Rashin hakuri ne ya sa likitoci shiga yajin aiki a Kaduna – Kwamishinan Lafiya
Kwamishinan Kula da Kiwon Lafiya na Jihar Kaduna Dokta Paul Dogo ya bayyana cewa rashin hakuri ne ya sa knngiyar Likitoci na jihar suka shiga yajin aiki. Kwamishinan ya kuma sanar da hakan ne a zantawarsa da Aminiya jim kadan bayan kammala wani taro a kan inganta sashen lafiya da aka yi a jihar. Aminiya: […]
Kwamishinan Kula da Kiwon Lafiya na Jihar Kaduna Dokta Paul Dogo ya bayyana cewa rashin hakuri ne ya sa knngiyar Likitoci na jihar suka shiga yajin aiki. Kwamishinan ya kuma sanar da hakan ne a zantawarsa da Aminiya jim kadan bayan kammala wani taro a kan inganta sashen lafiya da aka yi a jihar.
Aminiya: Wane matsayi ake a yanzu a kan batun gyaran kananan asibitocin shan magani a Jihar Kaduna?
A yanzu haka ana cigaba da yin gyaransu domin ko a yanzu mun zaga mun ga cewa akalla kusan saba’in cikin dari biyu da hamsin da biyar 255 da gwamnati za ta gyara an kai kashi kusan hamsin na aikinsu.
Kuma mai girma gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i da ya lura aikin ba ya tafiya kamar yadda ya kamata sai ya kafa kwamiti na musamman wanda shi shugaban ma’aikata na jihar ke shugabanta domin a tabbatar an kammala aikinsu cikin makonni shida.
Wannan kudiri da aka dauka na nuna cewa akwai niyya na musamman domin a kammala su saboda akwai abubuwa da ake jira. Kamar na’orori da gwamnatin jihar ta riga ta saya amma babu damar sanya su domin ba a kammala aiyukan ba an jibge su kurum shi ya sa ake kokarin kammala aikin.
Baya ga haka muna marmarin ganin cewa mutane sun fara cin muriyar wannan ayyuka da ake yi domin a kara habaka bangaren kiwon lafiya saboda mutane su kasance cikin koshin lafiya.
Aminiya: A yanzu haka likitoci na yajin aiki a Jihar Kaduna. Me za ka ce a kan haka?
Likitoci ne kawai ke yajin aiki ko su kansu ma wani bangare ne na likitocin ke yajin aiki da ake kira resident Doctors. A yanzu haka idan ka je asibitoci za ka ka ga wasu na aikin duba marasa lafiya.
Ko su kansu gaskiya dalilan da ya sa suka shiga yajin aiki ba masu karfi ba ne domin bukatun marasa lafiya na kan gaban duk abubuwan da suke so. Rashin hakuri ne da ko rashin ganewa ne ya sa suka dauki matakin. Domin kuwa mun zauna da su mun yi masu bayani amma ba su ji ba.
Amma muna rokonsu har ila yau da su ajiye wannan yajin aiki su dawo su cigaba da aikinsu. Kamar yadda kuka ji Gwamnan Jihar Kaduna na kokari kwarai da gaske domin a nan kasar da kasashen waje an san da ayyukansa.
Shi ya sa wata cibiya da ke kasar Birtaniya ta gayyace shi sati biyu da suka gudana da ya je ya yi masu bayanin irin gudunmuwa da yake bayarwa wajen inganta kiwon lafiya.
Da ba don kokari da hazakar da yake nunawa ba da ba za a kira shi ba. Shi ya sa muka nuna masu cewa su duba kokarin da yake yi a maimakon mu godewa gwamna abin da za mu saka masa ke nan.
Kowace ranar 22 ga wata ma’aikacin Kaduna yake samun albashi. Ka waiwaya wasu jihohi ka ga yadda ake wahala. Muna rokon jama’a da ’yan jarida da ku taimaka wajen yi masu magana su dawo.
Masu wahala iyayenmu ne mata da yaran mu mata da kannen mu mata da sauran yaran mu su ke wahala. Shi ya sa na fada masu cewa su yi tunani mai zurfi domin a matsayin mu na likitoci mun yi rantsuwa da cewa babu abin da da zai hana mu kula da mara lafiya a farkon abin da muke yi.
Mun fada masu wannan yajin aiki da kuma rantsuwa da suka yi sun batawa marasa lafiya da yakamata mu kare su rai. Shi ya sa nake kara rokonsu da su ji tausayin jama’a su dawo bakin aiki.
Aminiya: Ina aka tsaya a kan batun daukar sabbin likitoci da z ‘a tura su yi aiki a asibitocin gwamnati da ke fama da rashin likitoci?
An riga an dauka kuma tuni mun fara tura su asibitoci domin cigaba da ayyukansu ciki har da ma’aikatan jinya da likitoci da dai sauran ma’aikatan asibiti duk mun dauka. domin fara aiki a asibitocinmu.
Aminiya: Ina gaskiyar sabon tsarin gwamnatin jihar cewa za a fara bai wa dattawa da suka kai shekaru saba’in magunguna kyauta?
Gaskiya ne wannan za nce bayan mun kaddamar da wannan shiri mun horar da jami’in kiwon lafiya dari biyu da za su gudanar da wannan tsari. Kuma ina tabbatar maka da cewa magungunan da za a ba su masu kyau ne domin ba kowa zai iya zuwa kasuwa ya saya ko ya same su cikin sauki ba.
A yanzu bayan mun kammala horarwa za mu fara rajistar sunayensu. Da an yi wa mutum rajista zai samu sako a wayarsa cewa an yi masa rajista cewa ya tafi asibiti inda aka dauki sunansa domin a can zai rika zuwa karbar magani.
Aminiya: Ke nan akwai wasu likitoci da ke kula da marasa lafiya a yayin wannan yajin aiki??
Duk wani likita da ke matsayin matakin albashi na 14 zuwa sama suna aiki, shi ya sa idan ka je za ka ga gwargwado akwai ayyukan da ake yi.