Rashin kudi ne babbar matsalar gwamnatin Jihar Bauchi – Baba Madugu
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Bauchi, Alhaji Baba Madugu ya bayyana cewa gwamnatinsu tana da sababbin tanade-tanade a kasa domin ciyar da jihar gaba, amma kuma karancin kudi na daya daga cikin abubuwan da ke kawo tarnaki ga gwamnatin Barista Mohammed Abubakar.Alhaji Baba Madugu ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu a […]
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Bauchi, Alhaji Baba Madugu ya bayyana cewa gwamnatinsu tana da sababbin tanade-tanade a kasa domin ciyar da jihar gaba, amma kuma karancin kudi na daya daga cikin abubuwan da ke kawo tarnaki ga gwamnatin Barista Mohammed Abubakar.
Alhaji Baba Madugu ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu a ofishinsa da ke Bauchi, inda ya ce, “Lokacin da Gwamna Mohammed Abubakar ya karbi ragamar mulki ya gaji bashin albashin ma’aikata na watanni kafin daga bisani ya nemo kudade a biya ma’aikata hakkokinsu da suke bin gwamnati. Shekara daya ke nan da ’yan watanni, kuma za mu iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu.”
Ya kara da cewa: “Gwamna Abubakar ya zo da manufofi masu kyau na bunkasa harkokin noma da kiwo tare da bunkasa kasuwanci a Jihar Bauchi, to amma ya iske babu kudi a kasa, kuma ga farashin mai ya fadi a duniya, ta yadda kudin shigar da jihar ke samu bai iya gudamar da tsare-tsaren.”
Ya ce Gwamnan ya nada sababbin shugabannin riko na kananan hukumomin jihar 20 ne a kokarinsa na kusanto da gwamnati ga jama’a.
“Akwai hanyoyi da dama da gwamnati ta ba da kwangilar gyara su a cikin fadar jiha har zuwa kananan hukumomi. Don haka muna kira ga jama’a su ci gaba da hakuri da wannan gwamnati wadda ta zo da manufofi masu kyau. Gwamna Mohammed Abubakar babban burinsa shi ne ya koya wa mutane yadda ake kama kifi tare da gyara tarbiyyar matasa ta yadda za su zamo mutanen kirki,” inji shi.
Ya tabbatar da cewa ma’aikatan kananan hukumomin jihar suna bin bashin albashin wata biyu, sai ma’aikatan jihar da suke bin bashin albashin wata daya, ya ce wannan shi ne gaskiyar abubuwan da suke faruwa a Jihar Bauchi.
Sai ya yaba wa jaridar Aminiya kan yadda take kamanta adalci a labaran da take bayarwa, inda ya yi kira da babbar murya ga ’yan siyasa da al’ummar jihar su ci gaba da bayar da goyon baya ga gwamnatin APC tun daga matakin jiha har zuwa tarayya domin samun nasarar da ake fata na mayar da kasar nan kan turbar kwarai.