Rashin jari ne matsalata -Yakubu Usaini

Wani mai kera fitilar gargajiya da ake kira a-ci-balbal mai suna Yakubu Usaini da ke zaune a Legas ya ce rashin jari ne babbar matsalar da ke ci masa tuwo a kwarya.Yakubu Usaini, mai kimanin shekara 46, ya shaida wa Aminiya, a wata tattaunawa, cewa da yana da isasshen jari da ya bunkasa sana’ar. “Rashin […]

Rashin jari ne matsalata -Yakubu Usaini

Yakubu Usaini yayin da yake kera fitilaWani mai kera fitilar gargajiya da ake kira a-ci-balbal mai suna Yakubu Usaini da ke zaune a Legas ya ce rashin jari ne babbar matsalar da ke ci masa tuwo a kwarya.
Yakubu Usaini, mai kimanin shekara 46, ya shaida wa Aminiya, a wata tattaunawa, cewa da yana da isasshen jari da ya bunkasa sana’ar. “Rashin isassun kudi na damuna. Da a ce ina da jari da na fadada sana’ar nan ta hanyar bude katafaren shago ko kamfanin da zan rika kera fitilu daban-daban na gargajiya da na zamani.  Allah Ya yi mini hikima da fasaha, ta yadda ina iya kera kowace irin fitilar gargajiya”. Inji shi.Samfurin fitilun da Yakubu Usaini ya kera (a kebe) da kuma komatsan da akan yi amfani da su wajen harhada fitilun ne. Hotuna: Abubakar HarunaYa ci gaba da cewa duk da matsalolin da yake fuskanta ya sami nasarori da yawa a sana’ar, wadda da ita ya yi aure, ya haifi yara, “Kuma ina daukar dawainiyar iyalina ba tare da wata matsala ba. Na koya wa wasu da dama, wasu suna zaman kansu, wasu kuwa ina tare da su a shagona. Wannan ba karamin ci gaba ba ne, sai dai na yi wa Allah godiya”.
Ya ce ya shafe fiye shekaru 20 kan sana’ar, wadda ya koya don sha’awar da yake da ita ta neman halaliyarsa, tare da ba da horo ga yara da manya masu yawa. “Da sana’ar fanabita nake yi, sai babu aiki, sai na koyi wannan sana’ar wajen wani dan asalin kasar Ghana, don rufa wa kaina asiri. Wasa-wasa sai na rika samun bunkasa, har Allah Ya kawo ni wannan lokaci. Na gode wa Allah, ga shi har yanzu ina cin abinci da ita”.
Ya ce yakan yi amfani da gwangwanaye  da guduma da kusa da dalma da kuma karfen bugu wajen kera fitilar.
“Sana’ar tana da rufin asiri kuma tana da alfanu mai yawa ta yadda mutum, in dai ba mai zalama ba ne, zai sami abin da zai ciyar da iyalansa. Saboda alfanun da muke samu, ya sa akwai samari da yawa da ke bukatar in koya musu wannan sana’a. Ita sana’a, idan ba yin ta kake yi ba, to ba za ka san abin da ake samu ba. Ka ga wannan karamar fitilar tana kaiwa Naira 200, babbar kuwa tana kaiwa kimanin Naira 400. Ban da fitilu, har ‘banki’ na ajiyar kudi muna yi. Shi ma ‘bankin’ akwai babba, akwai karami. A kullum ina samun kamar Naira dubu biyu.
“A karshe ina kira ga matasa da kada su rika raina sana’a, domin ita sana’a, hanya ce da dan Adam zai rufa wa kansa asiri da kare mutuncinsa”. Inji shi.