Rashin hukunta bokaye ya sa ake ta satar sassan jikin dan Adam -Sheikh Zakariya
Wani malamin addinin Musulunci da ke Abuja Sheikh Hussaini Zakariya Yawale ya ta’allaka matsalar sace mutane ana cire sassan jikinsu a kasar nan a kan rashin zantar da hukuncin Allah a kan bokaye da wadanda ke yi musu hidima. Sheikh Hussaini Zakariya wanda ke tsokaci a kan abin alhinin da ya auku da wani yaro […]
Wani malamin addinin Musulunci da ke Abuja Sheikh Hussaini Zakariya Yawale ya ta’allaka matsalar sace mutane ana cire sassan jikinsu a kasar nan a kan rashin zantar da hukuncin Allah a kan bokaye da wadanda ke yi musu hidima.
Sheikh Hussaini Zakariya wanda ke tsokaci a kan abin alhinin da ya auku da wani yaro da wasu matsafa suka kwakule wa ido a garin Zariya a kwanakin baya, ya ce matukar gwamnati na da sha’awar kawo karshen matsalar cire sassan jikin dan Adam da matsafan ke yi, dole ne ta dauki hukunci mai tsauri a kan bokaye da masu yi musu hidima wadanda ya ce addinin Musulunci ya kyamaci aikinsu.
Ya ce a shari’ance aikata bokanci ko zuwa wajen mai yin sa da nufin neman taimako na raba mutum da addini nan take, kuma hukuncin mai akata shi, shi ne kisa. “Haka masu yi musu hidima wajen cire sassan jikin mutum, aiwatar da haddi a kansu ya kamata a yi ta hanyar cire idon wanda ya cire na wani, ko kuma yanke harshen wanda ya yanke na wani,” inji Malamin.
Ya ce Sheikh Usmanu danfodiyo ya sha fama da bokaye a lokacin da yake da’awar jaddada addini a kasar nan, a yayin da dansa Muhammadu Bello bin Fodiyo, wanda a lokacinsa ne aka fara aiwatar da shari’a, bokaye suka rika buya.
Da Aminiya ta tambayi ra’ayinsa a kan yana da wuya hukuma ta iya daukar hukunci mai tsauri a kan bokaye saboda akwai zargin ma’abota mulki da dama na tare da su, sai malamin ya ce idan haka ta kasance lallai ya zama wajibi al’umma su sake tunani tun a lokacin zaben shugabanninsu don gudun zaben bara-gurbi wadanda mulkinsu ka iya kawo bala’i ga kasa.