Rashin hawa ya sa bikin Sallah ya zama lami a Kano
Wannan ne karo na biyu da ba a yi hawan Sallah ba a Kano. Sai kuma lokacin annobar Kwarona.
Hawan Sallah biki ne da aka dade ana gudanar da shi a Kano tsawon shekaru wanda ke kara wa garin martaba, tare da janyo baki manyan baki daga ciki da wajen kasar nan da sauran mutane daban-daban.
Mutane da yawa kan je jihar don su yi tozali da kasaitaccen hawan wanda aka tabbatar babu wurin da ake gudanar da hawa kamar na Kano a fadin kasar nan.
Abin mamaki shi ne yadda sarakuna da masu rike da sarautun gargajiya ke tuttudowa garin don kallon hawan Daushen da ake yi washegarin Sallah.
Sai dai mazauna babban birnin jihar da sauran jama’ar da je zuwa kallon hawan ba su ji dadin yadda a Sallar bana hawan bai yiwu ba, a kokarin tabbatar da tsaro da hukumomi suka yi sakamakon dambarwar Sarautar Kano da ta kunno kai a tsakanin ’yan uwa biyu, Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II da kuma Sarki na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero inda kowane daga cikinsu ke da’awar cewa kujerar tasa ce.
Sarakunan biyu suna gudanar da zaman fadanci a fadoji biyu inda suka yi yunkurun gudanar da hawan.
Tunanin yiwuwar barkewar rikici a lokacin hawan ya sa Rundunar ’Yan sandan Jihar ta hana gudanar da hawan baki daya.
A ranar 23 ga Mayun 2024 ne, Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sa hannu a kan sabuwar Dokar Masarautu ta Shekarar 2024 wacce Majalisar Dokokin Jihar ta amince da ita, dokar da ta soke sarakuna 5 masu daraja ta daya da suka hada da Kano da Bichi da Rano da Karaye da Gaya da Bichi da kuma duk wasu nade-nade da aka yi kafin dokar.
Haka kuma Gwamnan ya sake dawo da tubabben Sarki na 14 Malam Muhammadu Sanusi II, sai dai an kalubalanci wannan yunkuri na gwamnati a kotu inda ake neman dawo da Aminu Ado Bayero a kan kujerarsa duba da cewa ba ya garin yayin da aka tube shi, kuma ba a tuhume shi da aikata laifi ba kafin a tube shi.
A shekarun da suka shude bikin Hawan Sallar yana nuni da kasaitar Kano da yadda al’adun mutanen yankin suke.
Yadda aka yi wa dawaki ado da kuma yadda mutane ke yin shiga iriiri baya ga nada rawunna a kawunansu.
Wannan ne karo na biyu da ba a yi hawan Sallah ba a Kano tun lokacin marigayi Sarki Ado Bayero lokacin da jihar ta yi fama da rikicin Boko Haram a shekarar 2012 zuwa 2014.
Sai kuma lokacin annobar Kwarona a shekarar 2020.
A ranar Sallar Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci Sallar Idi a Masallacin Kofar Mata, maimakon Filin Idi saboda ruwan sama da aka tashi da shi a ranar Sallar.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da rakiyar manyan jami’an gwamnati sun bi sahun dimbin al’ummar jihar inda suka sallaci raka’a biyu a masallacin.
Bayan kammala Sallar ce magoya baya da sauran jama’a ba su ji dadin ganin Sarkin kawai ba tare da mahaya dawaki da maroka da mawaka da dogarai da sauransu ba.
Bisa al’ada idan an kammala Sallar Idi, Sarki yakan zaga a kan dokinsa ta Unguwar Kofar Wambai da Zage da Satatima da Gidan Shettima inda yakan tsaya su gaisa da Gwamna da sauran manyan mutane kafin daga bisani ya koma fada ta Kofar Fatalwa inda yakan tsaya ya mika sakonsa ga al’umma.
Sai dai a wannan karo yayin da yake komawa fada, Sarkin shi kadai a dokinsa ya yi wa al’umma wa’azi inda ya nemi su zauna lafiya da juriya.
Ya kuma nemi su ci gaba da yin addu’ar neman sauki game da halin kuncin rayuwa da al’umma ke ciki.
Shi ma a nasa bangaren Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi Sallar Idi a karamar fadarsa da ke Nasarawa.
Shi ma kamar Sarki Sanusi bayan da aka kammala Sallar ya koma fadarsa a kan farin dokinsa ba tare da rakiyar sauran mahaya dawaki kamar yadda aka saba ba.
Abin da ba a yi ba shi ne yawon zaga gari da masu rike da sarautu tare da dimbin mabiyansu, lamarin da bai yi wa jama’ar gari dadi ba.
Ita ma Gwamnatin Jihar Kano ba ta ji dadin yadda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya bayar da sanarwar hana Hawan Sallar ba, ba tare da tuntubar Gwamnan wanda shi ne shugaban tsaro na jihar ba.
Kwamishinan Shari’a na Jihar Alhaji Haruna Isa Dederi ya shaida wa manema labarai cewa Kwamishinan ’Yan sandan ba ya yin biyayya ga umarnin da Gwamnan yake bayarwa.
“Wasu mutane suna bijire wa umarnin shugabannin tsaro inda ta kai har Kwamishinan ’Yan sanda zai bayar da umarnin hana Hawan Sallah a jihar nan ba tare da tuntubar shugaban tsaro na jihar ba, inda yake fakewa da cewa yana karbar umarni daga sama,” in ji Kwamishinan.
A cikin wata sanarwa da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta fitar dauke da sa hannun Kakakinta SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta nemi al’ummar jihar su yi biyayya ga dokar kasancewar an yi ta ce da nufin kare lafiyar al’ummar jihar.
Takardar sanarwar ta ci gaba da cewa “Bisa hadin gwiwar jami’an tsaro daban-daban an yi haka ne domin kiyaye lafiyar al’ummar jihar ba wai tunanin yin wani bukukuwa don nishadi ba.
Don haka muna neman masu bin doka da oda da su ci gaba da ba jamian tsaro hadin kai.
Domin shirye shirye sun kammala wajen gudanar da bukukuwan Sallah lafiya ba tare da yin wasu bukukuwa da aka saba ba.”
Wannan sanarwar ce ta janyo aka gudanar da Sallar ba tare da yin shagulgulan da aka saba yi na Hawan sallah wadanda suke nishadantarwa tare da hada kan mutane a kan tarihinsu da suka gada kaka da kakanni.
Wani dan jarida da ke aiki a wani gidan rediyo mai zaman kansa wanda a lokuta da dama yake yin sharhi a kan bikin Hawan Sallar, mai suna Ado Sa’idu Warawa ya ce abin bakin ciki ne a ce a gudanar da Sallar ba tare da hawa ba.
“Abin bakin ciki ne a ce ba a yi Hawan Sallah a Kano ba a wannan lokaci saboda rikicin masarauta.
“Duk da cewa mun ga irin hakan a baya inda ba a yi hawan ba saboda rikicin Boko Haram da kuma annobar cutar Kwarona.
“Sai ga shi kuma a yau hawan ya gagara saboda rigimar sarauta,” in ji shi.
Ado Warawa ya yi fatar cewa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kano za su dauki matakin da ya dace don warware matsalar a kan lokaci.
Wani mazaunin jihar, Adamu Aminu Fagge ya nuna damuwarsa a kan hakan.
Ya bayyana cewa Sallar bana ba ta yi dadi ba sakamakon rikicin masarautar.
A cewar Fagge duk da cewa maganar na gaban kotu wanda ba a bukatar wani ya tofa albarkacin bakinsa har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukuncin karshe, amma dai Sallah ba ta yi dadi ba kamar yadda aka saba a shekarun baya.
Ya kara da cewa Sallah ba tare da hawa ba kamar miya ce babu gishiri da kayan kanshi.
“Idan ka Kalli fuskar mutanen Kano za ka gane cewa suna cikin alhini na rashin yin Hawan Sallar,” in ji shi.
A cewarsa duk da matsin tattalin arziki da ya sa mutane suka bazama neman abin da za su ci, Jihar Kano tana zaune lafiya sai dai rashin yin hawan ya sa su cikin damuwa.
A cewar wani mai daukar hoto, Nasiru Adamu Sarki Darki abin ya shafe shi kaitsaye saboda bai samu damar daukar hoto yadda ya kamata ba, saboda yakan dauki mahaya dawaki da sauran mutane daban-daban.
A bangaren ’yan sandan jihar sun bayyana gamsuwarsu kan yadda jama’ar gari suka gudanar da Sallar Idi lafiya a kananan hukumomin jihar 44.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Alhaji Usaini Gumel ya ce ya ji dadi kan kwantar da hankali da zaman lafiyar da mazauna Kano suka nuna, inda ya yi fatar za su ci gaba da nuna haka a lokacin bukukuwan Sallar.
Gumel ya kare tarihin aikinsa a jihar, inda ya ce jama’a za su yaba masa kan matakin da ya dauka game da rikicin sarautar Kano.
Kamar yadda aka saba bayan an yi Hawan Sallah idan gari ya waye akan gudanar da Hawan Daushe.
Sannan washegari a fita Hawan Nasarawa inda Sarki ke kai gaisuwa da jami’an gwamnati a karkare Hawan Sallar da Hawan Dorayi.