Rashin kara aure ke jawo karuwanci
Fitaccen dan kasuwa, wanda ya yi fice wajen kara aure, wanda yafito daga yankin Kudu maso Kudu, Ned Nwoko ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.
An bayyana cewa zama da mace daya da mazan Kudancin kasar nan ke yi na ci gaba da haifar wa ’yan matan yankin yin gararamba, suna bin maza domin su samu abin da za su sanya wa bakinsu.
Fitaccen dan kasuwa, wanda ya yi fice wajen kara aure, wanda yafito daga yankin Kudu maso Kudu, Ned Nwoko ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema lanarai.
- IPOB: Yajin aikin ’yan Arewa ya kawo tsadar abinci a Kudu
- Badakalar N10bn: Kotu ta tura dan uwan Gwamnan Kogi kurkuku
Nwoko ya ci gaba da cewa, “idan maza a Kudancin kasar nan za su rika auren mata hudu da yaranmu ba za su rika yin yawon karuwanci ba suna neman abin da za su sanya wa bakinsu.”
Ned Nwoko, wanda tsohon dan majalisa ne ya yi mamakin irin yadda ’yan Kudu suka rike akidar auren mace daya su zauna da ita.
“Kara aure ba wata matsala ba ce. Hakan zai kawo karuwar iyali da rage yawon fasikanci da ’yan matan Kudu ke yi.”
Ya kuma bayyana matukar damuwa da irin yadda ’yan mata a Kudu suke rayuwarsu, inda ya ce “abin na ba ni tsoro da takaici.”
A kan haka ya doka misali da ’yan Arewa, inda ya ce, “a Arewa mafi karanci, mutum a ce matarsa daya. Daga mai biyu sai uku da hudu. Abin da ba mu da shi a Kudu ke nan.”