Rashin kudi na hana mata fitowa takara – Amina BB. Faruk

Aminiya ta zanta da Barista Amina B. B. Faruk da ta fito takarar Majalisar Wakilai a Mazabar Gezawa da Gabasawa a Jihar Kano, inda ta bayyana cewa rashin samun tallafin kudi yana hana mata fitowa takara: Za mu so sanin tarihinki a siyasance. Sunana Amina Ummulkhair Ibrahim B.B Faruk. Shekarata hamsin da ’yan kai. ’Ya’yana […]

Rashin kudi na hana mata fitowa takara – Amina BB. Faruk

Amina BB. Faruk

Aminiya ta zanta da Barista Amina B. B. Faruk da ta fito takarar Majalisar Wakilai a Mazabar Gezawa da Gabasawa a Jihar Kano, inda ta bayyana cewa rashin samun tallafin kudi yana hana mata fitowa takara:

Za mu so sanin tarihinki a siyasance.

Sunana Amina Ummulkhair Ibrahim B.B Faruk. Shekarata hamsin da ’yan kai. ’Ya’yana hudu de jikoki.  A siyasa kuwa zan iya cewa idan ana gadon ta to ni gadar ta na yi, domin a cikinta aka haife mu. Iyayemu sun yi aikin gwamnati, daga baya kuma suka shiga siyasa. Kin san siyasa, harka ce ta mutane, idan kana cikinta to dole ne ka duba halin da mutanenka suke ciki, ta ina za ka gyara musu da sauransu. Wannan shi ne abin da muka taso, muka ga iyayenmu suna yi wanda mu ma shi muke so mu yi wa al’ummarmu.

Me ya ja hankalinki  kika fito takarar kujerar majalisar wakilai?

Duk da cewa ina cikin Jam’iyyar PDP tun tuni, domin zan iya cewa mahaifina shi ya kai Jam’iyyar PDP garin Gezawa sai dai ban taba tsayawa takarar wani mukami ba.  Ina zaune mutanen Gezawa suka kirani suka ce suna nema na yi musu gagoranci, na wakilce su a Majilisar Wakilai. Idan mutum yana majalisa, akwai wani abin da ake kira constituency project. Shi wannan constituency project yana nufin ka je wurin mutane ka tambayesu abin da suke bukata a yi musu wanda rayuwar su za ta inganta da shi, abubuwa kamar makarantu da asibitoci da kwararrun malaman koyarwa da na asibiti da hanyoyi da tsaftataccen ruwan sha dasauran su. Na yi aiki a hukumar da ke kula da ’yan gudun hijira na ga yadda constitieuncy projects ya taimaka wa ’yan gudun hijira (IDPS) a Maiduguri. Idan Allah Ya ba ni wannan kujera zan yi iya kokarina wajen ganin al’ummata ta samu ci gaba ta hanyar wakilcin da za mu yi.

To idan na fahimce ki, kina nufin ba wani aikin a zo-a-gani da aka yi a mazabar Gezawa da Gabasawa ke nan?

Ni dai ban gani ba kuma ba a nuna min ba, amma an taba nunamin wasu dakuna guda biyu wanda aka ce wai ajujuwa ne wanda aka yi musu, kuma  raina ya baci da aka nuna min wai aiki cigaban da aka yi musu ke nan. Don har yau babu wani abIn a zo-a-gani da aka yi a shekara takwas din da dan majalisar da ke kan kujerar ke yi. Kin san tunda kika ga mutane sun taso sun nemi mace ta wakilce su kin san akwai matsala.

Wadanne matsaloli za ki fara tunkara idan kika samu wannan kujera?

Ai wannan matsololin ba a Gezawa da Gabasawa kadai ya shafa ba. Ina kallon matsalolin gaba daya ne a wani abin da Bature ke kira ‘HOLISTICALLY’. Kin ga idan kika dauki harkar mata wacce harka ce da ta shafi rayuwan al’umma gaba daya. Wannan ya kunshi gina musu asibitoci da ba su magani kyauta da ingata rayuwar ’ya’yansu da ba su jari da koya musu sana’o’i.  Sai kula da harkar matasa musamman a kan sama mususana’o’i da za su dogara da kansu wanda hakan zai magance fadawarsu cikin wasu halaye marasa kyau musamman harkar shaye-shayen muggan kwayoyi. Bayan wannan, wakilcin da muke so mu yi wa mata a majalaisa yana da muhimmaci kwarai da gaske musamman mu matan Hausawa. Idan kin duba akwai matsalar rashin shigar mata Hausawa siyasa don kafin ki ga mace guda daya Bahaushiya a Majalisar Dattijai ko ta wakilai sai kin ga matan kudu masu yawa. Haka kuma kowa ya san cewa al’adarsu da tamu ba daya ba ce, wanda hakan kuma kan yi tasiri wajen samar da dokokin da suka shafi mata domin su za su nemi abin da ya yi daidai da al’adarsu ba tare da yin la’akari da ya saba tamu al’adar ba. Amma kin ga idan muna da wakilci a wurin fa, komai za a yi sai an tuntube mu

Ya kike kallon siyasar mata a kasar nan?

E! maganar a bayyane take a Najeriya ba a son mata su yi mulki kwata-kwata. So ake yi mu zama ’yan amshin shata. Maganar da ake yin a kaso 35 da za a ba mata, ba da gaske ake yi ba. Kin san akwai ranar ce Gudaji Kazaure ya taba yin wata magana a majalisa cewa, “ba za ba mata mulki ba, saboda a gida mu na yi musu mulki, a nan ma kuma za mu ci gaba da yi musu mulki.” To na ga alama da gaske suke. Idan kin duba nan Kano, ba kawai aka hana mata takara ba, an yi wa wata haka a Kaduna, an yi a Kalaba. Mun rasa dalilin da ya sa ake son hana mata mulki, domin  addinin Musulunci  bai  hana mace ta yi wakilci ba. Sai dai duk da wannan abu da ake yi mana, ba za mu ce mun saki mun hakura ba. Za mu ci gaba da fitowa ana damawa da mu har Allah Ya sa mu samu.

Wata babbar matsalar da ke damun mata a harkar siyasa ba ya ga cewar mazan suna mamaye wuraren, akwai matsalar kudi da ake kashewa kafin a kai ga samun nasara ko kuma wurin yakin neman zaben, wanda kuma mata da yawa ba su da halin. Don haka idan an samu mace wacce ake ganin ta cancanta, ya kamata a taimaka mata musamman wajen abin da ya shafi kudi da suka hada da sayen fom da sauransu

Wane kira kike da shi ga ’yan siyasa gaba daya?

Babban kirana shi ne mu ji tsoron Allah. Duk abin da aka ce babu Allah a harka, to an shiga bata. Da ace ba mu yarda da Allah ba, to sai mu yi abin da muka ga dama. Tunda mun yarda da Allah, mun san cewa akwai ranar Alkiyama da Allah zai  tsaidamu mu bayar da shaida kan abin da muka aikata.