‘Rashin haihuwa ya sa ni sace jariri’
Wata mata mai kimanin shekara 30 da ta shiga komar ’yan sanda a Jihar Kano bisa zargin sace wani jariri dan kwana daya da haihuwa a garin Gwarzo cikin Jihar Kano, ta ce rashin haihuwa ce ta sanya ta sace jaririn. Matar mai suna Bara’atu Mohammed ana zarginta da sace jaririn ne a lokacin da […]
Wata mata mai kimanin shekara 30 da ta shiga komar ’yan sanda a Jihar Kano bisa zargin sace wani jariri dan kwana daya da haihuwa a garin Gwarzo cikin Jihar Kano, ta ce rashin haihuwa ce ta sanya ta sace jaririn.
Matar mai suna Bara’atu Mohammed ana zarginta da sace jaririn ne a lokacin da mahaifiyarsa ke hutawa a dakin haihuwa na Babban Asibitin Gwarzo, inda ta tafi da shi gida ya yi kwana uku a hannunta ta saya masa kayan jarirai da sauransu kafin daga baya wani dan uwnta ya tilasta mata mayar da jaririn wurin da ta sato shi.
Wanda ake zargi da sace jaririn, ta ce, “Na yi aure tsawon shekara 16 amma Allah bai ba ni haihuwa ba, domin an gaya min ba zan taba haihuwa ba, hakan ya sa na zo asibitin na dauki jaririn.”
A nata bangaren mahaifiyar jaririn mai suna Jamila dahiru ta yi wa Aminiya karin haske kan yadda aka sace jaririnta inda ta ce matar ta yi mata karya ne cewa kakarta ta nemi a kai mata jaririn waje don ya sha iska. “Ban san cewa satar jaririn za ta yi ba, ina kwance a dakin hutu, sai ga wannan matar ta shigo ta ce, wai inji kakata Dije ta ce na bayar da jaririn a kai shi waje don ya sha iska. Ni kuma jin haka sai na ce mata ga shi nan ta dauke shi. Daga nan ta dauke shi ta fice daga dakin,” inji ta
Mai jegon ta kara da cewa, “To sai bayan an dauki wasu mintoci sai kakata ta shigo dakin tana tambaya ta jaririn, sai na gaya mata cewa yana wurin matar da ta aiko ta karbe shi. A nan ne kakata ta ce ita ba ta turo kowa ya karbi jariri ba. Daga nana ne muka gane cewa matar karya ta yi in don ta sace jaririn.”
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka damka jaririn ga mahaifiyarsa, kuma za su gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu don fuskanta shari’a.