Rashin kamfanoni ya haifar wa Arewa maso Gabas matsancin talauci – Abdullahi Isa
An bayyana rashin kamfanoni a shiyar Arewa maso Gabas a matsayin silar talaucin da ya addabi yankin domin duk shiyyoyi shida na kasar nan suna da kanfanonin sarrafa karafa ban da Arewa maso Gabas. Abdullahi Isa, Shugaban Kungiyar ’Yan Bola-Jari na Jihar Gombe ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe. […]
An bayyana rashin kamfanoni a shiyar Arewa maso Gabas a matsayin silar talaucin da ya addabi yankin domin duk shiyyoyi shida na kasar nan suna da kanfanonin sarrafa karafa ban da Arewa maso Gabas.
Abdullahi Isa, Shugaban Kungiyar ’Yan Bola-Jari na Jihar Gombe ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe.
Abdullahi Isa ya ce da za a samar da kamfani koda daya ne a yankin da zai rika sarrafa karafa da za a rage talauci a tsakanin al’umma domin duk ranar duniya ana tayar da motoci fiye da goma na tsofaffin karafa zuwa sauran shiyyoyin kasar.
Ya ce, ya fara wannan harkar ce tun bai da jari lokacin da yake bi kan bola yana tsintar karafa yana kaiwa ya sayar har ta kai yanzu yana iya tayar da mota uku zuwa biyar duk wata.
Shugaban ya ce ya fara harkar bola-jari ce tun 1984, sannan duk wani rufin asiri da mai nema ko dan kasuwa yake da shi shi ma daidai gwargwado ya mallaka don ya je Hajji, ya gina gida yana kuma tafiyar da harkokin gidansa duk da wannan harka.
Ya kara da cewa da gwamnati za ta samar da kamfanoni a yankin, hakan zai rage ta’addanci domin ko a Kudancin kasar nan abin da ya kawo karshen matsalolin rashin tsaro ke nan.
Abdullahi Isa ya ce suna taimaka wa gwamnati wajen rage mata dawainiyar matasa marasa aikin yi, inda ya ce ko shi yana da yara a kusan dukan kananan hukumonin Jihar Gombe 11.
Ya ce yana da yaran da ya ware a Jihar Taraba da suka kama kasa, don ko tafiya zai yi daga gidansa har zuwa jihar da zai je bai samu matsalar da ta fi karfin shawo kanta saboda duk garin da ya je yaran suke daukar dawainiyarsa hatta otel da zai kwana.