Rashin hanya ke sa ’yan fashi na barna a yankin Birnin Magaji
Rashin hanya mai kyau na daga cikin abin da ke sa ’yan fashi da makami su rika barna ga jama’ar karamar Hukumar Birnin Magaji da ke Jihar Zamfara.Wakilinmu wanda ya ziyarci garin Birnin Magaji hedkwatar karamar hukumar Birnin Magaji a ranar Asabar da ta gabata, wani mazaunin garin, Alhaji Inusa Birnin Magaji ya shaida masa […]
Rashin hanya mai kyau na daga cikin abin da ke sa ’yan fashi da makami su rika barna ga jama’ar karamar Hukumar Birnin Magaji da ke Jihar Zamfara.
Wakilinmu wanda ya ziyarci garin Birnin Magaji hedkwatar karamar hukumar Birnin Magaji a ranar Asabar da ta gabata, wani mazaunin garin, Alhaji Inusa Birnin Magaji ya shaida masa cewa ba abin da ya kawo wannan sai siyasa.
Ya ce a cikin kananan hukumomin da ke jihar, ta Birnin Magaji ce kawai ba ta da hanya, duk da cewa lokacin gwamnatin Yarima an ba da aikin hanyarsu, wadda har zuwa yanzu ba ta wuce Nasarawan Godel ba.
daya daga cikin ’yan sintirin yankin Malam Bello Abubakar Mashayar Giwa ya ce saboda rashin kyan hanya, ’yan fashi suna cutar da su matuka, “An kashe mana ’yan banga da dama a bakan aiki, kuma ni kaina na rasa shanu 33 da tumaki 13,” inji shi.
Ya ce kusan duk hanyoyin da za a shiga Birnin Magaji barayi suna iya tare mutum saboda rashin kyansu, ya kawo misali da hanyar da ta tashi daga Birnin Magaji zuwa Dauran da wadda tashi daga kokiya zuwa Nasarawan Godel da ta Bulashe da ta Gusami Gora da sauransu.
Wata majiya a garin ta koka kan yadda ’yan sintiri suke kama barayi suna ba jami’an tsaro, amma sai su sake su, inda majiyar ta kawo misali da wani mai suna Bello dan canji da ’yan sintiri suka kama aka mika shi ga ’yan sanda amma yanzu ya dawo, sai wani mai suna Sani wanda ya yiwo gudun hijira daga Jihar Yobe, sun kama shi amma ’yan sanda sun sake shi.
Shugaban ’Yan banga na karamar Hukumar Birnin Magaji Malam Abu, ya ce a bana kawai an kashe masu ’yan banga da dama a garuruwan Yalla da kokiya da Makera da Gora da Nasarawan Godel da Mailayi da kuma Balitawa. Ya ce shi kansa sama da barayi 20 suka kira shi a waya suka ce sai sun kashe shi.
Shugaban ya ce duk da irin wannan hadarin da suke ciki bai hana su kama ’yan fashin su ba jami’an tsaro ba.
Wakilinmu ya ziyarci ofishin ’yan sanda na Birnin Magaji don jin ta bakinsu kan korafin jama’a na cewa ’yan sintiri sun kama ’yan fashi uku, sun mika musu amma sun saki wasu daga cikinsu, amma Babban Jami’in ’Yan sandan yankin (DPO), ya aiko DCO dinsa cewa ba zai samu ganinsu ba, yana cikin aiki sai dai su yi hakuri.