Rashin kyan hanyoyin Najeriya ne ya sa za mu sayi motoci masu tsada – Majalisar Dattawa
Majalisar ta ce motocin Ministoci ma sun fi nasu yawa
Majalisar Dattijai ta kare shirin da take yi na sayen motocin alfarma samfurin SUV ga mambobinta.
Kodayake majalisar ba ta bayyana ainihin kudin motocin ba, amma ta ce mambobinta sun ce sun fi son wadanda aka shigo da su daga ketare a kan wadanda ake kerawa a gida Najeriya.
- Gwamnan Katsina ya raba wa daliban Jihar miliyan 640 a matsayin tallafin karatu
- An yanke wa likitan da ya yi wa ’yar uwar matarsa fyade daurin rai da rai
Da yake mayar da martani a kan lamarin yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja, shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar, Sunday Karimi, ya ce ’yan Najeriya suna sanya ido a kan ’yan majalisar amma sun kawar da idanun nasu daga kan na ministoci.
A cewarsa, kowanne daga cikin ministocin na da akalla motocin aiki guda hudu.
Sanatan ya ce, “Wanda yake da mukamin Minista na da motoci kirar Land Cruiser sama da guda uku, da Prado da kuma wasu motocin, amma ba kwa tambayarsu ba’asi, me ya sa sai na ‘yan majalisa?
“Wadannan motocin da kuke gani, la’akari da irin lalacewar hanyoyin Najeriya, idan na je mazabata na dawo da su, sai sun fita hayyacinsu.
“Dalilin da ya sa muka amince mu sayi irin wadancan motocin shi yanayin kudinsu da kuma juriyarsu.
“Ba wai da ka muka yanke shawarar wadannan motocin ba, sai da muka duba yanayin kwarinsu da kuma yanayin rashin kyan hanyoyin Najeriya.
“Muna son mu sayi abin da za mu iya yin amfani da shi na tsawon shekaru hudu. Kun riga kun san cewa batun sayen motocin majalisa ba sabon abu ba ne, duk bayan shekaru hudu sai an sabunta shi.”
Sanata Sunday ya kuma ce hatta ’yan majalisun jihohi na sayen motocin aiki, ba su kadai suke saye ba.
“Idan ka je majalisun jihohi, za ka ga yawancinsu an saya musu motoci tun ma kafin a rantsar da su, Gwamnoni sukan saya su ajiye musus suna jiransu, haka ma Shugabannin Kananan Hukumomi,” kamar yadda ya bayyana.