Rashin kudin musayar waje ya durkusar da kasuwarmu – Alhaji Jibrila
Shugaban masu hada-hadar canjin kudi reshen kasuwar New Benin, Alhaji Jibrila Abdullahi ya bayyana matukar damuwarsa akan abin da ya kira faduwa sana’ar canjin kudi ga ‘yan kasuwa a wannan reshen kuma ya ce haka take a sauran rassan kasuwannin canjin da ke cikin Benin. Domin a cewarsa, duk gaba daya ’yan kasuwar Dodo guda […]
Shugaban masu hada-hadar canjin kudi reshen kasuwar New Benin, Alhaji Jibrila Abdullahi ya bayyana matukar damuwarsa akan abin da ya kira faduwa sana’ar canjin kudi ga ‘yan kasuwa a wannan reshen kuma ya ce haka take a sauran rassan kasuwannin canjin da ke cikin Benin. Domin a cewarsa, duk gaba daya ’yan kasuwar Dodo guda suke bautawa saboda haka matsalar ta shafi ko ina ina a jihar Edo
‘A halin da muke ciki yanzu ya san ba mu jin dadi a wannan harkar ko kadan, domin abin da muke gani yake tafiya yana dawowa a nan kasuwarmu sai dai mu hada da hakuri kuma mu yi wa Allah godiya saboda a da can ba haka lamarin yake a wurinmu ba, mun ji dadi sosai a lokutan baya, amma inda muka fara samun matsala tun alokacin da Banki ya bullo da wani tsarin baya ba mu da kudin Amurka Dala daga nan muka fara jin jiki da mu da abokan huldarmu, har kasuwar ta durkushe mana muka kasa samun madafa, tare da abokan huldarmu na kasuwa idan suka je Banki sai a hana su kudin musayar waje, har muka wayi gari matsaloli suka taro a kanmu,” inji shi.
Ya ce, mu da ke zaune a nan Benin muna da kwanciyar hankali saboda akwai zaman lafiya tsakaninmu da ‘yan asalin jihar ta Edo, domin mutane ne masu son baki a yankinsu. Saboda haka zan yi anfami da wannan damar inyi kira ga daukacin ’yan Najeriya da ce wa mu yi hakuri da juna, mu bar gaba da juna ko kyashi a kan samun da wasu suke da shi. Allah shi ne ya ba su abin da ya da ce. Mu dukufa da addu’o’in fatan alheri ga kasar mu, abin da muke jin yake ci gaba da faruwa a yankinmu na Arewa ba mu jin dadinsa, kuma yana jefa fargba a zukatanmu; mu da ke zaune a Kudu. Domin abin da muka fahimta shi ne, idan babu zaman lafiya, babu wata harka ta arziki da za ta gudana.
A cewarsa: “Ina bai wa wadannan masu tada kayar baya da ainihin ita gwamnatin tarayya su kai zuciya nesa, su zauna a tattauna ta hanyar sulhu; su fadi damuwarsu, wadda aka gani ta dace sai a yi musu domin a samu maslahar kawo karshen wannan kisan kiyashi da ake yi wa ‘yan Arewa, musamman a yankunan Barno da Yobe da Adamawa da fatan wannan kiran da na yi, tare da shawarar da na bayar ga ita gwamnati da wannan kungiyar ta Boko haram za ta samu karbuwa da yin aiki da ita.”
“Ina son ganin ‘yan Arewa da ‘yan kudu baki daya mu hadu, mu hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinki daya, domin ci gabanmu da ‘ya’yanmu da jikokinmu masu tasowa anan gaba. Domin mu sani fa babu wani mutum daban daga waje mai zuwa ya gyara mana in ba mu dinne ba muka tashi tsaye ,” a cewarsa lokacin da ya karkare bayanansa.