Rashin makadi ne matsalata – Mawaki Ahmad Nagudu

Wani matashi da ke wakokin Hausa a Jihar Legas mai suna Ahmad Umar Nagudu ya ce rashin makadin da hankalinsa ya kwanta da shi ne matsalar da ke damun sa.Ahmad Nagudu dan asalin Jihar Legas ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.Ya ce: “Gaskiya a nan […]

Rashin makadi ne matsalata – Mawaki Ahmad Nagudu
Rashin makadi ne matsalata – Mawaki Ahmad Nagudu

Ahmad Umar NaguduWani matashi da ke wakokin Hausa a Jihar Legas mai suna Ahmad Umar Nagudu ya ce rashin makadin da hankalinsa ya kwanta da shi ne matsalar da ke damun sa.
Ahmad Nagudu dan asalin Jihar Legas ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.
Ya ce: “Gaskiya a nan Jihar Legas muna da karancin masu kida. Shi ya sa nake shan wahala kwarai da gaske wajen samun makadin da hankali zai kwanta da shi. Mun saba da kidan gambara  amma su kuwa a Arewa asalin Hausar suke yi shi ya sa suka yi mana nisa, amma ina fatan Allah Zai fitar da ni daga wannan matsala na samu makidin da raina zai kwanta da shi ta yadda idan na tashin yin waka ba zan yi wata fargaba ba.”
Ahmad dan kimanin shekaru 24 a duniya ya bayyana cewa ya shiga harkokin waka ne saboda sha’awar da yake da ita tun yana karami.
Daga nan sai ya ce ya yi wakoki da yawa wadanda ba zai iya kirga su ba lokaci guda.
“Ka san shi komai ra’ayi ne. To ni ina da ra’ayin waka kuma ina sha’awarta tun ina karami. Idan na ga mutane na yin waka sai in rika sha’awarsu har ta kai ina kwaikwayar wadansu daga cikin mawaka. Daga baya da na taso sai na fara yin waka tun ina yi kadan-kadan har sunana ya fito duniya. Ya zamana ina buga wakokina na kaina.” In ji shi.
Ya kara da cewa  wakar sabuwar rayuwa da son-maso-wani su ne wakokin da ya yi fice da su.
Amma ya ce ya fi son wakar son-maso-wani saboda waka ce ta aure da soyayya.
Saboda haka sai ya ce burinsa ya yi fice mutane su san shi a sassa da dama na duniya.
“Na samu nasarori a harkar waka wanda suka hada da sanin jama’a da kuma haduwa da mutane daban-daban. Idan na tuna da wannan nasara sai na ji wani farin ciki da murna’. In ji shi.