Rashin kwararrun malamai laifi wane ne?

A makalata ta makon jiya da na yi ta`aziyyar marigayi ABM Mukhtar Muhammad Shugaban Hukumar Daraktocin gidan Radyon Freedom da ke Kano, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a wani asibiti da ke birnin Landan a ranar Lahadi 1 ga wannan watan, na yi alkawarin in Allah Ya so a wannan makon zan kawo ta`aziyyar […]

Rashin kwararrun malamai laifi wane ne?

A makalata ta makon jiya da na yi ta`aziyyar marigayi ABM Mukhtar Muhammad Shugaban Hukumar Daraktocin gidan Radyon Freedom da ke Kano, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a wani asibiti da ke birnin Landan a ranar Lahadi 1 ga wannan watan, na yi alkawarin in Allah Ya so a wannan makon zan kawo ta`aziyyar rashin abokin aiki, kuma dana Tijjani Ado Ahmed, da Allah Ya yi ma rasuwa a kasar Amurka a ranar Asabar 30-09-2017, inda ya je don wakiltar gidan Radiyo Freedom wajen wani taro na makwanni biyu. Babban dalilin da ya sa na jinkirta ta’aziyyarsa zuwa wannan makon, bai wuce tsammanin da nike ba, na zuwa cikin makon za a kawo gawar Tijjani Kano don yi masa sutura.

 Amma sai ga shi har ya zuwa lokacin da na kammala wannan makala gawar marigayi Tijjani ba ta iso ba. Ni kuma ina ganin rashin da cewar ba a rufe mutum ba, in yi ta’aziyyar rubutu akansa ba. Don haka ina fata mai karatu, zai bi ni bashi zuwa mako na gaba in Allah Ya kaimu da rai da lafiya.         

Don haka mai karatu bari in dawo akan abin da makalata ta wannan makon za ta mayar da hankali akai, wato rashin kwararru kuma ingantattun malamai da aka dade ana fama da su a kasar nan, musamman tsakankanin Jihohin Arewa, ko a jihohin arewar ma, a jihohin shiyyar da ta kunshi Arewa maso Yamma, wato jihohi irin su Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da Sakkwato da Kebbi da Zamfara, shiyyar da ta fi sauran shiyyoyin kasar nan mafi yawan al’umma.  

Mai yiwuwa mai karatu a ranar Talatar makon da ya gabata, ya ji irin babatun Gwamnan Jihar Kaduna Malan Nasir El-Rufa’i, lokacin da yake karbar a yarin Bankin Duniya a fadar gwamnatin jihar da ke Kaduna, yana kokawa a kan irin yadda daga cikin malaman makarantun Firamare 33,000, da suka zauna jarrabawar ‘yan aji hudu na makarantun Firamare, 21,700, ba su iya cin jarrabawar ba, wato gwari-gwari malamai 11,300 kawai su ci jarrabawar sauran kashi 66 cikin 100 ba su kai labari ba.

Gwamna El-Rufa’i ya danganta wannan al’amari da irin yadda gwamnatocin da suka gabata a jihar, suka rinka sanya harkokin siyasa a fannin ilimi na jihar. A fadarsa yanzu gwamnatin jihar ta yi aniyar daukar malamai 25,000, don farfado da fannin ilmin Firamare, abin da ya ce haka na daga cikin hanyoyin da gwamnati za ta samu iya canja mawuyacin halin da tabarbarewar ilmi ya shiga a jihar.

A kan tabarbarewar fannin ilmin Firamare, ka iya cewa ta gwamnatin Kaduna ce ta bayyana a sarari zuwa yanzu, amma nasan ko kaffara mutum ba zai yi ba idan ya yi rantsuwa da Allah cewa haka koma munin ya fi haka idan da za a binciki matsayin ilmin koyarwar malaman makarantun Firamare kai har ma da na gaba da Firamare a wasu jihohin Arewacin kasar nan, musamman na wadancan jihohin shiyyoyin Arewa maso Yamma da na ambata tun farko. 

Shi dai nauyin ba da ilmi ga ‘yan kasar nan, bisa ga tanade-tanaden sassa daban-daban na Kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, da aka yi wa kwaskwarima, ya tanadi kowace gwamnati (karamar hukuma da jiha da tarayya) na da rawar da za ta ta ka wajen bayar da ilmi. Majalisun kananan hukumomi su ke da alhakin dauka da biyan albashin malaman makarantun Firamare, kai har ma da gina musu ajujuwa da sa ma musu kayayyakin koyo da koyarwa da sauran abubuwa. Yayin da gwamnatocin jihohi suke da alhakin kula da ilmin gaba da Firamare da ma na manyan makarantun da suka kirkira dari bisa dari. ita ma gwamnatin tarayya tana da na ta makarantun gaba da Firamare da manyan makarantu da ta ke kula da su kacokan a cikin jihohi daban-daban na cikin kasar nan. Ba ya ga hukumar harajin ilmi da ta kafa wadda ta kan ba da tallafi a fannoni daban-daban a cikin gudanar da manyan makarantu walau na gwamnatun tarayya ne ko na jihohi. 

Mai karatu daga wannan bayani na sama za ka iya gane wasu daga cikin abubuwan da suke haddasa tabarbarewar ilmi na Firamare, wanda ya ke shi ne harsashin ilmin boko, wato bisa ga irin yadda mafi yawan dawainiyar tafiyar da shi kusan kacokan ta ke karkashin majalisun kananan hukumomin kasar nan, kananan hukumomin da ake kokawa ba su da kwararru kuma wadatattun ma’aikata tun daga sama har kasa. Sannan uwa uba ga shi ba su da cikakken ‘yancin cin gashin kai, musamman wajen yin tusarrafi da kudaden shigarsu, wadanda gwamnonin jihohi kan handame musu da sunan Ajiyar hadin gwiwa.

Ko shakka babu siyasa ta taka gagarumar rawa cikin tabarbarewar fannin ilmin Firamare a wannan lokacin, kasancewar shugabanni da kansilolin majalisun kananan hukumomi na kasar nan sukan yi yadda suka ga dama, walau wajen daukar malaman makarantun aiki ko kara musu girma ko ladaftar da su da batun kara musu ilmi don samun kwarewa. Zan iya tunawa wata shekara a nan Jihar Kano, majalisun kananan hukumomi suka dauki malaman makarantu Firamare aiki, al’amarin da ya kai tun farko ba a dauki wadanda suke da ilmi koyarwa ba, sannan kuma aka rinka aza su a kan kasa da albashin da suka cancanta a ba su. Sai bayan da aka gama sai aka gane cewa ai kudin da aka kasafta don daukar malaman sun haura abin da aka ba malaman, wannan ta sa aka rinka kiran malaman daya- bayan-daya ana canja matsayin albashin da aka ba kowa har aka samu daidaito.

Ko da a kwanannan lambar yabo da kungiyar malaman makarantu ta kasa NUT ta bai wa Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta ba shi ne a kan gagarumin karin girma ga gwamnatinsa ta yi wa kusan dubun dubatar malaman makarantun Firamare da suka shafe shekaru aru-aru a kan matakin albashi daya. Idan kuma ka bincika haka za ka tarar da irin wannan labarin a kusan dukkan Jihohin Arewa, alhali malaman makarantun gaba da Firamare da suke karkashin kulawar gwamnatocin jihohi ba su fuskantar irin wancan cin kashi. Mai karatu, da irin wadannan matsaloli da makamantansu da ban iya ambatawa ta ina karatun Firamare zai samu wani tagomashi?

Har sai gwamnatoci majalisun kananan hukumomi da na jihohi da na kungiyoyin iyayen yara da malamai na makarantun Firamare sun tashi tsaye sun kuma kama ta fannoni daban-daban, kama daga samar da kwararru kuma wadatattun malamai da gine-gine da ayyukan koyo-da-koyarwa da dukkan abubuwan da za su kyautata jin dadin malaman makarantun Firamare ka na wannan fannin ilmin boko zai inganta kamar yadda ake bukata. 

Ita ma Majalisar yi wa Malaman makarantu rijista ta kasa wato TRCN da aka kafa tun a shekarar 1993, don tabbatar da cewa dukkan wanda yake koyarwa yana da ilmin da ya kamata, kuma ta rika gudanar musu da tarurrukan kara wa juna ilmi da aniyar bunkasa ayyukansu da lallai ita ma ta tashi tsaye don ceto wannan fanni mai muhimmancin gaske a cikin ilmin boko.