Rashin ruwan sama ya hana manoma bacci a Taraba
An shafe kimanin mako uku ba tare da an samu saukar ruwan saman ba.
Manoma a Taraba sun shiga zullumi game da daukewar da ruwan sama ya yi a Jihar.
A yankin Arewaci da kuma Tsakiyar Jihar an shafe kimanin mako uku ba tare da an samu saukar ruwan saman ba, lamarin da ya sanya ala tilas aka dakatar da ayyukan noma tare da yi wa taraktoci da dama da ke aiki a gonaki kiranye – suka baro daji zuwa cikin gari.
- An sauya shugaban tsaron Masallacin Harami bayan yunkurin kashe limami
- ’Yan bindiga sun kashe basarake a Sakkwato
- An yanke wa dattijo lafiyayyar kafa aka bar mai ciwon
Wani manomi ya ce, “Kasar ta bushe ba za mu iya yin shuka ko gudanar da wani aikin noma ba a yanzu.”
Malam Jalo Garba, ya shaida wa Aminiya cewa rashin ruwan saman a wannan lokacin yana alamta mummunan abu da ke bukatar a dage da yin addu’a.
Ya ce a bara warhaka amfanin gona har sun fara girma, amma a bana ayyukan noma sun tsaya saboda rashin saukar damina.
Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa baya ga haka, daruruwan manoma da leburori sun rasa na yi a halin da ake ciki.
Mallam Jalo, ya ce abin damuwa ne cewa har zuwa yanzu manoma da dama ba su kai ga shuka amfanin gonarsu ba, wanda hakan hadari ne sosai ga wadatar da abinci.
“Kashi 90 cikin 100 na jama’armu manoma ne kuma rashin ruwan sama ya sa sun koma zaman kashe wando,” inji shi.
Manoma da dama da Aminiya ta zanta da su na da ra’ayin cewa ya kamata a yi addu’ar rokon ruwan saman domin samun taimakon Allah.