Rashin nasara a wasa bakon abu ne a wurina – Mourinho

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke kasar Ingila, Jose Mourinho ya ce rashin nasara a wasan kwallon kafa wani bakon abu ne a wurinsa.Jose Mourinho wanda a bara kungiyarsa ta lashe gasar cin kofin Premier ya bayyana haka ne bayan rashin nasarar da kungiyar Chelsea ke yi a wasannin bana, wanda rabon da […]

Rashin nasara a wasa bakon abu ne a wurina – Mourinho
Rashin nasara a wasa bakon abu ne a wurina – Mourinho

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke kasar Ingila, Jose Mourinho ya ce rashin nasara a wasan kwallon kafa wani bakon abu ne a wurinsa.
Jose Mourinho wanda a bara kungiyarsa ta lashe gasar cin kofin Premier ya bayyana haka ne bayan rashin nasarar da kungiyar Chelsea ke yi a wasannin bana, wanda rabon da ta yi hakan tun shekara 29 da suka wuce.
kungiyar Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Eberton a gasar Premier a ranar Asabar, kuma shi ne karo na uku da aka doke ta a wasanni biyar da ta buga.
Wannan sakamakon ya sa Chelsea wacce ta lashe Kofin Premier na bara ta koma mataki na 17 a kan teburin Premier da maki hudu kacal.
Jose Mourinho ya ce “Ba na cikin farin ciki da halin da kungiyar Chelsea ta tsinci kanta a ciki, kuma ban saba da rashin nasara a wasannina ba, amma zan karbi kaddara.”
Chelsea ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Maccabi Tel Abib a ranar Larabar da ta gabata a fafatawar neman zuwa gasar cin Kofin Zakarun Turai, inda ta lallasa ta da ci 4-0. Wannan nasara ta dan kwantar da kurar da ake ganin tana neman yi waje da Mourinho daga horar da kungiyar ta Chelsea.