Rashin tabbas kan aikin haƙar fetur na damun mutanen Bauchi da Gombe

NNPC ya ce, ya gano danyen man a rijiyar Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

Rashin tabbas kan aikin haƙar fetur na damun mutanen Bauchi da Gombe

Rijiyar mai ta Kolmani ce ta farko da samu danyen mai da ya kai na kasuwanci a Arewa maso Gabashin Najeriya. (Hoto: Aminiya/Simon Sunday).

Al’ummomin jihohi Bauchi da Gombe da kuma na Arewa sun fara nuna damuwa kan rashin tabbas game da aikin hako man fetur da aka kaddamar a jihohin biyu lokacin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

An faro wannan aiki ne tun a shekarun 1990 lokacin da aka fara ba da lasisin nemo man a rijiyoyi masu lamba (OPLs) 809 da 810 ga kamfanonin Shell da Chevron.

A lokacin an bukaci kamfanonin sun binciko man da ake hasashen samu, tare da hako rijiyoyin.

Kamfanin Shell ya hako rijiyar Kolmani-1 a kan OPL 809 sai Chevron ya hako Nasara-1 a kan OPL 810.

Kamfanonin biyu sun ba da rahoton gano iskar gas da za ta isa a yi kasuwanci kuma suka ce ba su samu man fetur mai yawa ba.

Daga nan sai Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), ya ci gaba da aikin a shekarar 2019 ya ba da sanarwar gano danyen mai da iskar gas mai yawa.

Wannan albishir da kamfanin ya yi ya sa farin ciki ga ’yan Nijeriya, musamman mutanen Arewa.

Kamfanin NNPC ya ce, ya gano danyen man a rijiyar Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe, inda ya ce a rijiyar Kolmani akwai danyen man fetur fiye da ganga biliyan daya da gas da ya kai ganga biliyan 500.

Ya ce, a karon farko na aikin za a samar da matatar mai da sashin sarrafa iskar gas, kuma za a kafa tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 300 da kamfanin yin taki mai samar da tan 2,500 a rana.

Kamfanin NNPC ya ce, zai yi hadin gwiwa ne da Kamfanin Sterling Global Oil da Kamfanin Bunkasa Zuba Jari na Jihohi Arewa wato New Nigeria Development Company (NNDC).

Tsohon Shugaban Kasa Buhari ne ya kaddamar da hako mai na farko a Arewa bayan gano shi a rijjiyar Kolmani a watan Nuwamban, 2022.

Shugaban ya ce, Kamfanin NNPC ya samu jihohi 19 sun zuba jari, kuma an samu masu zuba jari har Dalar Amurka biliyan uku a gida da waje.

Sai dai a bayan nan wakilanmu sun gano aikin hakar man ya ragu matuka bayan kaddamar da aikin, lamarin da ya jefa damuwa da takaici ga jama’a, idan aka yi la’akari da halin da ake ciki a kasuwannin mai da iskar gas.

Aminiya ta gano cewa, kwanaki kadan bayan Buhari da Shugaban Kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu sun jagoranci kaddamar da aikin hako man, sai kamfanonin da suka fara aikin suka tattara kayan aikinsu ba tare da bayyana dalili ba.

Mutane da dama da aka zanta da su sun ce, rashin samun rahoton ci gaba da aikin na haifar da damuwa da yanke kauna ga cin gajiya da fa’idar da ake tsammani daga aikin.

Mazauna kauyen Futuk da ke Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi, Dahiru Muhammad Jamda da Wakili Mbut Mohammed Idris sun bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki da wasa da ci gaban tattalin arzikin da zai kawar da al’ummar jihohin Arewa daga kangin talauci da rashin aikin yi.

Shi ma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed a wani lokaci ya ce, lamarin na jawo matukar damuwa.

Ya ce, ta yaya Shugaban Kasa zai taso daga Abuja ya kaddamar da aikin bayan an zuba jarin sama da Dala biliyan uku, amma a ce aikin ba ya tafiya sun ma mai da wajen fako?

Gwamna Bala ya ce, sun tattauna lamarin a taron Kungiyar Gwamnonin Arewa, “Muna iya kokarinmu tare da Gwamnan Jihar Gombe a kan batun.

“Kuma a taron gwamnonin Arewa da muka yi a Kaduna mun dauki matakai da kudirori da dama don ganin sun dawo ga aikin hakar man, amma ba zan yi riga malam masallaci ba in lokaci ya zo za mu fayyace dukkan bayanan.

“A matsayinmu na shugabanni ba na son mu tayar da hankali, tunda dai ’ya’yanmu ne suke shugabancin wurin,” in ji shi.

A bangaren Gwamnan Jihar Gombe kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce, suna iya bakin kokarinsu tare da Gwamnan Jihar Bauchi kan batun.

Ya ce, su ne suka bukaci tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi duk abin da zai iya ya tabbatar an fara hakar man fetur a Arewa, kuma ya yi kokari an fara.

“Kuma na gana da Shugaba Bola Tinubu na ba shi labarin halin da ake ciki, ya ce in rubuta.

“Na rubuta zan ba shi, kuma na tabbata zai dauki kwakkwaran mataki don ganin an ci gaba da hako mai daga Kolmani,” in ji shi.

Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masana’antu da Ma’adinai da Aikin Gona ta Jihar Bauchi (BACCIMA), Alhaji Aminu Muhammad Danmalikin Bauchi ya ce, akwai shubuha a harkar hakar man.

A cewrsa, sun tuntubi bangarori da dama, amma babu jami’in gwamnati ko na NNPC da ya ce musu uffan kan batun.

Shugaban na BACCIMA ya ce aikin ba irin wanda za a dauka da wasa ba ne domin ana sa ran zai sake fasalin albarkatun da ake da su a Nijeriya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos