Rashin mutunta harshen Hausa ne babban kalubalenmu – Sabo Wushishi

Ko za ka fara da bayyana tarihinka a takaice? Sunana Mahmud Sabo Wushishi, Shugaban Nurul Islam MSMS wadda ta somo tun daga Sakkwato a 1977, a nan kuma Kaduna na bude Nurul Islam a Unguwar Sanusi a 1980, bayan na baro Kwalejin Sultan Abubakar da ke Sakkwato. Kuma kafin in je wannan kwaleji, na yi […]

Rashin mutunta harshen Hausa ne babban kalubalenmu – Sabo Wushishi

Ko za ka fara da bayyana tarihinka a takaice?

Sunana Mahmud Sabo Wushishi, Shugaban Nurul Islam MSMS wadda ta somo tun daga Sakkwato a 1977, a nan kuma Kaduna na bude Nurul Islam a Unguwar Sanusi a 1980, bayan na baro Kwalejin Sultan Abubakar da ke Sakkwato. Kuma kafin in je wannan kwaleji, na yi karatun Alkur’ani da Tajwidi a Jihar Borno.

Tun ina firamare a Wushishi na soma saurarun rediyo da karanta jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da kuma rubuta zabi sonka da ra’ayoyi a wancen lokaci. Duk wanda yake tsohon mai sauraron redyio, yana jin wannan suna a sauran shirye-shirye na Musulunci, musamman a Gidan Rediyon Tarayya Kaduna. 

Na rika karanta wa Mai Shari’a marigayi Bashir Sambo tambayoyi a rediyo (Allah Ya jikansa). Kuma na gabatar da shirin ‘Masu Hikima Sun Ce’ da ‘Rayuwar Musulmi,’ a lokacin da sabani ya shiga tsakanin ’yan darika da ’yan Izala a farkon fitowarta kafin a yi mata rajista a 1977. 

Na kuma koyar a makaranta da ke Unguwar Sarki a karkashin Jama’atu Nasril Islam, inda a wannan lokaci dan abin da ake ba mu Naira 75 ne. A wannan lokaci ne na hadu da Abdullahi Katsina wanda ya soma Jakar Magori na farko, inda ya nemi in rika yi masa wani rubutu. A nan ne na soma yi masa Masu Hikima Sun Ce, wanda ya yi matukar farin jini har ake sa shi sau biyar a rana daya, wanda bai wuce minti uku zuwa biyar ba.

Sai ga shi yanzu na ji wani yanzu yana kwaikwayona a Gidan Rediyon Amurka, wanda kuma na tabbata masu sauraro za su iya yanke wannan hukunci.

Akwai rubuce-rubuce na Masu Hikima Sun Ce har na hadu da Alhaji Umaru Dambo ya karbi kwafi a hannun Sulaimanu, wanda shi ne Darakta a lokacin na sashen Hausa. Kuma wannan shiri da ake ji na Hajjin Bana, ni ne na yi wannan takahidi da ake ji na Aikin Hajji, watau “Labbaikallahumma Labbaik…” Ni ne na soma tsara karin domin ni ne furodusa na biyu na shirye-shiryen Musulunci.

Ban taba samun matsala ba domin a lokacin Allah Ya jikan Malam Ibrahim Arab, an zo da wani rubutu daga kasar Saudiyya a kan Mauludi, Alhaji Yasuf Ladan ya turo su wajena. A lokacin tun da aikin rediyo na biyayya ne da hakuri, da ya ce ga wata takarda ya zo da ita, sai na amsa na gabatar. Daga nan ne sai ni kuma matsala ta so ta same ni da Musulman. In ba haka ba, da nake gabatar da shirin Masu Hikima Sun Ce da Rayuwar Musulmi, ban samu matsala ba. Amma tun da na gabatar da wannan takarda a kan Maulidi sai aka ga kamar na karkata wajen sukar Maulidin. Alhali kuma ni biyayya na so in yi, wanda hakan ya so ya janyo matsala a makarantata, har Sarkin Tudun Wada ya ce duk fadin Jihar Kaduna lokacin ma tana hade da Katsina; babu wata makaranta mai yawan dalibai kamar tawa.

Domin ko Malam Rakana a lokacin sai a ce dalibansa sun yi dubu, ni kuwa sai a ce ba a san yawansu ba. Amma ni da Allah Ya taimake ni, dalibaina ba su bara; bambancinsu da sauran dalibai ke nan. Duk daliban da aka kawo gidana ba su bara kuma duk wanda aka kawo nan shi zai dauki nauyin abincinsa. Haka muka yi ta tafiya.

Me ya janyo ra’ayinka har ka fara wallafa wakoki da rubutun Hausa?

Babban dalilina na kwadayin rubutun Hausa shi ne saboda in samu isar da sakona ga al’umma, wadanda suke jin harshen Hausa. Saboda ganin yadda na yi rubuce-rubucen Hausa a waccen lokaci. Dubi mawaka wadanda suka yi zamani a lokacin siyasar su Aminu Kano da su Sardauna, wakensu ya game Arewa kaf, lokacin muna yara, muna ta kwaikwayo. Ga su marigayi Alhaji Namange Zariya, su Aliyu Akilu da sauransu. To, irin wadannan rubuce-rubuce da suke yi sun taimaka mana. Allah Ya jikan Abubakar Ladan Zariya, har ni ma na yi masa wake bayan rasuwarsa saboda irin gudunmuwar da ya bai wa Najeriya a kan rubutun Hausa.

Ka ga harshen Hausa ya ba da gudunmuwa wurin addini, ya ba da gudunmuwa wurin ilimin boko, ya kuma ba da gudunmuwa kwarai wajen sana’o’i da al’adu. Sai dai mayar da shi baya ya sa ya zama nakasa da tawaya kwarai, domin duk wani sake-sake da gine-gine da ake yi a da mun san sune a cikin harshen Hausa. Ko a shari’ance babu harshen da aka nuna ka yi kishinsa kamar harshen Alkurani saboda shi ne harshen addini. Daga shi fa sai harshen kasarku, wanda kasarku ta daukaka. Sannan harshen gidanku, wanda shi ne harshen iyayenku. To, kishinsu ya sa na yi rubutun Hausa da kuma domin daukaka harshen da kuma mahimmancinsa gare ni.

Littafai da wakoki nawa ka rubuta zuwa yanzu?

Yanzu a littafin masu Hikima Sun Ce ina da littafi kusan 53, ina cikin na 54 a yanzu. Wakoki kuma daban-daban masu baitoci sama da dari zuwa dari biyu akwai ma mai baitoci dubu cikinta. Saboda haka ba na rasa littattafan wakoki talatin da wani abu. Na kuma soma rubuta wakar Hausa ne tun da na kammala firamare a 1960, domin ina kyautata zaton an haife ni a 1948 ne a Wushishi. Allah cikin ikonSa ne ya sa na samu ilimin wannan waka ta hanyar boko tare da Arabiyya. Haka kuma na rika tafiya da su biyu. Na yi wakoki a kan hadin kan kasa, na yi wa Gidan Rediyon Tarayya kuma sukan sa idan an zo taron bikin cikarta shekara.

A wasu daga cikin wakokinka ka yi magana ne aka hadin kan kasa, ko za ka yi mana karin bayani?

Lokacin da muke yara ba mu san wani bambanci ba a tsakanin Musulmi da Kirista da masu sauran addinai ba. Ba mu san wata maganar darika ko Izala ba, abin da kawai muka sani shi ne Musulmi. Kuma duk inda ka je a Arewacin kasar nan za ka ga idan lokacin Sallah ya yi, Musulmi za su hadu su yi Sallah. Kuma idan watan Azumi ya zo, za a hadu a yi tare. Duk wani soke-soke tsakanin Kirista da Musulmi babu shi, domin ba a ga kafar haka ba. Abin da kawai ake nuna mana shi ne, idan mun je taronsu suka ba mu takarda akan amshe saboda shi yaro ba a raba shi da shige-shige. Kuma a wannan lokaci ana ganin darajar juna, babu wanda yake wulakanta wani. Na yi imani a lokacin za ka ga mutum Musulmi ne yana abota da Kirista. Tun a lokacin za a rika aike a tsakanin juna, wanan ya je gidan wancen wannan ya je gidan wannan. 

Najeriya kasa ce kamar yadda ka ga wake-waken kaza. Bakin ba zai ciru ba, farin ba zai ciru ba. Haka take tare, ko a so, ko kar a so. A rayuwar Najeriya, lokacin da aka mika mulki komai na tafiya daidai, domin ko a cikin shirina na masu Hikima Sun Ce, samun goyon bayan da muka yi daga masu addinai daban-daban shi ya kara masa farin jini. Amma daga bisani ’yan uwanmu ne ma masu addinin saboda akida suke zuwa su bata abin, ba wai wadanda ba addini daya kuke da su ba. Wannan ita ce matsalar da ke damunmu.

Wani kalubale kuke fuskanta, musamman ku mawallafa wakokin Hausa da rubutu a yanzu?

Rashin bai wa harshen Hausa mahimmanci da bai wa shi marubucin gudunmuwa. Allah jikan Alhaji Abubakar Ladan. A lokacin da na samu labarinsa ina gida can Wushishi a Neja na ziyarce shi a gida domin ganin halin da yake ciki. Har ta kai na zo gidan Rediyo, a ce irin gudunmuwar da Abubakar Ladan ya bayar a ce an same shi a irin wannan hali har ta kai kamar ma ba a san da shi ba. Wannan ita ce babbar matsalar da ke damun marubuta yanzu. 

Ka ga su manyan malamai suna da manyan almajirai masu kudi suna biyan kudi ana saka shirye-shiryensu. Amma mu ga rubuce-rubucen nan zube mun yi, ba wanda zai zo ya ce kawo a buga. Ko an amsa idan wasu sun zo daga jami’a sai dai su tsinci abin da suke so a ciki kawai su ajiye, a maimakon su buga a watsa su a makarantun firamare da sakandare domin bunkasa harshen Hausa; sannan kuma kai da ke yi ka samu sauki, a’a.

Kai dai iyakarka ka rubuta ka ajiye, idan ba ka yi sa’a ba in ka mutu a kone. Wani lokaci a jaridu ne muke sa’a su buga mana. Har shafi ake ba ni a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, wani lokaci har ihsani ake mani. Yanzu ba a ma karba sai dai kawai ka yi ta rubutawa kana ajiyewa. To, da rubutawar da ba da damar ka karanta, duk irin wannan suna bunkasa harshen Hausa. Harshen Hausa kuma harshe ne mai sauki a Najeriya. Babu harshen da ya fi shi sauki a harsunan Najeriya, shi ya sa ake yinsa a ko’ina.

Wace hanya kake ganin za a magance matsalolin da kuke fuskanta?

Shi ne gwamnati ta shigo ta nemi duk inda wadanda ke kokarin bunkasa wannan harshe na Hausa tun daga kananan hukumomi. Su a kananan hukumomi sun san wadanda suke da su, sai a ba shi mahimmanci ta yadda zai zo a hadu a jiha, ta yadda za a taimaka masu su bunkasa harshen a kasa baki daya. Sannan duk wanda zai yi wallafa sai gwamnati ta duba ta ga idan ya dace a wallafa wannan littafi sai a taimaka masa. Yanzu duk wanda ya yi karatu shekaru hamsin da suka wuce, idan ka tambaye shi wane littafi ya karanta, babu, domin sun bace. Littatafan da ake amfani da su a yanzu ba namu ba ne ko kuma ba tarbiyyarmu ba ce suke koyarwa. Karance-karancen duk ya gurbata tarbiyya. Yanzu sai ka ji yaro na cewa baba ya zo a zauna a tattauna, wanda wannan bai dace ba a al’adance amma sai ga shi kana cewa ya zo ku tattauna matsalar gida da shi. Ko kuwa malami da ke duba nafsin Alkur’ani ka ce wai y azo ku zauna ku nemi mafita kai da shi. Wacce mafita tun da mu rayuwarmu ba a irin ta wadancen ba ce? Mu rayuwarmu akwai tsari irin yadda shari’a ta shimfida, wanda shi aka ce mu bi. Allah kuwa Ya raba dama da hagu ko a jikanka, Ya kuma yi mahada. Yanzu misali, idan ana cikin masallaci ana Sallah ka ga ai dama kurum za ka bi. Su kuma wadanda suke da harka irin ta yi wa Allah tarayya da tsafi, sai su je su yi nasu, babu ruwanka. 

Inda kuma aka ce mu hadu, kamar titi, ofis, kasuwa sai ka zo da naka addinin, shi ma ya zo da nasa na gargajiya, mu ilimantar da juna; domin haka Allah Ya yi tsarin, tun da shi bai da bukatar dama ko hagu. Bai da bukata daga Musulmin bai kuma da bukata daga Kiristan. Kai ke da bukata, idan kana so. Saboda haka rashin gane wadannan al’amura shi ke wahalar da mu. Shi ya sa babban abin da ake so shi ne, idan kana son duniya bai wuce ka yi biyayya da hakuri ba. In kuma kana son lahira sai ka rike gaskiya da amana da hakuri. In kuma akwai kari, bai wuce ka yi addu’a ba.

 

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta