Rashin kauna ya sa na kashe mijina – Rahama

Amaryar nan da ta kashe mijinta bayan kwana uku da aurensu Raham Husain da ke hannun ’yan sandan Kano ta ce ta yi aika-aikar ce saboda ba ta kaunar mijin. Sai dai ta shaida wa Aminya cewa ta daba masa wukar ce don hana shi saduwa da ita, amma da don ta kashe shi ba. […]

Rashin kauna ya sa na kashe mijina – Rahama
Rashin kauna ya sa na kashe mijina – Rahama

Amaryar nan da ta kashe mijinta bayan kwana uku da aurensu Raham Husain da ke hannun ’yan sandan Kano ta ce ta yi aika-aikar ce saboda ba ta kaunar mijin. Sai dai ta shaida wa Aminya cewa ta daba masa wukar ce don hana shi saduwa da ita, amma da don ta kashe shi ba.

A makon jiya ne muka kawo muku labarin amarya Rahma Hussain da ta kashe angonta Tijjani bisa dalilin auren dole da aka yi mata da marigayin wanda malamin makarantar allo ne a Unguwar Darmanawa.
Rahama ta ce duk da akwai danganataka ta jini tsakaninsu da angon nata ba ta kaunarsa. “A gaskiya tun farko ba na son sa, duk kuwa da cewa kakaninmu daya. Kuma shi kansa ya san ba shi nake so na aura ba, haka su ma iyayena sun sani, amma suka aurar da ni gare shi,” inji ta.
Sai dai wani makwabcin angon kuma abokin malaminsa mai suna Alaramma Sani ya ce, ba auren dole aka yi tsakanin angon da amaryarsa ba.
Alaramma Sani, ya ce yana daga cikin mutanen da suka wuce gaba wajen nema wa Tijjani auren Rahama. “Kasancewata ta aminin malaminsa da ni aka yi komai na neman auren. Kuma a iya saninmu babu wata kiyayya a tsakaninsa da amaryar, domin babu wani abu na aure da amaryar ba ta nema da kanta a wurinsa ba. Duk shirye-shiryen bikin tare suka yi kayansu har ankon biki a wurinsa ta nemi kudi ya biya, kuma ana saura kwana uku auren ya je zance wurinta. Kin ga da a ce akwai matsala da mun sani. Ni dai a fahimtata akwai wani abu na cin amana a ciki kawai,” inji shi.
Malam Sani ya ce “Misalin karfe 9:30 na safe muna makaranta sai wani ya zo ya gaya min cewa matar Tijjani ta caka masa wuka. Jin haka ya sa na yi saurin zuwa gidan don sanin abin yi. Ina isa kofar gidan na same shi ya fito waje rike da cikinsa, daga nan sai na yi sauri na samo A Daidata Sahu na sa shi tare a ciki don kai shi asibiti inda muka bi ta ofishin ’yan sanda aka ba mu ’yan sanda biyu don su raka mu Asibitin Malam Aminu Kano. Kuma bayan likitoci sun duba shi ne suka tabbatar da rasuwarsa sakamakon caka masa wuka da ta yi a wuri biyu a cikinsa,” inji shi.
Alaramma Sani ya ce, “Bayan aika-aikar ta fito daga gidan tana neman guduwa, sai ya sa wani saurayi dan unguwar da ya ga lokacin da ta yi bayan layi a guje ya bi ta. Ganin haka sai ta shiga wani gida tana ihun cewa wai kwarto ne ya biyo ta. Nan ya yi wa jama’ar da ke kofar gidan bayanin halin da ake ciki mutanen suka kama ta suka dawo da ita gidanta.”
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya shaida wa Aminiya cewa tunda wacce ake zargin ta amsa laifinta, abin da ya rage musu shi ne su gurafanar da ita gaban kotu don yi mata hukunci.