Rashin kammala hanyar Kano zuwa Maiduguri na janyo asarar rayuka shekara 17 da farawa

Tun daga shekarar 2006 aikin ya samu tsaiko saboda wasu dalilai.

Rashin kammala hanyar Kano zuwa Maiduguri na janyo asarar rayuka shekara 17 da farawa

Tun shekara 17 da suka gabata wato a shekarar 2006 Gwamnatin Tarayya ta bayar da kwangilar sake aikin gina hanyar Kano zuwa Maiduguri, sai dai a wancan lokacin aikin ya samu tsaiko saboda wasu dalilai.

Bayan da tsohuwar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kama mulki sai ta sake waiwayar aiki tare da bayar da kwangilar gudanar da shi ga wasu kamfanoni a shekarar 2018.

An kasa aikin hanyar zuwa gida biyar a jihohin da aikin hanyar ya shafa.

A kaso na farko akwai daga Kano zuwa Wudi zuwa Shuwarin.

Sai kaso na biyu daga Shuwarin zuwa Azare, sai Kaso na uku daga Azare zuwa Potiskum sai kaso na hudu da na biyar daga Potiskum zuwa Maiduguri.

Sai dai za a iya cewa duk da tsawon shekarun da aka dauka ba ana aikin zuwa yanzu kaso 80 cikin 100 ne na aikin aka kamamla a kaso na biyu da na uku da na hudu.

Sai kaso na farko wato daga Kano zuwa Wudil zuwa Shuwarin da kuma na biyar da zai shiga cikin Maiduguri ne wadanda aikin su ya rage da wasu ’yan kilomitoci.

A bangaren kaso na karshe wanda ya shafi Jihar Borno za a iya cewa aikin kadan ya rage domin an kammala kaso 80 na aikin.

Amma da Aminiya ta dawo baya wato kaso na daya wanda ya tashi daga Kano ya wuce Wudi da Gaya zuwa Shuwarin ta gano cewa akwai sauran rina a kaba, domin akwai sauran kusan kilomita 49 da ba a kammala ba.

Wasu sassa na lalataccen titin Kano zuwa Maiduguri

Binciken Aminiya ya gano cewa an dauki tsawon wata 15 ba tare da Kamfanin Dantata and Sawoe wanda ke gudanar da aikin ya ci gaba da gudanar da aikin ba.

Har ila yau Aminiya ta lura cewa rashin kammala wannan hanya ya janyo hanyar ta zama kadarkon mutuwa duba da irin rayuka da dukiyoyi da ake rasawa a koyaushe.

A ziyarar da Aminiya ta kai a kan hanyar ta ga cewa an fara gudanar da aikin tun daga kan iyakar sabuwar gadar sama ta Muhamamdu Buhari da ke Wudil inda aka yi aikin a hannu biyu kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar aikin.

Sai dai kuma daga garin Wudil har zuwa Gaya an ci gaba da gudanar da aikin bangaren daya inda aka yi watsi da daya bangaren lamarin da ya tilasata wa masu bin hanyar yin amfani da titi guda daya.

Hanya ce mai hatsari —Direbobi

Har ila yau Aminiya ta lura da irin yadda direbobi suke shan matukar wahala wajen yin tuki a kan titin sakamakon kauce wa ramuka da suke yi da kuma bin hannu daya a wasu wuraren.

Wani direba mai suna Abdulkarim Mahmud Kofar Mata ya bayyana cewa irin hatsarin da wannan hanyar ke jefa rayuwar al’umma abin ba ya misaltuwa.

“Gaskiya irin hatsarin da ke faruwa a wannan hanya sai dai mu ce ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!

“Domin Allah kadai ne Ya san yawan rayukan da ake rasawa a kullum.

“Idan fa direba ya biyo hanyar nan sai dai kawai ya yi addu’a domin neman sauka lafiya.

“Hanya ce mai hatsarin gaske duba da hannu daya ake amfani da ita sannan ita din ma duk ramuka sun cinye ta.

“Idan har direba ya taho a hannun da kake tafiya to sai dai aka yi hakuri ka daga kafa domin daya motar musamman ma idan babbar mota ce ta wuce sannan kai daga baya sai ka wuce.

“Idan kuwa ba ka yi haka ba, to, komai zai iya faruwa,” in ji shi.

Shi ma wani direban Musa Ahmad ya koka kan yadda titin ya zama matsala ga al’umma domin kuwa a cewarsa ya zama shiga da alwalarka.

Ya ce, “Kin ga manyan motocin nan sun zama abin tsoro ga kananan motoci masu bin hanyar.

“Kasancewar hannu daya ake bi. Idan ka taho sai dai ka rabe a gefe.

“Ga shi kuma abin takaicin gefen titin da akan yi domin a tsara sun rufe shi sai ki ga direba ya rasa yadda zai yi.

“To a nan ne fa za ki ga hatsari na faruwa musamman idan direban karamar mota shi ma a guje yake, to shi ke nan ko dai ya fada rami ko ya yi taho-mu gama da babbar mota.”

Ban da wannan kuma lamarin ya jawo koma-baya ta fuskar tattalin arziki ga mutanen yankunan duba da cewa mutane na jin tsoron bin hanyar.

Muna so gwamnati ta kawo mana dauki — Mazauna

Al’ummar yankin da masu bin hanyar sun nemi gwamnati ta kai musu dauki domin ceto rayukan dimbin mutanen da suke bin hanyar dare da rana.

A baya-bayan nan ma Majalisar Wakilai ta ce da zarar ta kafa kwamiti mai kula da ayyuka za ta damka masa alhakin bincikar abin da ya janyo rashin kammala aikin hanyar.

Wannan na zuwa ne bayan da dan majalisar Alhaji Yusuf Shitu Galambi ya gabatar wa majalisar kudiri a kan hakan.

Yayin da aikin ya kammala a wasu jihohi uku da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi bikin bude su, sauran wuraren da ba a kammala ba ana gabar kammala su nan ba da dadewa ba.

Aminiya ta tuntubi Manajan Kula da Aikin Hanyar a Kamfanin Dantata and Sawoe Mista Roy Hungushi ya ce ba ya da ikon yin magana a kan wannan batu don haka ya nemi Aminiya ta tuntubi shugabannin kamfanin da ke Abuja.

Injiniya Nasiru Dantata shi ne Babban Daraktan Kamfanin Dantata and Sawoe ya ki cewa komai a kan batun lokacin da Aminiya ta tuntube shi, domin bai amsa kiraye-kirayen da aka yi masa ta wayarsa ta hannu ba haka kuma bai bayar da amsar sakonnin da ta tura masa ta wayar ba.

A yanzu da Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan Ayyuka ta bayar da wa’adin mako biyu cewa kowane dan kwangila da ya yi watsi da aikin da yake gudanarwa ya koma bakin aikinsa idan kuma ba haka ba zai fuskanci kwace kwangilar daga hannunsa.

Abin jira a gani shi ne ko kamfanonin za su ji wannan barazana tare da komawa bakin aiki ko a’a.