Rashin samun tallafi ne matsalata – Mawaki B-Meri
Fitaccen mawakin zamani na Hausa Hip-Hop da ke Jihar Legas mai suna Abdullahi Isma’il, ya ce rashin samun tallafi shi ne babban kalubalen da yake fuskanta a harkokinsa na wakoki. Mawakin, wanda ake yi wa lakabi ba B-Meri ya yi furucin ne yayin da ya kawo ziyara ofishin Aminiya da ke Jihar Legas a kwanakin […]
Fitaccen mawakin zamani na Hausa Hip-Hop da ke Jihar Legas mai suna Abdullahi Isma’il, ya ce rashin samun tallafi shi ne babban kalubalen da yake fuskanta a harkokinsa na wakoki.
Mawakin, wanda ake yi wa lakabi ba B-Meri ya yi furucin ne yayin da ya kawo ziyara ofishin Aminiya da ke Jihar Legas a kwanakin baya.
Ya ce: “Babu shakka ina fuskantar kalubale da yawa. Don a gaskiya rashin samun mutanenmu da za su tallafa mani su zuba kudinsu cikin harkar shi yake ci mani tuwo a kwarya. Mutanenmu har yanzu ba su fahimci muhimmancin waka ba. Su kansu masu sayar da wakokin za ka ga ba sa son karbar namu wakokin, idan ka yi alban ka kai musu sai su rika yi maka hanya-hanya.”
Ya ci gaba da cewa: “Wani kalubalen da nake fuskanta shi ne mutanenmu da yawa ba su dauki waka sana’a ba saboda haka duk abin da muke yi gani suke yi muna bata lokacinmu a banza, mu kuma mun san cewa sana’a muke yi da ake samun arziki.”
Ya bayyana cewa ya yi wakoki da yawa da suka hada da waka mai suna Alhamdu lillahi da Ango da Amarya da Matata da So Mai Sonka da Mu Ji Dadi da Zaman Lafiya da sauran wakoki da yawa.
B-Mari ya kara da cewa ya fara sha’awar waka tun yana yaro karami tun yana kwaikwayon wasu har ta kai yana yin wakokin kansa.
Ya ce ya fara da wakokin Turanci amma daga bisani saboda kishin yaren Hausa ya koma yin wakokin da Hausa.
“Kishi ne ya sa na koma yin waka da Hausa amma a da sai dai na yi da Turanci ko da Yarabanci. Daga bisani sai na lura sauran mawaka suna kishin yarensu sai ni na koma yi da Hausa amma nakan shigar da Yarabanci da Turanci a cikin wakokin. Na yi wakoki da Yarabanci.” Inji shi.
Sai dai B-Mary ya bayyana cewa ya fi son wakarsa mai lakanin Matata saboda abubuwan da ya kunsa na fasaha. To, amma ya bayyana cewa girman kai da kyashi su ne suke hana Hausawa mawaka ci gaba a ji har Legas.
Daga nan sai ya yi kira ga ’yan uwansa mawakan Hausa a jihar su farka daga barcin da suke yi su taho a hada kai don a cin ma burin da aka sa a gaba.
“Babu yadda za mu ci gaba sai mun kawar da girman kai da kyashi da bakin ciki mun so juna mun hada kai don mu cin ma burin da muka sanya a gaba. Ta haka za mu kasance tsintsiya madaurinki daya. Kuma idan muka zama daya babu wanda zai iya karya mu.” Inji shi.