Rashin karatu ne babbar matsalar ’yan fim-Abdulaziz M Sharif

Abdulaziz Muhammad Sharif fitaccen jarumin fina-fanan Hausa ne. A hirar da ya yi da Aminiya a kwanakin baya, ya bayyana yadda ya fara harkar fim da nasarorin da ya samu da kuma wasu daga cikin kalubalen da ya fuskanta: Tarihina a takaiceAssalamu alaikum, sunana Abdulaziz Muhammad Sharif, an haife ni a garin Rigasa da ke […]

Rashin karatu ne babbar matsalar ’yan fim-Abdulaziz M Sharif
Rashin karatu ne babbar matsalar ’yan fim-Abdulaziz M Sharif

Abdulaziz Muhammad Sharif fitaccen jarumin fina-fanan Hausa ne. A hirar da ya yi da Aminiya a kwanakin baya, ya bayyana yadda ya fara harkar fim da nasarorin da ya samu da kuma wasu daga cikin kalubalen da ya fuskanta:

Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Abdulaziz Muhammad Sharif, an haife ni a garin Rigasa da ke Jihar Kaduna. Na yi makarantar firamare da sakandare a Rigasa, daga nan na fara harkokin fina-finan Hausa.
Dalilin da ya sa na shiga harkar fim
A gaskiya sha’awa ce, saboda tun ina karami nake kaunar fina-finan Indiya da kuma namu na Hausa. Wannan ne ya sa bayan na kammala karatun sakandare, ba wata sana’a da ta bijiro raina sai sana’ar fim.
kalubale
Da farko ni da kani na wato mawaki Umar M Sharif mun fuskanci kalubale daga wurin iyayenmu, daga bisani suka fahimci dabi’unmu ba su canza ba, sai cikin yardar Allah suka ba mu dukkan goyon bayan da ya dace.
Fina-finan da na yi
Sun hada da: ‘Ba Zan Bar Ki Ba’ da ‘Makashinka’ da ‘Me Ye Mafita?’ da ‘Ka So A So Ka’ da ‘Jinin Jikina’ da dai sauransu. Akalla za su kai dari.
kalubale a harkar fim
Rashin karatu tsakanin masu sana’ar ne babban kalubalen da ke ci wa sana’ar tuwo a kwarya. Kuma idan na ce maka karatu ba kawai ina maganar karatun boko ba ne. Ina nufin ilimin boko da na addini. Saboda idan da kowane mutum da ke cikin sana’ar yana da wadataccen ilimi, to da tuni an magance dukkan matsalolin,  ciki har da matsalar satar fasaha, saboda wanda ke da ilimi kuma yake amfani da shi ba zai zama mai satar basirar wani ba. Idan da za su gane, da saka dukiyoyinsu suka yi zuwa halattaciyyar hanya, wannan ne zai sa kowa ya amfana.
Kirana ga abokan sana’ata
Ya dace mu hada kai don mu kasance  tsintsiya madaurinki daya. Saboda ta haka ne kawai za mu iya magana da murya daya.
Nasarori
A gaskiya daga fara sana’ar zuwa yau, na samu ci gaba sosai. Misali na samu damar mu’amala da mutane daban-daban duk albarkacin wannan sana’ar.
Burina
Ina da burin Allah Ya kara daukaka ni a harkar. Ina da kuma burin koma wa makaranta.
Iyali
Ina da mata daya, da kuma da daya.