi shugaba in dai muna son ci gaba. A nan ina kira ga mawaka manya da kanana da su zo mu hada kanmu, mu yarda da shugabanci, don rashin yin haka ba mu da in da za mu je. Gwamnati ta ba da tallafi don rashin kungiya muka rasa wannan tallafin. A can baya mun taba kafa kungiyar Inuwar Fasaha, wadda ke dauke da duk manyan mawakanmu, aka yi shugaba na farko Sadik Zazzabi; rasin hadin kai ya tarwatsa tafiyar. Yanzu an sake farfado da ita karkashin jagorancin Misbahu amma dai har yanzu tana masassara. Kira na ga mawaka da su yarda da shugabanci don samun nasararmu.

Ko kina da alaka ta jini da Maryam A. Baba?
Gaskiya ba ni da wata alaka da Maryam A. Baba ta jini sai dai ’yar uwar sana’ata ce kawai kuma mun fi mu’amala da ita bisa ga sauran mawaka. Rayuwar waka ce ta hada mu kawai. Ita da Zainab A. Baba ce suke uwa daya uba daya, ba da ni Murja Baba ba. Sa’annan ina kira ga ’yan uwana mawaka mata da su kare kansu da mutuncinsu in aiki ya zo mana mu yi yadda ya kamata, ba cuta ba cutarwa. Mu damke amanar junanmu, kar mu cutar da kanmu. Allah Ya saka wa kowa da alheri har mawaka maza domin ni ina da kyakkyawar alaka da kowa. Su kuwa masoyana, na gama ba su sako don na ce masu alkawari na dauka zan so su kamar ni kaina, addu’ar da suke yi mini ina gani; Allah Ya saka masu da alheri sosai.