Asarar da Arewa ke yi saboda rashin wutar lantarki
Ɓarayi na amfani da rashin wutar Arewa a matsayin wata dama suna sace manyan wayoyi da kayayyakin lantarki a tiransufoma
Masana’natu da kananan ’yan kasuwa a Arewacin Nijeriya sun fara durkushewa a sakamakon shafe kwana takwas a jere babu wutar lantarki a yankin.
’Yan kasuwa da iyalai da sauran harkoki a yankin sun shiga tsaka mai wuya a yayin da matsalar ta sa kamfanoni sallamar ma’aikata, wasu kuma na fargabar durkushewa idan ba a magance ta ba.
“Yau kwana biyar ke nan da muka bukaci ma’aikatanmu su koma gida, muna jira mu ga al’amarin ya yi sauki,” in ji mai kamfanin casar shinkafa a Gombe, Malam Umar Musa.
Wani mai sayar da kifin kankara da sauran kayan sanyi a garin ya ce, “Idan har ba a magance matsalar da wuri ba, to ni da kananan ’yan kasuwa kamata, za mu durkushe.”
- NAJERIYA A YAU: Dalilin da ’yan Nijeriya suka yi watsi da ababen hawansu?
- Muna aiki tuƙuru don gyara wutar Arewa — TCN
Aminiya ta samu rahoto cewa bata-gari a yankin na amfani da yanayin rashin wutar wajen sace-sacen muhimman kayan wutar lantarki da tiransufomomi.
Asibitoci da cibiyoyin kasuwanci da sauran al’ummar yankin na kokawa kan yanda harkokinsu suka samu koma sakamakon wannnan matsala.
Asibitoci da cibiyoyin gwaje-gwajen kiwon lafiya, wadanda suka dogara kan samun tsayayyar wutar lantarki domin gudanar da ayyukansu suna fama da tsaiko inda dole ta sa suke rage yawan aikin da suke gudanare.
Suna kuma kokawa bisa yadda suke kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen mai, wanda ya yi tsadar da bai taba yi ba, domin gudanar da ayyukansu a sakamakon rashin wutar.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin da ’yan Nijeriya suka yi watsi da ababen hawansu?
- Muna aiki tuƙuru don gyara wutar Arewa — TCN
Kasazalika ’yan kasuwa, musamman masu sayar da kayan sanyi da na ƙanƙara, inda suka bayyana cewa matsalar da jawo musu mummunar asara, ta hanyar lalacewar kayansu.
Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa wannan matsala da tsadar man da suke saya domin kuma firinji kayansu, ta sa ba su da zaɓi face su ƙara farashin kayayyaki.
Wata matar aure ta koka kan yadda rashin wutar ta haddasa tashin gwauron zabon farashin ƙanƙara zuwa Naira 1,500, wanda shi ma din ba a samu sai an yi takakkiya
Masu sana’ar ga-ruwa da gidajen ruwan da suke sayowa sun ƙara farashi, sakamakon tsada da kuma yawan man da a halin yanzu suke dogara da shi a injinan rijiyoyin burtsatsen nasu.
Matsala ta ƙara ƙamari a yayin da ɓarayi ke amfani da rashin wutar na sama da mako guda a matsayin wata dama inda suke zuwa suna sace manyan wayoyi da kayayyakin lantarki a tiransufoma.
Kamfanin Samar da Lantarki na Nijeriya (TCN), ya ba wa al’ummar yankin tabbacin cewa yana yin duk mai yiwuwa domin shawo kan matsalar.
Sai dai kuma ya bayyana cewa tashin tsaro a yankin da abin ya faru ya kawo tarnaƙi ga yunkurinsa na gano ainihin inda matsala take da kuma magance ta.
Akalla sau bakwai aka samu ɗaukewar wutar lantarki a fadin Nijeriya a shekarar 2024 da muke ciki.
Na baya-bayan nan ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata bayan lalacewar babban layin lantarkin mai karfin 330kV da ya taso daga Enugu zuwa Binuwai da suka wanda ya taso daga Shiroro zuwa Kaduna.
Zuwa yanzu, an shafe kwana takwas babu wuta a yankin Arewa maso Yamma da Arewa Maso Gabas da wani yanki na Arewa ta Tsakiya, a sakamakon wannan matsala.
Kano:
Majinyata a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano sun bayyana cewa da dare ba sa iya barci saboda sauro da ke damun su a sakamakon kashe injin janareta da hukumar asibitin ke yi.
Wani majinyaci mai suna Malam Umaru Direba ya ce ya ce dole ta sa suka koma kunna maganin sauro na hayaƙi, saboda yadda sauron suke addabar su.
Wani jami’in asibitin yanda shaida wa wakilinmu cewa a kullum ana sayen man Naira 500,000 a asibitin, shi ya sa aka taƙaita kunna injijan janareta, musamman da yamma.
Ya bayyana cewa cewa duk da haka, ɓangaren ayyukan gaggawa na asibitin yana amfani da na’urar lantarki mai amfani da hasken rana.
Wasu masu sayar da a Kasuwar Tarauni, Hussaini Rufa’i da Salihu Usman suna bayyana cewa rashin wutar ta jawo musu asara, saboda ba sa iya adana kaya masu saurin lalacewa.
Babban Jami’in Kasuwanci na Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), Abubakar Jimeta ya dora laifin rashin wutar na tsawon lokacin a kan lalacewar babban layin wutar lantarki na kasa da kuma sace kayan wutar da barayi ke yi.
Gombe:
wani mai sayar da kifin kankara a Gombe, Muhammad El-Kabeer ya ce, rashin wutar ta jawo musu gagarumar asarar, inda a kullum sai sun kunna injin janareto na kusan awa shida domin kayan su yi sanyi
Ya ce hakan ta sa dole kayan nasu suka kara tsada, lamarin da ya haddaas karancin ciniki, domin kwastomomi ba sa iya saya yadda suka saba.
Muhammad ya ci gaba da cewa, “Idan har ba a shawo kan matsalar nan ta wutar lantarki da wuri ba, to ni da kananan ’yan kasuwa kamata, jarinmu zai karye.”
Shi ma wani mai kamfanin shinkafa a Gombe, Malam Umar Musa ya bayyana cewa rashin wutar ta sa kamfanin nasa ya daina aiki.
“Yau kwana biyar ke nan da muka bukaci ma’aikatanmu su koma gida, muna jira mu ga al’amarin ya yi sauki,” in ji mai kamfanin casar shinkafan.
Kaduna:
A Jihar Kaduna, iyalai na kokawa kan wanann matsala, inda suka ce ta sa kuncin rayuwa ta kara tsanani.
Al’ummar yankin Hayin Malam Bello da ke unguwar Rigasa a Kaduna sun bayyana cewa tasu matsalar ta kara kamari inda bata-gari suka sace kayan tiransufomar unguwar a yayin da ake fama da wannan yanayi.
Wata ’yar unguwar, Halima Mu’azu, ta ce sana’ar mahaifiyarta ta sayar da zobo da kunu ya samu matsala saboda rashin wutar.
Wani shugaban al’ummar yankin, Alhaji Ibrahim Fage, ya ce sun fara yin karo-karon kudade domin samun abin da za a gyara transufomar.
Jos:
A garin Jos da ke Jihar Filato, ’yan kasuwar katako sun ce cinikinsu ya ragu matuka sakamakon tsawon lokacin da aka dauka babu wutar.
Abubakar Salihu da ke sayar da katako a kasuwar ya ce, “Wannan kasuwa an san ta da yawan harkokin hada-hada amma yanzu komai ya tsaya, sai dai ka zo a ka yi zaman jira ka koma gida.
“ Sai da wuta muke iya kunna injina mu yi aiki, saboda wannan matsala ta rashin wuta ta kawo mana cikas sosai.”
Aminiya ta gano cewa bata-gari sun sace kayan tiransufoma a yankin Unguwar Rogo da Garage da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa ta jihar.
Wani mazaunin yankin Garage, Muhammad Munir ya ce bata-garin“sun sace muhimman kayan tiransufomar da za su ci makudan kudade masu yawa kafin a iya maido da su.”
Alhaji Bala Tanko mazaunin Unguwar Rogo, cewa ya yi barayin “sun yi amfanin da yanayin rashin wutar suka sace wayar tiransufomarmu suka bar mu sama da kuwana shida a duhu.”
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Jos (JED) ta bukaci al’umma da su tashi tsaye wajen bayar da kariya ga kayayyakin samar da wuta.
Bauchi:
Iyalai da iyalai da dama na cikin halin ha’ul’a’i a Bauchi sakamakon tsayawar harkokin masu sana’ar injin nika, wadanda rashin wutar ta hana su aikin nika hatsi
musamman wadanda suka dogaro da tuwo da dangoginsa a matsayin babban abincinsu
Harkokin masu sana’ar injin nika sun tsaya cik a Jihar Bauchi, inda rashin wutar ta sa ba sa iya nika hatsi.
Wannan lamari ya jefa iyalai da dama cikin halin ha’ul’a’i, musamman wadanda suka dogaro da tuwo da dangoginsa a matsayin babban abincinsu.
Yobe:
Shugaban ’yan kasuwar kayan gwari a Jihar Yobe, Alhaji Sani Abubakar ya bayyana cewa sun “kimanin wata guda ke nan da ake samun koma -bayan ciniki saboda mutane ba sa saya da yawa, wasunmu kuma kayan nasu na rubewa saboda rashin wurin ajiya mai sanyi.
Aminiya ta gano cewa masu sana’ar ga-ruwa jihar sun kara farashi a Damaturu, hedikwatar jihar, inda suke sayarwa ga duk wanda ya fi saya da daraja. Kimain kashi 70 bisa 100 na mazauna Damaturu sun dogara ne wajen samun ruwa daga rijiyoyin burtsatse.
Adamawa:
Wata mata a yankin Jimeta a Jihar Adamawa, Hajiya Asma’u ta ce ta yi asarar kayan abinci masu sauyran lalacewa na makudan kudade saboda rashin wutar.
A nata bangaren, jami’ar hulda da Jama’a ta Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Yoba (YEDC) Blessing Tunoh, ta ce sun samu rahoto 37 na satar kayan wutar lantarki a watanni uku na farkon wannan shekara.
Binuwai:
Friday Ejembi a Karamar Hukumar Otukpo ta Jihar Binuwai ya ce sun shafe kwana 10 babu wutar lantarki a unguwar Obotu-Ugboju, a yayin da masu kananan sana’o’i ke kokawa kan rashi wutar.
Su da masu sana’o’in hannu a garin Makurdi, hedikwatar jihar suna kokawa kan tsadar mai da suke saya a kan N1,200 zuwa N1,250.
Wata mai sayar da kifin kankara a Karamar Hukumar Gboko, Mwuese Terkula, ta ce, “idan babu wuta ba zan iya adana kifi ba, don haka idan wannan matsala ta ci gaba, dole sai dai in hakura da wannan sana’ar.”
Nasarawa:
A Jihar Nasarawa, wata mata mai suna Aisha Umar ta ce rashin samu wutar yadda ya kamata, ya ja mata asara a gidanta da kuma kasuwancinta.
Manajan yankin na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) na Lafia, Injiniya Baro Ahmed, ya bayyana cewa a halin yanzu, karfin wutar da ake samarwa a Nijeriya megawatt 4,000 ne kuma ya yi kadan sosai.
Ya bayyana cewa megawatt bakwai ake ba wa Jihar Nasarawa a yanzu, maimakon megawatta 20 da ta saba samu.
Kwara:
Lamarin ya kara karami a Asibitin Koyarwa na Jam’iar Ilorin (UITH), inda ake fama da matsalar wutar a daidai lokacin da ma’aikatan jami’a suka tsunduma yajin aiki.
Aminiya ta gano cewa, in banda bangaren kula da lafiya na gaggawa da ke asibitin, ba ba kunna injin janareto sai da dan takaitaccen lokaci ga bangaren ofisoshi masu muhimmanci.
Muna kokarin gyara —TCN
Kamfanin TCN ya ce yana aiki tare da Ofishin Mashawarcin Shugaban Qasa kan Tsaro domin gyara layin lantarkin Shiroro zuwa Kaduna da bata-gari suka lalata.
Lalacewar layin ne ya jefa Jihohin Kaduna da Kano da wasu manyan garuruwan Arewa cikin duhu na tsawon kwanaki.
Sanarwa da kakakin TCN, Ndidi Mbah ya fitar ta ce, duk da kalubalen tsaro da ake fuskanta, bangarorin biyu suna yin bakin kokarinsu wajen ganin sun gyara wutar an ba da jimawa ba.
Ana iya tuna cewa jami’ar TCN, Injiniya Nafisa Asli ta bayyana cewa ‘yan ta’adda ne suka lalata babban layin lantarkin Shiroro zuwa Kaduna, wanda ke ba wa yankin Arewa wuta.
Amma Mbah ya bayyana cewa suna aiki domin ganin ofishin NSA ya samar da isasshen tsaro domin ba wa jami’an kamfanin damar zuwa wurin da abin ya faru domin gyara wutar.
A gaggauta gyara wutar Arewa —Sanatocin yankin
Kungiyar sanatocin Arewa sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta gyara wutaryankin da ya lalace tare da daukar matakan hakan aukuwar hakan a nan gaba.
Sanarwar da suka fitar dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Sanata Abdulaziz Yar’adua bayan wani zama da suka yi a Kaduna ta kuma bukaci gwamnati ta tabbata ta dauki duk matakan hanzarta gyara layin lantarki na Shiroro zuwa Kaduna, wanda lalacewarsa ta jefa yankin cikin duhu na tsawon sama da mako guda.
Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya sanar cewa ’yan ta’adda ne suka lalata layin lantakarin na Shiroro zuwa Kaduna, wanda shi ke samar da wuta ga yankin Arewa.
Ya bayyana cewa, ya riga ya tanadi duk kayan da suka kamata domin gyara wutar, amma ofishin mashawarcin shugaban kasa kan sha’anin tsaro ya gargadi kamfanin game da hadarin shiga wurin, saboda gudun fadawa hannun ’yan bindiga.
Amma kamfanin ya bayyana cewa yana aiki tare da ofishin domin ganin cewa an gyara wutar nan ba da jimawa ba.
Ina da maganin matsalar —Atiku
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023 kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce kundin yakin neman zaben nasa yana da bayanin hanya mafi inganci na magance wannan matsalar.
Ya bayyana cewa mafita ita ce cire harkar wutar lantarki daga jerin abubuwan da Gwamnatin Tarayya ce kadai ke da ikon samarwa.
“A ba wa gwamnatocin jihohi dama da karfin gwiwar samarwa da rarraba lantarki da kansu,” in ji Atiku.
Muna asarar biliyoyi —Kamfanoni
Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun ayyana cewa matsalar ta jawo musu asarar biliyoyin Naira.
Wani daga cikin kamfanonin da ya nemi a boye sunansa ya bukaci a hukunta TCN kan gazawarta wajen samar da wutar yadda ya kamata.