Rashin Lantarki: An lalata tiransifoma 80 cikin kwanaki 10 —  JED

An sace manya-manyan wayoyin wutar masu rarraba wutar lantarkin ga unguwanni a tsawon lokacin daukewar wutar, jihar Filato ta fi shafar matsalar.

Rashin Lantarki: An lalata tiransifoma 80 cikin kwanaki 10 —  JED

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (JED) ya bayyana cewa sama da taransifoma 80 ne aka lalata da kuma sace wayoyin cikinta a lokacin da aka samu matsalar wutar lantarki a Arewa.

Kamfanin ya kuma bayyana cewa, an sace manya-manyan wayoyin wutar masu samar da wutar lantarki ga unguwanni a tsawon lokacin, inda ya ƙara da cewa jihar Filato ta fi shafar matsalar.

Babban jami’in fasaha mai kula da ayyuka, Injiniya Hamisu Wakili Jigawa ya bayyana wa Aminiya hakan a hedikwatar kamfanin JED a ranar Juma’a.

A cewar jami’in fasaha, ayyukan masu lalata tiransifoma ɗ in sun kawo naƙasu wajen samar da wutar lantarki cikin sauƙi da inganci ga unguwannin da abin ya shafa.

Ya ce “ɓarnar da aka yi wa na’urar tiransifoma ɗ in wajen satar wayoyin wutar sun kawo ƙalubale sosai. Matsayin ɓarnar ta yi yawa. Wasu layukan sun riga sun lalace gaba ɗ aya.

“  Wayoyin na’urorin al’miniyom ɗ in da ke rabar da wutar ga wasu unguwannin gaba ɗaya sun lalace. Muna da kusan ƙarfin wuta 213 kɓs waɗanda gaba ɗaya ba su da na’urori na na rbar da wutar kwanaki.

 A jiya ne muka iya gyara na ƙarshe. Mun yi asarar na’urorin rarraba wutar da yawa musamman wayoyin da suke rarraba wutar lantarki daga tiransifoma.

A wasu lokuta, masu ɓarnar suna buɗe tiransfoma, su kwashe mai a ciki da komai gaba ɗaya. Tankin ya zama fanko kawai, “in ji shi.