Rashin tabbas kan daminar bana ya hana manoman Jihar Yobe runtsawa
Wadansu Manoma a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, sun ce rashin daidaitar saukar ruwan sama, ya sanya fargaba ga manoman jihar cewa ya kamata su karkata ga yi wa amfanin gonar ban-ruwa. Manoman a hirarsu, da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), sun ce yananin daminar ya fara nuna alamun fari, inda suka ce hakan […]
Wadansu Manoma a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, sun ce rashin daidaitar saukar ruwan sama, ya sanya fargaba ga manoman jihar cewa ya kamata su karkata ga yi wa amfanin gonar ban-ruwa.
Manoman a hirarsu, da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), sun ce yananin daminar ya fara nuna alamun fari, inda suka ce hakan bai zo mu su da dadi ba.
Daya daga manoman, Malam Bukar Modu, ya ce da dama daga manoman da suka yi shuka da wuri, bayan samun ruwan farko, yanzu sun rasa na yi, dalilin rashin samun ruwan yadda aka yi tsammani tun farko.
“Wadansu manoma, sai da suka sake shuka, bayan lalacewar shukar da ta fara tsira, sakamakon rashin ruwan sama,” inji Modu.
Wani manomin mai suna, Alhaji Ibrahim Kaku, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya yi ritaya, ya ce ba zai fara shuka ba tukuna, duk kuwa da cewa, ya riga ya gama hudar gonarsa, saboda yadda ruwan saman ya tsagaita na wani lokaci.
“Lamarin ya zama abin fargaba gare mu, saboda rashin tabbas na juriyar amfanin, sakamakon rashin dorewar ruwan sama,” inji shi.
Alhaji Ibrahim Kaku, ya yi kira ga gwamnati ta bullo da shirye-shiryen da za su haifar da noman ban-ruwa ga amfanin gona.
“Lura da yananin ruwan sama, noman ban-ruwa ne kawai mafita wajen tabbatar da inganta samar da amfanin gona da wadatar abinci da habakar tattalin arziki,” inji shi.
Shi ma da yake tsokaci, Haruna Madaki, ya bukaci gwamnati ta yi kokarin samar da kayayyakin noma, musamman taki ga manoman don zuba takin da wuri.