Rashin sakar wa masu horar da ’yan wasa mara shi ne matsala –Sabo Jet

Tsohon mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Eleben Star da ke garin Jos, Sabo Abdulmumini Idris, ya ce rashin barin masu horar da ’yan wasa na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles su gudanar da aikinsu kamar yadda ya kamata shi yake kawo cikas wajen ci gaban kulob din.Malam Sabo wanda ake […]

Rashin sakar wa masu horar da ’yan wasa mara shi ne matsala –Sabo Jet
Rashin sakar wa masu horar da ’yan wasa mara shi ne matsala –Sabo Jet

Tsohon mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Eleben Star da ke garin Jos, Sabo Abdulmumini Idris, ya ce rashin barin masu horar da ’yan wasa na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles su gudanar da aikinsu kamar yadda ya kamata shi yake kawo cikas wajen ci gaban kulob din.
Malam Sabo wanda ake kira Sabo Jet ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja a makon da muke ciki.
Ya ce, ‘Abin da yake faruwa shi ne idan aka kawo sabon mai horar da ’yan wasa na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya sai ka ga manajoji suna yi masa katsa-landan. Suna kawo masa ’yan wasa daga wurare daban-daban, sai ka ga ya zama tamkar hoto a wurin ba ya yin abin da ya kamata. Saboda haka dole ne a rika sakar wa masu horar da ’yan wasa mara don su gudanar da aikinsu kamar yadda ya kamata. Hakan shi zai sa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles bangaren maza da bangaren mata da sauran takwarorinsu su cimma nasara’.
Ya ci gaba da cewa, ‘Matsala ta biyu ita ce su kansu masu horar da ’yan wasan ba sa daukar ’yan wasan da suka kamata. Saboda da haka sai ka ga kulob din bai tsinana komai ba.  Yakamata  sabon mai horar da ’yan wasan Super Eagles, Sunday Olise ya rika bibiyar wasanni kungiyoyin kwallon kafa da ke sassa da dama na gida kamar su Kano Pillars da Sunshine da Eyimba da sauransu ta haka ne zai rika samun ’yan wasa masu kwazo.’

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja