Rashin hadin kan malaman Najeriya zai sake jefa Musulmi cikin bala’i- Sarkin Arewan Bauchi

A ranar Arfar aikin hajjin da ya gabata ne malaman Najeriya da suka hada da Izala da kuma darika da sauransu suka yi taron sulhu da kuma yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, sai dai jim kadan bayan malaman sun dawo gida sai Sheikh dahiru ya kira taron ‘yan jarida ya ce wannan taron dai […]

Rashin hadin kan malaman Najeriya zai sake jefa Musulmi cikin bala’i- Sarkin Arewan Bauchi
Rashin hadin kan malaman Najeriya zai sake jefa Musulmi cikin bala’i- Sarkin Arewan Bauchi

A ranar Arfar aikin hajjin da ya gabata ne malaman Najeriya da suka hada da Izala da kuma darika da sauransu suka yi taron sulhu da kuma yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, sai dai jim kadan bayan malaman sun dawo gida sai Sheikh dahiru ya kira taron ‘yan jarida ya ce wannan taron dai karya ne da yaudara. A wannan tatttaunawar da Aminiya ta yi da Sarkin Arewan Bauchi kuma Shugaban kungiyar samar da zaman lafiya da kuma kyakkyawan mulki a Arewa, Alhaji Hassan Muhammad Sharif ya ce rashin hadin kan malaman babban bala’i ne ga Musulman Najeriya.

 

Me za ka ce dangane da takaddamar da ta kaure tsakanin malaman Izala da na darika tun bayan da suka dawo daga aikin Hajji?
A gaskiya babanmu Sheikh dahiru bai kyauta ba, domin a ka’idar shugabanci duk wani malami ko almajiri shi shugabansa ne. Bai kamata ya yi haka ba; kamata ya yi idan wasu suka yi abin da bai dace ba sai a zo wurinsa shari’a, ya dauki matsayin uba ga dan izala da kuma dan darika. Zai iya kiran sarki ko mataimakin shugaban kasa ya yi masa nasiha kan abin da ya yi ba daidai ba. Muna girmama shi don haka ina fata nan gaba irin wadannan maganganu ba za su rika fitowa daga bakinsa ba. Batun ya ce ba za su zabi dan izala ba bai taso ba, domin ba abin da Musulunci yake fuskanta ba ke nan; Musulunci na bukatar hadin kai domin a yanzu a Najeriya da ma duniya gaba daya an sa musulunci a gaba. Ya kamata malaman sun hada kansu su gane idan suka rarrabu to hakan ba karamin bala’i ba ne ga Musulmi. Akwai Sheikh Loko da ya mayar da martani a ciki ya kafirta ‘yan darika to hakan bai dace ba, hadin kai ake nema. A yanzu an daina samun littafin Jawahirul ma’anin da aka ce an rubuta salatin da ya fi kur’ani sau dubu shida. Ko a malaman darika ban taba jin wanda ya fito wa’azi yake cewa an samu abin da ya fi kur’ani sau dubu shida ba, idan ma an fada ai yanzu ba a fada. Na yi tsammanin Sheikh Loko ya zai kawo abin da zai zama gyara sai kuma ya sake zafafa abin, hakan bai dace ba. Ina fata za su gyara su hada kai don musulunci ya samu murya daya, kazafi da yarfen da ake yi wa musulunci a daina, sannan su rika yi wa shugabannin wa’azi don su rika tafiya a turbar daidai.
Me za ka ce dangane da takaddamar da ake yi a kan matsayin shariftaka?
Ko don akwai sharif a cikin sunana ne ya sa ka yi mini wannan tambayar? Ni ban ga abin takaddama ba domin ba wai abin alfahari ba ne ka ce kai wane ne ko dan wane ba ne. Manzon Allah (SAW) ya ce abin alfahari gare dan Adam shi ne imaninka da koyi da manzon Allah (SAW) da kuma uwa uba tsoron Allahnka. Allah (SWT) Ya ce Ya halicci wuta ga duk wanda ya saba masa, sai annabi ya ce ko da kuwa Balaraben Bakuraishe ne. Ya kuma halicci aljanna ga duk wanda ya bauta maSa, ko da bawa ne daga kasar Habasha, domin a lokacin babu wadanda ake gani da kaskanci kamar mutumin Habasha. Don haka ba abin alfahari ba ne ka ce kai sharifi ne, abin alfaharinka shi ne kusantarka da Allah da kuma koyi da manzonSa. Za a iya samun sharifai a Kano ko Maiduguri. Duk wanda ya san yadda Annabi da sahabbansa suka rayu ba zai yi shakka don an samu sharifai a Kano ko Maiduguri ba. Sahabbai sun yi yawo cikin duniya wajen daukaka addini kuma ba sa kyamar duk wanda ya musulunta baki ne ko fari, duk wuraren da suka ziyarta sun yi aure kuma sun aurar. A fahimta sahabban manzon Allah su goman nan duk kusan ‘yan uwa ne, akwai dangantaka mai karfi da ta hada su, sun kuma auri mata uku zuwa hudu ba tare da bambanci yare ko launin fata ba. Mutanen Maiduguri suna da alaka da sahabbai, haka ma Kano, sun aura a Kano, sun kuma aurar. Akwai wanda ya ce manzon Allah mai yankakke baya ne, Allah da Kansa Ya ce annabi ba mai yankakken baya ba ne, wanda ya fada shi ne mai yankakken baya. Annabi ya ce burinsa zuri’arsa ta fi ta kowane annabi yawa, don haka idan aka auna wadannan maganganu za ka gane idan an samu zuri’arsa a Kano da Maiduguri ba zai zama abin mamaki ba. Don haka bai kamata masu cewa su sharifai ba ne su buge da wakake ba tare da suna koyi da irin ayyukansa ba, ba daidai ba ne sharifai su zauna su rika cewa a ba su don darajar kakansu, dukanmu al’umma daya ne daga Annabi Adamu muke .
A kullum rikicin PDP yana kara tsanani yake yi kasancewarka dan jam’iyyar me za ka ce kan hakan?
Wannan al’amari zai kawo cikas, a jam’iyya ko mutum daya ne yake adawa ai gibi ne ballantana gwamnoni har bakwai da kuma wadansu jiga-jigai. A gaskiya PDP tana da kura-kurai, amma ta kasa gano su. Kullum tana duba wa take so ne ba wanda yake son ta ba. Ba na goyon bayan bangaren Bamanga ko na su Kwankwaso domin duk tafiyarsu daya ce. Kowane bangaren da irin kuskurensa. Abin da nake fata shi ne a daina bakaken maganganu da kuma saurin fita daga jam’iyya da sauransu. Kamata ya yi a yi zaman gaskiya don a kawo karshen al’amarin, sannan su shawo karshen fatara da talauci da suka addabi talakawa.
Tun da rikicin PDP na kara kazanta ba ka ganin hakan zai iya ba Jam’iyyar APC nasara a kan jam’iyyarku?
Nasara daga Allah take, don haka duk wanda ya ce maka abu zai yiwu ko ba zai yiwu ba ya jahilci matsayin ubangiji. Abin da na sani shi ne adalci na tabbatar da mulki, zalunci na kawo karshen mulki.
A yanzu shugaban Jonathan ya nemi a kara wa’adin dokar ta baci a jihohin Yobe da Barno da kuma Adamawa, ko ka goyi bayan hakan?
A gaskiya ban goyi baya ba. Idan ka lura abubuwan sun yi sauki, kuma ya kafa kwamitoci, yana nufin ba su yi amfani ba ke nan? Talakawa suna cikin matsi kuma na sake matsa musu.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50