Rashin kudi ne matsalarmu -Shugaban kungiyar IPSN
kungiyar yada addinin Musulunci (Islamic Platform Society of Nigeria -IPSN), ta ce rashin samun tallafin kudi na gudanar da harkokin kungiyar shi ne babban kalubalen da yake fuskantar su.Shugaban kungiyar na kasa, Imam Shafi’u Abdulkareem shi ne ya yi furucin yayin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wa’azin addinin musulunci […]
kungiyar yada addinin Musulunci (Islamic Platform Society of Nigeria -IPSN), ta ce rashin samun tallafin kudi na gudanar da harkokin kungiyar shi ne babban kalubalen da yake fuskantar su.
Shugaban kungiyar na kasa, Imam Shafi’u Abdulkareem shi ne ya yi furucin yayin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wa’azin addinin musulunci wanda kungiyar ta shirya a dakin taro na Adebola da ke unguwar Opebi a jihar Legas a karshen makon da ya gabata.
Ya ce ‘ka san duk abinda za ka gudanar da ya danganci al’amarin addini da kudi sai ka sami matsaloli. A yanzu kalubalen da muke fuskanta shi ne na halin-ko’in kula da musulmi ke nunawa wajen tallafawa ayyukan kungiyarmu. Ba kamar kiristoci ba da za ka ga suna tallafawa addininsu amma duk da haka muna kokarin wayar da kan mutanenmu dangane da muhimmancin ba da taimako don daukak addinin Allah’.
Ya kara da cewa ‘Sau da yawa idan aka ce jama’a su taimaka sai su rika yi maka kallon wanda zai damfare su ko kuma kana so ka cuce su wanda ba haka manufarmu take ba, manufarmu ita ce mu yada addinin musulunci da jawo wadanda ba musulmi ba su shigo cikin musulunci a tafi tare’.
Ya bayyana cewa burin kungiyar shi ne ta wayar da kan jama’a su fahimci addinin musulunci ta hanyar gudanar da wa’azi da laccoci da kuma tattaunawa tsakanin musulmai da kiristoci.
Saboda da haka sai ya ce shi ya sa kungiyar ba ta da hadafin yada wata manufa ta wata kungiya sai dai manufar musulunci ta bai daya.
Ya ce daya daga cikin ayyukan da kungiyar ta sa a gaba shi ne gayyato manyan malamai daga kasashe daban-daban da suka kware ta fannin wa’azi da Alkur’ani da Baibul.
‘Shi ya sa muka gayyato Shaikh Mabera daga jihar Sakkwato ya zo ya ba da lacca a kan dayantakar Ubangiji a cikin al’kur’ani da Baibul, muna sa ran za mu gayyato Yusif Deedat daga kasar Afirka ta Kudu da manyan malamai daga kasashen Amurka da Canada domin su ba da tasu gudunmawar’.