Rashin hadin kan shugabannin Fulani ne matsalarsu

Alhaji Muhammadu Usaini Sarkin Fulanin Buzaye shi ne Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore reshen Jihar Bauchi, a zantawar da ya yi da manema labarai ya ce rashin hadin kai a tsakanin shugabannin kungiyoyin Fulani ne matsalarsu:   Mene ne makasudinka na ganawa da manema labarai? Abin da ke tafe da ni damuwarmu ce ta […]

Rashin hadin kan shugabannin Fulani ne matsalarsu

Alhaji Muhammadu Usaini Sarkin Fulanin Buzaye shi ne Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore reshen Jihar Bauchi, a zantawar da ya yi da manema labarai ya ce rashin hadin kai a tsakanin shugabannin kungiyoyin Fulani ne matsalarsu:

 

Mene ne makasudinka na ganawa da manema labarai?

Abin da ke tafe da ni damuwarmu ce ta Fulani wadda rashin hadin kai ne abin da ke hana mu ci gaba kuma rashin hadin kan na shugannin kungiyoyin Fulani ne. Yadda Fulaninmu suka raba kansu kungiya daban-daban inda za ka ji wannan ya ce Kautal Hore yake wancan ya ce Miyetti Allah, wannan rarrabuwar kai  ne ya haddasa mana wannan matsala da Fulaninmu suke ciki.

Wasu matsaloli ne kuke fuskanta?

Matsalolin da muke fuskanta a Najeriya suna da yawa, kashi na farko yadda ake yayata Fulani su ne masu garkuwa da mutane, har yanzu shugabannin Fulani ba su zauna sun hada kansu suka fuskanci abin da yake faruwa ba. Na biyu yadda aka karbe mana dazuzzukan kiwo, har yanzu babu wani abu da aka fitar a kai. An yi tituna an toshe mana hanyoyi daban-daban, yadda ake samun matsalar makiyaya da manoma har yanzu ba a zauna an fitar da wani abu takamaimai guda ba.

Me ya jawo rashin hadin kan Fulani?

Matsalar ita ce gwamnati ma ta rasa kungiya daya da za ta rike, yau wadancan su ce su ne, gobe wadansu za su zo su ce su ne. Wato manufa ce ta rarraba kanmu don a raunata karfinmu domin mu Fulani mun fi kowace zuriya yawa a Najeriya.

A yanzu kungiyoyi nawa kuke da su masu rajista?

Muna da manyan kungiyoyi masu rajista kamar Miyetti Allah Cattle Breeders da Miyetti Allah Kautal Hore da sauransu.

Ta ina kake gani Shugaban Kasa zai iya shigowa wannan magana?

Wannan abin ya shafi  Bafulatanin da ke kauye da birni da sauran makiyaya da ’yan kasuwa. Ba ma a Najeriya ba, a Afirka duka ba wanda ya kai su yawa. Yanzu haka akwai abin da ke faruwa, idan aka ga Bafulatani ya shigo gari, kawai sai ’yan sanda su kama shi bai san komai ba, sai a ce ai mai garkuwa da mutane ne, sai a ce belinsa Naira dubu 500. Akwai masu yawo a mota suna ganin Bafulatani sai su kama shi kawai, idan ba ka kawo kudi kaza ba za a rubuta maka laifi kaza, yanzu wani bangare na hukuma sun koma kasuwanci da Fulani.

Kun taba samun Kwamshinan ’Yan sanda kuka shigar da koke kan haka?

Mun kai kukanmu wurare daban-daban. Koda aka kama mutanenmu a nan jihohin Arewa maso Gabas aka tura su Abuja haka aka je aka karbo su Naira dubu 300 wadansu ma har dubu 500.

Kun yi hadakar kungiyoyi inda suke haduwa karkashin kungiya daya, wannan bai magance matsalarku ba?

Mu a jihohi mukan hada kai, amma manyanmu da ke sama su ne ba su iya hada kai. Sai muka ga cewa idan wadancan sun je sun samo wani abu sai wadancan ma su ce ga shirinsu. Sai ya kasance ba za su iya tsayar da magana daya ba. Kuma ya kamata su gane wannan abin da suke yi suna cutar da al’ummarsu ce, ya kamata su koma jagoranci nagari shi ne abin da zai fitar da mu. Shi ya sa muke so a samu Shugaban Kasa ya shiga tsakani a samu hadin kai da zaman lafiya.

Ta yaya rashin hadin kan yake shafar harkokin kiwo?

Ka ga wannan gwamnati ta kai shekara biyar da kafuwa amma yanzu mu al’ummar  Fulani ba abu daya da za mu ce ga shi an yi mana. Kuma ya kamata ko burtali ne a ce an fitar daga nan zuwa Legas ya yi Fatakwal. Fulanin nan mutane ne da suke kawo ci gaba a jihohin nan inda za a fahimci Bafulatani a Najeriya, amfaninsa ya fi na kowace kabila. Yanzu ka dauki mahauta a nan Najeriya, miliyan nawa ne suke karkashinmu suna da gidajensu da motocinsu? Kuma ka dubi yadda muke tallafa wa bangaren takin gargajiya, akwai jihohin da ba su amfani da takin zamani idan Fulani sun sauka a gonarka kawai shi ke nan. Ba zai yiwu muna da sana’armu kuma muna cewa a taimake mu kuma a ce wai mu bar sana’armu, anya zai yiwu? Fulani kashi uku ne a Najeriya, na farko akwai Fulani da suke zaune ne a wuri daya, akwai Fulani masu labi su kuma za su tafi su dawo su tafi ci-rani, akwai kuma Fulani na cikin gari. Fulani masu labin nan yaya za a yi gwamnaati ta tallafa musu, shi ne abin da muke so gwamnati ta shigo. Shi Bafulatani idan ka yi aikin labi bai damu da sauran  abubuwa ba.

Matsalar laifuffuka da ka ce ana zargin Fulani ana zaluntarsu yaya kake gani gwamnati za ta shigo lamarin?

Wannan kuma abin da muke so gwamnati ta yi shi ne su jam’ian tsaro ba abin da ba su sani ba, in dai mutum na jin harshenmu kawai yana yin wani abu sai a ce Bafulatani ne. Wadansu kuma sukan saka riga irin ta Fulani ko su sa rawani sai a ce Bafulatani. Muna so a bambanta mu da wadannan abubuwa, sannan ya kamata ku ’yan jarida ku yi mana adalci, babu kabila daya da za ta yi laifi sai a ce su ne kadai. Muna so idan mutum ya yi laifi, sunansa Umar to a ce Umar ya yi laifi ba Bafulatani ba, idan ka ce Bafulatani ka dauki al’ummar ce baki daya.