Rashin kudi ya sa ban karbi albashi ba – Gwamna Lalong

Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong ya ce rashin kudi a baitul-malin jiharsa ne ya sanya tun da ya ci zabe a watan Afrilu zuwa yau bai biya kansa albashi ba. Gwamna Lalong ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a Jos a lokacin da ya shiryar taron ganawa da ’yan jarida […]

Rashin kudi ya sa ban karbi albashi ba – Gwamna Lalong
Rashin kudi ya sa ban karbi albashi ba – Gwamna Lalong

Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong ya ce rashin kudi a baitul-malin jiharsa ne ya sanya tun da ya ci zabe a watan Afrilu zuwa yau bai biya kansa albashi ba. Gwamna Lalong ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a Jos a lokacin da ya shiryar taron ganawa da ’yan jarida domin cikarsa kwana 100 a kan karagar mulki. Ya ce Jihar Filato tana fama da rashin kudi wanda hakan ya kawo tsaiko wajen nade-naden mukarraban gwamnatin jihar.
Ya ce: “Rashin kudi ya sa ban biya kaina albashi ba, hakan kuma ya kawo tsaiko wajen rashin nade-nade mukarraban gwamnati, wadanda na nada ma har yau ba a fara biyansu albashi ba. Tabbas ni kaina ban karbi albashi ko na wata daya ba.” Gwamnan ya ce duk da rashin kudin da ake fama da shi a jihar ya yi abin a yaba masa a cikin kwanaki 100 na mulkinsa. “A bangaren sha’anin tsaro na sanya an kara mana ’yan sanda 150, kuma tuni an tura su yankunan kananan hukumomin Barikin Ladi da Riyom da ke fama da rikici.
Kan yaki da cin hanci da rashawa, muna zargin gwamnatin da ta gabace ni ta wawure dukiyar jihar, inda na tura batun ga Hukumar EFCC don binciken wadanda ake zargi. Duk da yake a yanzu hukumar tana jan kafa, amma zan tunatar da ita,” inji shi. Gwamna Lalong ya ce ya biya bashin albashin wata biyar daga cikin bakwai da ya gada, kuma ya ce zai biya na shida a wannan mako.
A lokacin da shugaban kungiyar ’Yan jarida ta Najeriya reshen Jihar Filato Yakubu Taddy yake jawabi, ya yaba wa Gwamnan bisa ga nasarorin da ya cimma, sai ya bukaci gwamnan ya kasance abokin ’yan jarida don ganin an guje wa watsa jita-jita kan gwamnatinsa.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista