Rashin tallafi ne matsalar sababbin marubuta – Sulaiman B. Sulaiman
Sulaiman Bello Sulaiman dalibi ne a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil-Kano. A matsayinsa na sabon marubuci ya bayyana irin kalubalen da sababbin marubuta ke fuskanta, musamman ta bangaren buga littattafai da sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Mene ne ya ja hankalinka ka fara rubuce-rubuce?Ganin da yadda bangaren ilimi ya shiga wani hali a […]
Sulaiman Bello Sulaiman dalibi ne a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil-Kano. A matsayinsa na sabon marubuci ya bayyana irin kalubalen da sababbin marubuta ke fuskanta, musamman ta bangaren buga littattafai da sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Mene ne ya ja hankalinka ka fara rubuce-rubuce?
Ganin da yadda bangaren ilimi ya shiga wani hali a kasar nan ya sa ni ma na yi tunanin cewa akwai gudunmawar da zan iya bayarwa a wannan bangare, musamman ta hanyar rubuce-rubuce. Abin da ya sa na dauki harshen Hausa na yi rubutu a kai shi ne, ina cikin jami’ar nan sai na fahimci cewa mutane da yawa ba su iya karanta rubutun Hausa ba, a maimakon su karanta shi daidai sai ka ga sun karanta shi a juye kamar ba ’ya’yan Hausawa ba. Wannan ya sa na ga dacewar na taimaka ta wannan bangare.
Zuwa yanzu littatatfai nawa ka rubuta?
Zuwa yanzu na rubuta littatatfai guda biyu duk da cewa matsalar rashin isassun kudi ya hana ni wallafa su amma dai ina da yakinin cewa littattafan za su sawwake wa jama’a hanyoyin koyon karatun Hausa. daya daga ciki shi ne ‘Koyi Zai Amfane Ka.’ Bayan da na kammala sai na dauke shi na kai wa malaman Jami’ar Bayero, inda wata malama ta duba tare da yin gyara a cikinsa.
Wane kokari ka yi wajen ganin ka wallafa littattafan?
A gaskiya da farko na yi kokarin neman mutane daban-daban domin su taimaka wajen buga littafin, musamamn ma ganin cewa littafi ne da za a iya yin amfani da shi a makarantu don samun ilimi amma hakana bai cimma ruwa ba. Baya ga daidaikun mutane da na rika bi, har gwamnati na kai wa kokan barata amma ba a sami biyan bukata ba sai ma yawo da hankali da aka yi ta yi har a karshe na hakura na daina zuwa wurinsu.
Me kake zaton ya bambanta littafinka da makamantansa?
Hanyar da na bi wajen koyar da Hausar mai sauki ce fiye da sauran hanyoyin da wasu marubutan ke bi wajen isar da sakonsu. Da na dudduba wasu littattafa da suke magana a kan koyon karatun Hausa sai na ga yawancinsu hanyoyin da suke bi sun fi karfafawa wajen hadda, don haka ni kuma sai na canza tunanin lamarin gaba daya inda na dauki hanyar koyarwa ta fahimta. Tsarin da nake bi shi ne yadda idan mutum ya ga abin a rubuce a ko’ina ne zai iya fahimtarsa ba wai batun hadda ba.
Wane kira kake da shi ga marubuta ’yan uwanka?
Kirana gare su shi ne, su buda harkar rubutunsu, ba wai kawai su ta’allaka rubutunsu a bangaren soyayya ba. Akwai abubuwan da ya kamata a ce an duba a rayuwa a yi rubutu a kansu don wayar wa jama’a kai. Misali, banagren ilimi da kiwon lafiya da yake-yake da sauransu, amma maimakon haka sai ka ga marubuta sun bar wannan damar sun je suna ta maimaita labari iri daya a litatatfai da dama.
Haka kuma ina kira ga kungiyoyon marubuta da su rika tallafa wa marubuta masu tasowa, ba wai su rika dakile su ba. Idan marubuci ya kawo littafinsa a duba masa tare da ba shi shawarwarin da zai gyara littafin, idan ya kasa buga littafin, a nan ya kamata kungiya ta yi wani abu wajen buga masa littafin idan ya so daga baya sai a warware. Idan sun duba ba lamari ne na gasa ba, a’a abu ne na kokarin ciyar da al’umma gaba. Har ila yau akwai bukatar su sassauta sharuddan shiga kungiyoyin domin sabbin marubuta su sami saukin lamurra.
Zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnati da ta taimaka tare da tallafa wa masu neman taimako irin namu, musamman ma idan an bincika an tabbatar da gaskiyar neman taimakon. Shigowata cikin wannan harka na fahimci cewa matsalar rashin samun tallafi daga jama’a da kuma gwamnati da kungiyoyi shi ne yake dakushe sababbin marubuta har ma takai sun daina sha’awar yin rubutu gaba daya. Idan kika dauke ni a misali, yanzu haka ban da wadannan litattafai da na rubuta guda biyu, ina da wasu a raina da nake so na rubuta, sai dai ganin cewa ban buga wasu ba, shi ya hana ni fara rubuta sababbin.