‘Rashin sauraron ra’ayin jama’a ke hana ayyuka yiwuwa a kasa’
Daraktan Yada Ra’ayoyin Jama’a na Cibiyar Shehu Musa Yar’adua, Amara Nwankpa, ya ce rashin sauraron ra’ayoyin jama’a yayin tsara jadawalin ayyukan da za a yi a Najeriya ne ke hana ayyuka da dama yiwuwa. Amara ya bayyana hakan ne, dangane da batun ko Gwamnatin Najeriya na iya cika alkawarin da ta dauka na yakar sauyin […]
Daraktan Yada Ra’ayoyin Jama’a na Cibiyar Shehu Musa Yar’adua, Amara Nwankpa, ya ce rashin sauraron ra’ayoyin jama’a yayin tsara jadawalin ayyukan da za a yi a Najeriya ne ke hana ayyuka da dama yiwuwa.
Amara ya bayyana hakan ne, dangane da batun ko Gwamnatin Najeriya na iya cika alkawarin da ta dauka na yakar sauyin yanayi, a wata tattaunawa ta yini guda da Cibiyar Inganta Aikin Jarida da Kawo Ci gaba Mai Dorewa ta shirya a Abuja.
- A farkon 2023 za mu fara tunkudo iskar Gas zuwa Kaduna da Kano – NNPC
- NAJERIYA A YAU: Shin Da Gaske Peter Obi Ya Jingine Yakin Neman Zabensa?
Ya ce, kowa ya san yadda Gwamnatin Najeriya ke kokarin cusa wa ’yan kasar amfani da iskar gas wurin yin girki, amma gwamnatin ta gaza samar da ita a farashi mai rahusa.
Da yake ba da misalin yadda rashin bayyana wa ’yan Najeriya makasudin tsare-tsarenta, Amara ya ba da misalin irin adadin bishiyoyin da masu gidajen burodi ke konawa a kullum, wanda ke kara dumama yanayin da ke janyo iftila’in iska mai karfi da kuma ambliyar ruwa.
Ya ce, da gwamnati ta tuntubi masu gidajen burodi domin jin yadda za a yi amfani da iskar gas wurin gudanar da sana’arsu, da za su iya ba ta shawarwari da za su yi matukar amfani wurin saukaka kawo tsarin.
Masu hikima na cewa, ‘Da dan gari akan ci gari,’ Gwamnatocin duniya na ci gaba da neman mafita kan sauyin yanayi da ke haddasa asarar da dukiya masu tarin yawa, ciki har da Gwamnatin Najeriya.
Sai dai wannan yunkuri kusan ba a ganin amfaninsa a kasar, lura da cewa ko a daminar bana an samu asarar rayuka da dukiya.