Rashin madatsar ruwa ke hana mu noman rani a ’yandaki – Salele ’Yandaki
Wani manomi mai suna Alhaji Salele ’Yanɗaki ya ce, rashin ruwa ko madatsar ruwa ke sa ba su noman rani a yankin ’Yandaki da ke Karamar Hukumar Kaita. Manomin ya shaida wa wakilin Aminiya cewa, “Sanin kowa ne Karamar Hukumar Kaita na daga cikin kananan hukumomin da ake da su a Jihar Katsina wadda ta […]
Wani manomi mai suna Alhaji Salele ’Yanɗaki ya ce, rashin ruwa ko madatsar ruwa ke sa ba su noman rani a yankin ’Yandaki da ke Karamar Hukumar Kaita. Manomin ya shaida wa wakilin Aminiya cewa, “Sanin kowa ne Karamar Hukumar Kaita na daga cikin kananan hukumomin da ake da su a Jihar Katsina wadda ta yi fice a batun noma wanda ya hada da na rani,” inji shi.
Ya ce “Ana noma tumatar da albasa, da tattasai da sauransu a wannan kasa, abin da ya shafi can wajen bangaren ’Yanhoho da Gafiya, ya nufi har wajen su Girka, Abdallawa har zuwa Dankama, dukan wadannan yankuna babu inda ba a wannan noma na rani sai nan shiyyar ’Yanɗaki.”
Manomin ya ce, akwai manoma a wannan yanki na ’Yandaki wadanda kuma suka shahara a wajen noman damina, amma har yanzu wannan matsala ta rashin ruwan da za su yi noman rani a yanki shi ne babban abin da ke ci masu tuwo a kwarya ga su kuma da wuraren da za su yi wannan noma.
“Saboda haka, a madadin jama’ar wannan yanki muke mika kokon barar mu ga shi Kantoman riko na karamar hukuma ta Kaita, Injiniya Bello Lawal ’Yandaki wanda kuma dan wannan yanki ne, da ya mika kokenmu ga Gwamna Masari wanda shi ma kowa ya san masani ne a kan harkar ruwa, kuma Gwamna ne wanda yake kula da batun harkokin noma kamar yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake kira, a dubi wannan yanki ta yadda za a bullo mana da wata hanyar da za mu rika amfana ta wannan hanya. Ba sai na ce komai ba ga matasanmu wadanda aka sani da cewa da zarar an samu wannan dama, to yankin ’Yandaki zai zamo daga cikin wuraren da za a yi alfahari da su ta wannan fuska.” inji Alhaji Salele ’Yandaki.
A wani labarin kuma, wadansu matasa ’yan uwan juna, Malam Shi’itu da Malam Shehu da suke noman rani a wani kauye mai suna Tarkama da ke a Karamar Hukumar Kaita, sun nuna bukatuwar kara wayar musu da kai musamman a dabarun noman ranin na zamani.
Su ce, noman sun gaje shi ne iyaye da kakanni, amma in baya ga ’yan shekarun nan hatta amfani da injin ban- ruwa ba su sani ba. “Muna noman tumatiri da albasa da tattasai a wannan sashe, tun daga nan har zuwa Masaki da Kwangwami da Unguwar Jibo da sauransu, amma gaskiya muna da karancin sani a kan wasu abubuwan na zamani kan noman ranin,” inji shi.
Muna so mu kara fadada noman namu da sauran wasu kayan da ake nomawa a ranin amma bamu da ilmin yin hakan. Saboda haka, muke kira ga wadanda abin ya shafa da su rika shigowa irin wadannan lunguna domin ilmantar da mu, domin manoman suna cikin lunguna ba bakin titi ba”, kamar yadda manoman suka ce. Bisa ga binciken da Aminiya tayi, a halin yanzu yankunan da ake yin wannan noman rani a yankin na karamar hukumar Kaita na gab da fara fitar da kayan noman ranin da suka noma. Binciken ya nuna a wannan yanki a yanzu suna daga cikin manoman tumatarin da za’a iya dauka ayi doguwar tafiya da shi ba tare da ya lalace ba. Binciken har ila yau, ya lura da cewa, ana ci gaba da kara samun wuraren noma a yanki kasancewar hatta da wasu daga ciki makwabta har daga cikin garin Katsina ana samun masu shiga wannan yanki domin yin wannan noma na rani. Sai dai kuma kamar yadda wasu manoman suka koka, akwai karancin ilimin noman ranin na zamani da kuma wasu kayan noman irin na zamani.