Rashin kishi ne yake ruguza kungiyoyin ’yan Arewa – danladi Zage
Shugaban kungiyar Zamzamiyya na Jihar Legas, Alhaji danladi dahiru Zage, ya ce halin-ko-in- kula da ’yan Arewa suke nunawa shi ne ulmul’aba’isin da yake sanyawa kungiyayoyin da ’yan Arewa suka kafa suke rushewa. Alhaji danladi Zage wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Jihar Legas, ya dage a kan cewa sai […]
Shugaban kungiyar Zamzamiyya na Jihar Legas, Alhaji danladi dahiru Zage, ya ce halin-ko-in- kula da ’yan Arewa suke nunawa shi ne ulmul’aba’isin da yake sanyawa kungiyayoyin da ’yan Arewa suka kafa suke rushewa.
Alhaji danladi Zage wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Jihar Legas, ya dage a kan cewa sai ’yan Arewa sun canja halayensu sannan kungiyoyinsu za su samu ci gaba.
“Babu shakka idan Hausawa ba su daina nuna rashin kishi ga kungiyoyin da suke ciki ba to kuwa kungiyoyinsu ba za su dore ba. Kuma za su rika samun koma baya. Sai ka ga an kafa kungiya amma sai ka ga mutane ba su dauke ta da wani muhimmanci ba. Za ka ga jama’a ba sa son zuwa taro kuma ba sa son biyan kudin kungiya, sai ka ga shugaban kungiyar da sauran jagorori ne za su rika yin dawainiya da kungiyar da kudinsu,”inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Kamar kungiyarmu ta Zamzamiyya da yake mu ayyukanmu sun fi karfi ga addini kamar gyaran masallatai da taimakawa jama’a da gyaren makabartu da ciyar da mutane lokacin azumi da tallafa wa wadanda za su yi aure da masu radin suna da sauran tallafin abubuwa rayuwa daban-daban, za ka ga sau da yawa idan muka kira taro jama’a ba sa son zuwa, sai mun yi da gaske sannan wani lokaci za ka ga an dan taru. Wannan abu yana dakusar da gwiwowin shugabanni. Haka shi yake janyo wa ka ga ayyukan kungiya yanayin tafiyar hawainiya. Kuma mutanenmu Hausawa su suka fi yin wasa da kungiya ba kamar sauran kabilu ba. Da za ka ga suna yin taro a kai- a kai.”
“Ina kira ga mutanenmu da sauran ’yan Arewa baki daya a duk lokacin da aka kafa kungiya su dauke ta da muhimmanci. kungiya aba ce mai alfanu da hatta gwamnati ta na alfahari da kungiyoyi. Kuma ina kira ga mutanenmu su yi koyi da wasu kabilun kudu yadda suke tafiyar da harkar kungiyoyinsu ba tare da yin sakwa-sakwa ba,”inji shi.
Ya bayyana cewa babbar nasarar da kungiyarsu ta samu daga watan Janairu zuwa yau shi ne hadin kai.
Ya ce: “Mun gyara masallatai da yawa da makabartu da yawa. Hakazalika, mun yi shirye-shirye don gudanar da ciyarwa a lokacin azumi sannan kuma akwai masallatai da muka saya musu tabarmin salla da kuma tufatar da talakawa ba tare da nuna bambanci ba.”